previous next

YAK 1

Gaisuwa

1  t Daga Yakubu, bawan Allah, da kuma na Ubangiji Yesu Almasihu, zuwa ga kabilan nan goma sha biyu da suke a warwatse a duniya. Gaisuwa mai yawa.

Bangaskiya da Tawali'u


2  t Ya ku 'yan'uwana, duk sa'ad da gwaje-gwaje iri iri suka same ku, ku mai da su abin farin ciki ƙwarai. 3 Domin kun san jarrabawar bangaskiyarku takan haifi jimiri.

4 Sai kuma jimiri ya yi cikakken aikinsa, domin ku zama kamilai cikakku kuma, ba ku gaza da kome ba.
5  t In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuwa a ba shi. 6 t Amma fa sai ya roƙa da bangaskiya, ba tare da shakka ba. Don mai shakka kamar raƙuman ruwan teku yake, waɗanda iska take korawa tana tuttunkuɗawa.

7-8 t Kada irin mutumin nan mai zuciya biyu, wanda bai tsai da zuciyarsa a gu ɗaya a dukan al'amuransa ba, ya sa rai da wani abu a gun Ubangiji.
9 Ƙasƙantaccen ɗan'uwa yă yi taƙama da ɗaukakarsa. 10 t Mai arziki kuma yă yi alfarma da ƙasƙancinsa, gama zai shuɗe kamar hudar ciyawa.

11 t In rana ta tāke da ƙunarta, sai ciyawa ta bushe, hudarta ta kaɗe, kyanta kuma ya gushe. Haka ma mai arziki zai gushe yana a cikin tsakiyar harkarsa.

Gwaji da Jarrabawa


12  t Albarka tā tabbata ga mai jimirin gwaji, domin in ya jure gwajin, sai ya sami kambin rai, wanda Ubangiji ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari. 13 Duk wanda ake jarabta, kada ya ce Allah ne yake jarabtarsa, gama ba shi yiwuwa a jarabci Allah da mugunta, shi kansa kuwa ba ya jarabtar kowa. 14 Amma kowane mutum yakan jarabtu in mugun burinsa ya ruɗe shi, ya kuma yaudare shi.

15 t Mugun buri kuma in ya yi ciki, yakan haifi zunubi. Zunubi kuma in ya balaga, yakan jawo mutuwa.
16  t Kada fa a yaudare ku, ya 'yan'uwana ƙaunatattu. 17 t Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.

18 t Bisa ga nufinsa ya kawo mu ta maganar gaskiya, domin mu zama kamar nunan fari na halittarsa.

Jin Magana da Aikatawa


19  t Ya 'yan'uwana ƙaunatattu, ku san wannan, wato, kowa yă yi hanzarin kasa kunne, da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi, 20 don fushin mutum ba ya aikata adalci.

21 t Saboda haka, sai ku yar da kowane irin aikin ƙazanta da ƙeta iri iri, maganar nan da aka dasa a zuciyarku, ku yi na'am da ita a cikin halin tawali'u, domin ita ce mai ikon ceton rayukanku.
22 Amma ku zama masu aikata maganar, ba masu ji kawai, kuna yaudarar kanku ba. 23 Don duk wanda yake mai jin maganar ne kawai, ba mai aikatawa ba, kamar mutum yake mai duba fuskarsa a madubi, 24 don yakan dubi fuskarsa ne kawai ya tafi, nan da nan kuwa sai ya mance kamanninsa.

25 t Amma duk mai duba cikakkiyar ka'idar nan ta 'yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai ya mance ba, sai dai mai aikatawa ne ya zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake aikatawa.
26  t In wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, sai dai ya yaudari kansa, to, addinin mutumin nan na banza ne. 27 t Addini sahihi kuma marar aibu a gaban Allah Ubanmu, shi ne a kula da gwauraye mata, da marayu a cikin ƙuntatarsu, a kuma a keɓe kai marar aibi daga duniya.

James 1

1 James, a servant of God and of the Lord Jesus Christ, to the twelve tribes which are of the Dispersion, greeting.2 Count it all joy, my brethren, when ye fall into manifold temptations;3 Knowing that the proving of your faith worketh patience.4 And let patience have its perfect work, that ye may be perfect and entire, lacking in nothing.5 But if any of you lacketh wisdom, let him ask of God, who giveth to all liberally and upbraideth not; and it shall be given him.6 But let him ask in faith, nothing doubting: for he that doubteth is like the surge of the sea driven by the wind and tossed.7 For let not that man think that he shall receive anything of the Lord;8 a doubleminded man, unstable in all his ways.9 But let the brother of low degree glory in his high estate:10 and the rich, in that he is made low: because as the flower of the grass he shall pass away.11 For the sun ariseth with the scorching wind, and withereth the grass: and the flower thereof falleth, and the grace of the fashion of it perisheth: so also shall the rich man fade away in his goings.12 Blessed is the man that endureth temptation; for when he hath been approved, he shall receive the crown of life, which the Lord promised to them that love him.13 Let no man say when he is tempted, I am tempted of God; for God cannot be tempted with evil, and he himself tempteth no man:14 but each man is tempted, when he is drawn away by his own lust, and enticed.15 Then the lust, when it hath conceived, beareth sin: and the sin, when it is fullgrown, bringeth forth death.16 Be not deceived, my beloved brethren.17 Every good gift and every perfect gift is from above, coming down from the Father of lights, with whom can be no variation, neither shadow that is cast by turning.18 Of his own will he brought us forth by the word of truth, that we should be a kind of firstfruits of his creatures.19 Ye know this, my beloved brethren. But let every man be swift to hear, slow to speak, slow to wrath:20 for the wrath of man worketh not the righteousness of God.21 Wherefore putting away all filthiness and overflowing of wickedness, receive with meekness the implanted word, which is able to save your souls.22 But be ye doers of the word, and not hearers only, deluding your own selves.23 For if any one is a hearer of the word and not a doer, he is like unto a man beholding his natural face in a mirror:24 for he beholdeth himself, and goeth away, and straightway forgetteth what manner of man he was.25 But he that looketh into the perfect law, the law of liberty, and so continueth, being not a hearer that forgetteth but a doer that worketh, this man shall be blessed in his doing.26 If any man thinketh himself to be religious, while he bridleth not his tongue but deceiveth his heart, this man’s religion is vain.27 Pure religion and undefiled before our God and Father is this, to visit the fatherless and widows in their affliction, and to keep oneself unspotted from the world.