FIL 13
Gudunmawar da yake Faranta wa Allah Rai
1 t Sai ku nace da ƙaunar 'yan'uwa. 2 t Kada ku daina yi wa baƙi alheri, gama ta haka ne waɗansu suka sauki mala'iku ba da sani ba. 3 t Ku riƙa tunawa da waɗanda suke kurkuku, kamar tare kuke a ɗaure, da kuma waɗanda ake gwada wa wuya, kamar ku ake yi wa. 4 t Kowa yă girmama aure, Gădon aure kuwa yă zauna marar dauɗa, don fasikai da mazinata Allah zai hukunta su, 5 t Kada halinku ya zama na son kuɗi. Ku dangana da abin da kuke da shi, gama Allah kansa ya ce, “Har abada ba zan bar ka ba. Har abada kuma ba zan yashe ka ba.”
6 Saboda haka, ma iya fitowa gabagaɗi, mu ce,
“Ubangiji shi ne mataimakina,
Ba zan ji tsoro ba.
Me mutum zai iya yi mini?”
7 t Ku tuna da shugabanninku na dā, waɗanda suka faɗa muku Maganar Allah. Ku dubi ƙarshensu, ku kuma yi koyi da bangaskiyarsu. 8 t Yesu Almasihu ba ya sākewa, shi ne a jiya, da yau, hakika har abada ma. 9 t Kada baƙuwar koyarwa iri iri ta bauɗar da ku, ai, abu ne mai kyau alherin Allah ya zamana shi yake ƙarfafa zuciya, ba abinci iri iri ba, waɗanda ba su amfani ga masu dogara da su. 10 t Muna da bagadin hadaya, wanda masu ibada a alfarwar nan ba su da izini su ci abincin wurin, 11 t domin naman dabbobin da babban firist yake ɗiban jininsu yă kai Wuri Mafi Tsarki domin kawar da zunubai, akan ƙone shi ne a bayan zango. 12 t Haka ma, Yesu ya sha wuya a waje bayan birni, domin yă tsarkake jama'a da nasa jini. 13 t Saboda haka, sai mu fita mu je a gare shi a bayan zango, muna shan irin wulakancin da aka yi masa. 14 t Domin ba mu da wani dawwamammen birni a nan, birnin nan mai zuwa muke nema. 15 t To, a koyaushe, sai mu yi ta yabon Allah ta wurinsa, sadakar da muke miƙawa ke nan, wato mu yabe shi, muna ta ɗaukaka sunansa.
16 t Kada kuwa ku daina yin alheri da gudunmawa, domin irin waɗannan su ne suke faranta wa Allah rai.
17 t Ku yi wa shugabanninku biyayya, ku bi umarnansu, don su ne masu kula da rayukanku, su ne kuma za su yi lissafin aikinsu, don su yi haka da farin ciki, ba da baƙin ciki ba, don in sun yi da baƙin ciki ba zai amfane ku ba.
18 t Ku yi mana addu'a, gama mun tabbata muna da lamiri mai kyau, muna kuwa so mu tafiyar da al'amuranmu da halin kirki ne.
19 t Musamman nake tsananta roƙonku ku yi haka, don a hanzarta a komo da ni a gare ku.Sa Albarka da kuma Gaisuwa
20 t Allah mai zartar da salama, wanda ya ta da Ubangijinmu Yesu, Makiyayin tumaki mai girma, daga matattu, albarkacin jinin nan na tabbatar madawwamin alkawari,
21 t yă kamala ku da kowane irin kyakkyawan abu, domin ku aikata nufinsa, yă kuma aikata a cikinmu abin da yake faranta masa rai ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka tā tabbata a gare shi har abada abadin. Amin, Amin.
22 t To, ina roƙonku, 'yan'uwa, ku yi haƙuri da gargaɗina, don taƙaice na rubuto muku. 23 t Ku sani, an sāki ɗanuwanmu Timoti, da shi ma za mu gan ku, in ya zo da wuri. 24 t Ku gai da dukan shugabanninku, da kuma dukan tsarkaka. Waɗanda suke daga ƙasar Italiya suna gaishe ku. 25 t Alharin Ubangiji yă tabbata a gare ku, ku duka. Amin.
Hebrews 13
1 Let love of the brethren continue.2 Forget not to show love unto strangers: for thereby some have entertained angels unawares.3 Remember them that are in bonds, as bound with them; them that are illtreated, as being yourselves also in the body.4 Let marriage be had in honor among all, and let the bed be undefiled: for fornicators and adulterers God will judge.5 Be ye free from the love of money; content with such things as ye have: for himself hath said, I will in no wise fail thee, neither will I in any wise forsake thee.6 So that with good courage we say, The Lord is my helper; I will not fear: What shall man do unto me?
7 Remember them that had the rule over you, men that spake unto you the word of God; and considering the issue of their life, imitate their faith.8 Jesus Christ is the same yesterday and to-day, yea and for ever.9 Be not carried away by divers and strange teachings: for it is good that the heart be established by grace; not by meats, wherein they that occupied themselves were not profited.10 We have an altar, whereof they have no right to eat that serve the tabernacle.11 For the bodies of those beasts whose blood is brought into the holy place by the high priest as an offering for sin, are burned without the camp.12 Wherefore Jesus also, that he might sanctify the people through his own blood, suffered without the gate.13 Let us therefore go forth unto him without the camp, bearing his reproach.14 For we have not here an abiding city, but we seek after the city which is to come.15 Through him then let us offer up a sacrifice of praise to God continually, that is, the fruit of lips which make confession to his name.16 But to do good and to communicate forget not: for with such sacrifices God is well pleased.17 Obey them that have the rule over you, and submit to them: for they watch in behalf of your souls, as they that shall give account; that they may do this with joy, and not with grief: for this were unprofitable for you.18 Pray for us: for we are persuaded that we have a good conscience, desiring to live honorably in all things.19 And I exhort you the more exceedingly to do this, that I may be restored to you the sooner.20 Now the God of peace, who brought again from the dead the great shepherd of the sheep with the blood of an eternal covenant, even our Lord Jesus,21 make you perfect in every good thing to do his will, working in us that which is well-pleasing in his sight, through Jesus Christ; to whom be the glory for ever and ever. Amen.22 But I exhort you, brethren, bear with the word of exhortation, for I have written unto you in few words.23 Know ye that our brother Timothy hath been set at liberty; with whom, if he come shortly, I will see you.24 Salute all them that have the rule over you, and all the saints. They of Italy salute you.25 Grace be with you all. Amen.