previous next

FIL 5

1  t Kowane babban firist, da yake an zaɓe shi ne daga cikin mutane, akan sa shi yă wakilci mutane ga al'amarin Allah, don yă miƙa sadakoki da kuma hadayu domin kawar da zunubai. 2 t Yă kuma zamana wanda zai iya tafiyar da jahilai da sangartattu a cikin salihanci, tun da yake rarrauna ne shi ta ko'ina. 3 t Saboda haka, wajibi ne yă miƙa hadayu, ba saboda kawar da zunuban jama'a kaɗai ba, har ma don nasa.

4 t Ba wanda zai kai kansa wannan matsayi mai girma, sai dai Allah ya yi kiransa ga haka, kamar yadda aka kirayi Haruna.

5  t Haka kuma, Almasihu, ba shi ya ɗaukaka kansa ya zama Babban Firist ba, sai dai wannan ne ya sa shi, wanda ya ce da shi,
“Kai Ɗana ne,
Ni Ubanka ne yau.”

6  t Kamar dai yadda a wani wuri kuma ya ce,
“Kai firist ne na har abada,
Kwatancin ɗabi'ar Malkisadik.”
7  t Almasihu, a lokacin zamansa a duniya, ya yi addu'o'i da roƙe-roƙe, tare da kuka mai tsanani, har da hawaye, ga wannan da yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa saurare shi saboda tsananin miƙa kansa. 8 t Ko da yake shi Ɗa ne, ya koyi biyayya ta wurin wuyar da ya sha, 9 t da ya kai ga kammala, sai ya zama tushen madawwamin ceto ga dukkan waɗanda suke masa biyayya,

10 t gama Allah yana kiransa Babban Firist, kwatancin ɗabi'ar Malkisadik.

Faɗakarwa a kan Wata Koyarwa Dabam


11 Muna da abu da yawa da za mu faɗa a game da shi kuwa, amma zai yi wuyar bayani, da yake basirarku ta dushe. 12 t Ko da yake kamar a yanzu kam, ai, ya kamata ku zama masu koyarwa, duk da haka, ashe, ba ku wuce wani ya sāke koya muku jigajigan farko na Maganar Allah ba, har ya zamana sai an ba ku nono, ba abinci mai tauri ba. 13 t Ai, duk wanda yake nono ne abincinsa, bai ƙware da maganar adalci ba, kamar jariri yake. 14 t Amma abinci mai tauri, ai, na manya ne, wato waɗanda hankalinsu ya horu yau da kullum, su rarrabe nagarta da mugunta.

Hebrews 5

1 For every high priest, being taken from among men, is appointed for men in things pertaining to God, that he may offer both gifts and sacrifices for sins:2 who can bear gently with the ignorant and erring, for that he himself also is compassed with infirmity;3 and by reason thereof is bound, as for the people, so also for himself, to offer for sins.4 And no man taketh the honor unto himself, but when he is called of God, even as was Aaron.5 So Christ also glorified not himself to be made a high priest, but he that spake unto him, Thou art my Son, This day have I begotten thee:

6 as he saith also in another place, Thou art a priest for ever After the order of Melchizedek.

7 Who in the days of his flesh, having offered up prayers and supplications with strong crying and tears unto him that was able to save him from death, and having been heard for his godly fear,8 though he was a Son, yet learned obedience by the things which he suffered;9 and having been made perfect, he became unto all them that obey him the author of eternal salvation;10 named of God a high priest after the order of Melchizedek.11 Of whom we have many things to say, and hard of interpretation, seeing ye are become dull of hearing.12 For when by reason of the time ye ought to be teachers, ye have need again that some one teach you the rudiments of the first principles of the oracles of God; and are become such as have need of milk, and not of solid food.13 For every one that partaketh of milk is without experience of the word of righteousness; for he is a babe.14 But solid food is for fullgrown men, even those who by reason of use have their senses exercised to discern good and evil.