FIL 12
Horon Ubangiji
1 t Saboda haka, tun da taron shaidu masu ɗumbun yawa suka kewaye mu haka, sai mu ma mu yar da dukkan abin da ya nauyaya mana, da kuma zunubin da ya ɗafe mana, mu kuma yi tseren nan da yake gabanmu tare da jimiri,
2 t muna zuba ido ga Yesu, shi da yake shugaban bangaskiyarmu, da kuma mai kammala ta, wanda domin farin cikin da aka sa a gabansa ya daure wa gicciye, bai mai da shi wani abin kunya ba, a yanzu kuma a zaune yake a dama ga kursiyin Allah.
3 t Ku fa, dubi wannan da ya jure irin gābar nan da masu zunubi suka sha yi da shi, don kada ku gaji, ko kuwa ku karai. 4 t Famarku da zunubi ba ta kai har yadda za a kashe ku ba.
5 Kun kuma mance da gargaɗin nan da Allah ya yi muku a kan ku 'ya'yansa ne, wato
“Ya ɗana, kada ka raina horon Ubangiji,
Kada kuma ka karai, in ya kwaɓe ka.
6 t Domin Ubangiji, wanda yake ƙauna, shi yake horo,
Yakan kuma hori duk ɗan da ya karɓa.”
7 t Shan wuyar da kuke jurewa, ai, duk don horo ne. Allah ya riƙe ku, ku 'ya'yansa ne. To, wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa? 8 t In kuwa ba ku da horo irin horon da ake yi wa kowa, to, ashe, kun zama shegu ke nan, ba 'yan halal ba. 9 t Har wa yau kuma, ai, muna da ubanninmu na jiki da suke hore mu, mun kuwa yi musu ladabi. Ashe, ba za mu fi yi wa Uban ruhohinmu biyayya ƙwarai ba, mu rayu? 10 t Su kam, sun hore mu a ɗan lokaci kaɗan don ganin damarsu, amma shi, don amfanin kanmu ne yake horonmu, domin mu zama abokan tarayya a cikin tsarkinsa.
11 t Ai, kowane irin horo, a lokacin shansa, abu ne mai baƙin ciki, ba na farin ciki ba. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.Faɗakarwa a kan Ƙin Alherin Allah
12 t Domin wannan, ku miƙe hannuwanku da suke reto, da gwiwoyinku marasa ƙarfi. 13 t Ku bi miƙaƙƙun hanyoyi ɗoɗar, don kada mai ɗingishi ya gulle, a maimakon ya warke. 14 t Ku himmantu ga zaman lafiya da kowa, ku kuma zama a tsarkake, in banda shi kuwa, ba wanda zai ga Ubangiji. 15 t Ku kula fa, kada kowa yă kāsa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen ɗacin rai ya tabbata, ya haddasa ɓarna, har ya ɓata mutane masu yawa ta haka, 16 t kada kuma wani yă zama fasiki, ko mai sāɓon Allah, kamar isuwa, wanda ya sayar da hakkinsa na ɗan fari a kan cimaka a ɗaya tak.
17 t Kun dai sani daga baya, da ya so yă gāji albarkar nan, sai aka ƙi shi, domin bai sami hanyar tuba ba, ko da yake ya yi ta nemanta har da hawaye.
18 t Ai, ba ga abin da za a taɓa ne, kuka iso ba, ko wuta mai ruruwa, ko baƙin duhu duhu ƙirin, ko hadiri, 19 t ko ƙarar ƙaho, ko wata murya, wadda har masu jin maganarta suka yi roƙo kada su ƙara ji, 20 t don ba su iya jure umarnin da aka yi musu ba cewa, “Ko da dabba ce ta taɓa dutsen, sai a kashe ta da jifa.” 21 Amma ganin wannan abu da matuƙar bantsoro yake! Har ma Musa ya ce, “Ina rawar jiki don matuƙar tsoro.” 22 t Amma ku kun iso Ɗutsen Sihiyona ne, da birnin Allah Rayayye, Urushalima ta Sama, wurin dubban mala'iku. 23 t Kun iso taron farin ciki na kirayayyun 'ya'yan fari na Allah, waɗanda sunayensu suke a rubuce a Sama. Kun iso wurin Allah, wanda yake shi ne mai yi wa kowa shari'a, da kuma wurin ruhohin mutane masu adalci, waɗanda aka kammala.
