FIL 6
1 t Saboda haka, sai mu ci gaba a kan ka'idodin farko na al'amarin Almasihu, har ya zuwa kammala, ba wai mu sāke koyar da jigajigan nan na tuba da ibada marar tasiri ba, da na gaskatawa da Allah, 2 t da kuma na koyarwa a kan wanke-wanke, da ɗora hannu, da tashin matattu, da dawwamammen hukunci. 3 t Za mu kuwa ci gaba in Allah ya yarda. 4 t Domin waɗanda aka haskaka zukatansu sarai, har suka ɗanɗana baiwar nan ta Basamaniya, suka kuma sami rabo na ruhu mai tsarki, 5 har suka ɗanɗana daɗin Maganar Allah, da ikon zamani mai zuwa, 6 t sa'an nan kuma suka ridda, ba mai yiwuwa ba ne a sāke jawo su ga tuba, tun da yake sāke gicciye Ɗan Allah suke yi, su da kansu, suka kuma wulakanta shi a sarari. 7 Ƙasa ma da take shanye ruwan da ake yi mata a kai a kai, take kuma fid da tsire-tsire masu amfani ga waɗanda ake noma ta dominsu, Allah yakan sa mata albarka.
8 t Amma tsire-tsirenta ƙaya ne da kashin yawo, ba ta da amfani ke nan, tana kuma gab da la'antarwa, ƙarshenta dai ƙonewa ne.Tabbataccen Bege
9 t Ko da yake mun faɗi haka, a game da ku kam, ya ƙaunatattu, mun tabbata kuna a kan abubuwa mafiya kyau na zancen ceto. 10 t Gama Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi, wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi. 11 t Muna dai bukata ƙwarai kowannenku ya nuna irin wannan himma ga yin cikkaken bege, tabbatacce, har ya zuwa ƙarshe,
12 t don kada ku yi ragwanci, sai dai ku yi koyi da waɗanda suka karɓi cikar alkawaran nan, ta wurin bangaskiyarsu da haƙurinsu.
13 t Sa'ad da Allah ya yi wa Ibrahim alkawari, da yake ba wani wanda ya fi shi girma da zai rantse da shi, sai ya rantse da kansa,
14 t ya ce, “Hakika zan yi maka albarka, in kuma riɓanya zuriyarka.”
15 t Ta haka Ibrahim, bayan da ya jure da haƙuri, ya karɓi cikar alkawarin. 16 t Hakika mutane sukan rantse da abin da ya fi su, rantsuwa kuma ita ce abar da take tabbatarwa a duk lokacin gardama. 17 t Don haka, sa'ad da Allah yake son ƙara tabbatar wa magādan alkawarin nan dahir, cewa nufinsa ba mai sākewa ba ne sam, sai ya haɗa da rantsuwa, 18 t domin albarkacin abubuwa guda biyun nan marasa sākewa, masu nuna, cewa ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya, mu da muka gudu muka sami mafaka, mu ƙarfafa ƙwarai mu riski abin da muka kafa bege a kai. 19 t Begen nan kuwa da muke da shi, kamar anka yake ga rai, kafaffe, tabbatacce, shi ne kuma yake shiga har can ciki bayan labulen, 20 t a inda saboda mu ne Yesu ya riga mu shiga, da yake ya zama Babban Firist na har abada, kwatancin ɗabi'ar Malkisadik.
Hebrews 6
1 Wherefore leaving the doctrine of the first principles of Christ, let us press on unto perfection; not laying again a foundation of repentance from dead works, and of faith toward God,2 of the teaching of baptisms, and of laying on of hands, and of resurrection of the dead, and of eternal judgment.3 And this will we do, if God permit.4 For as touching those who were once enlightened and tasted of the heavenly gift, and were made partakers of the Holy Spirit,5 and tasted the good word of God, and the powers of the age to come,6 and then fell away, it is impossible to renew them again unto repentance; seeing they crucify to themselves the Son of God afresh, and put him to an open shame.7 For the land which hath drunk the rain that cometh oft upon it, and bringeth forth herbs meet for them for whose sake it is also tilled, receiveth blessing from God:8 but if it beareth thorns and thistles, it is rejected and nigh unto a curse; whose end is to be burned.9 But, beloved, we are persuaded better things of you, and things that accompany salvation, though we thus speak:10 for God is not unrighteous to forget your work and the love which ye showed toward his name, in that ye ministered unto the saints, and still do minister.11 And we desire that each one of you may show the same diligence unto the fulness of hope even to the end:12 that ye be not sluggish, but imitators of them who through faith and patience inherit the promises.13 For when God made promise to Abraham, since he could swear by none greater, he sware by himself,14 saying, Surely blessing I will bless thee, and multiplying I will multiply thee.15 And thus, having patiently endured, he obtained the promise.16 For men swear by the greater: and in every dispute of theirs the oath is final for confirmation.17 Wherein God, being minded to show more abundantly unto the heirs of the promise the immutability of his counsel, interposed with an oath;18 that by two immutable things, in which it is impossible for God to lie, we may have a strong encouragement, who have fled for refuge to lay hold of the hope set before us:19 which we have as an anchor of the soul, a hope both sure and stedfast and entering into that which is within the veil;20 whither as a forerunner Jesus entered for us, having become a high priest for ever after the order of Melchizedek.