24 t Kun iso wurin Yesu, matsakancin sabon alkawari, da kuma wurin jinin nan na tsarkakewa, wanda yake yin mafificiyar magana fiye da na Habila.
25 t Ku kula fa, kada ku ƙi mai maganar nan. Domin in waɗanda suka ƙi jin mai yi musu gargaɗi a duniya ba su tsira ba, to, ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi jin wannan da yake yi mana gargaɗi ma daga Sama? 26 t A lokacin nan muryarsa ta girgiza duniya, amma a yanzu ya yi alkawari cewa, “Har wa yau dai sau ɗaya tak, ba duniya kaɗai zan girgiza ba, amma har sama ma.” 27 t To, wannan cewa, “Har wa yau dai sau ɗaya tak,” ya nuna kawar da abubuwan da aka girgiza, wato abubuwan da aka halitta, don abubuwan da ba sa girgizuwa su wanzu. 28 t Saboda haka, sai mu yi godiya domin mun sami mulkin da ba ya girgizuwa, ta haka kuma mu yi wa Allah sujada abar karɓa, tare da tsoro da tsananin girmamawa, 29 t domin Allahnmu wuta ne mai cinyewa.
Hebrews 12
1 Therefore let us also, seeing we are compassed about with so great a cloud of witnesses, lay aside every weight, and the sin which doth so easily beset us, and let us run with patience the race that is set before us,2 looking unto Jesus the author and perfecter of our faith, who for the joy that was set before him endured the cross, despising shame, and hath sat down at the right hand of the throne of God.3 For consider him that hath endured such gainsaying of sinners against himself, that ye wax not weary, fainting in your souls.4 Ye have not yet resisted unto blood, striving against sin:5 and ye have forgotten the exhortation which reasoneth with you as with sons, My son, regard not lightly the chastening of the Lord, Nor faint when thou art reproved of him;
6 For whom the Lord loveth he chasteneth, And scourgeth every son whom he receiveth.
7 It is for chastening that ye endure; God dealeth with you as with sons; for what son is there whom his father chasteneth not?8 But if ye are without chastening, whereof all have been made partakers, then are ye bastards, and not sons.9 Furthermore, we had the fathers of our flesh to chasten us, and we gave them reverence: shall we not much rather be in subjection unto the Father of spirits, and live?10 For they indeed for a few days chastened us as seemed good to them; but he for our profit, that we may be partakers of his holiness.11 All chastening seemeth for the present to be not joyous but grievous; yet afterward it yieldeth peaceable fruit unto them that have been exercised thereby, even the fruit of righteousness.12 Wherefore lift up the hands that hang down, and the palsied knees;13 and make straight paths for your feet, that that which is lame be not turned out of the way, but rather be healed.14 Follow after peace with all men, and the sanctification without which no man shall see the Lord:15 looking carefully lest there be any man that falleth short of the grace of God; lest any root of bitterness springing up trouble you, and thereby the many be defiled;16 lest there be any fornication, or profane person, as Esau, who for one mess of meat sold his own birthright.17 For ye know that even when he afterward desired to inherit the blessing, he was rejected; for he found no place for a change of mind in his father, though he sought it diligently with tears.18 For ye are not come unto a mount that might be touched, and that burned with fire, and unto blackness, and darkness, and tempest,19 and the sound of a trumpet, and the voice of words; which voice they that heard entreated that no word more should be spoken unto them;20 for they could not endure that which was enjoined, If even a beast touch the mountain, it shall be stoned;21 and so fearful was the appearance, that Moses said, I exceedingly fear and quake:22 but ye are come unto mount Zion, and unto the city of the living God, the heavenly Jerusalem, and to innumerable hosts of angels,23 to the general assembly and church of the firstborn who are enrolled in heaven, and to God the Judge of all, and to the spirits of just men made perfect,24 and to Jesus the mediator of a new covenant, and to the blood of sprinkling that speaketh better than that of Abel.25 See that ye refuse not him that speaketh. For if they escaped not when they refused him that warned them on earth, much more shall not we escape who turn away from him that warneth from heaven:26 whose voice then shook the earth: but now he hath promised, saying, Yet once more will I make to tremble not the earth only, but also the heaven.27 And this word, Yet once more, signifieth the removing of those things that are shaken, as of things that have been made, that those things which are not shaken may remain.28 Wherefore, receiving a kingdom that cannot be shaken, let us have grace, whereby we may offer service well-pleasing to God with reverence and awe:29 for our God is a consuming fire.