previous next

YAK 2

Faɗaka a kan Tara

1  t Ya ku 'yan'uwana, kada ku nuna bambanci muddin kuna riƙe da bangaskiyarku ga Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangiji Maɗaukaki. 2 Misali, in mutum mai zobban zinariya da tufafi masu ƙawa ya halarci taronku, wani matalauci kuma ya shigo a saye da tsummoki, 3 sa'an nan kuka kula da mai tufafi masu ƙawar nan, har kuka ce masa, “Ga mazauni mai kyau a nan,” matalaucin nan kuwa kuka ce masa, “Tsaya daga can,” ko kuwa, “Zauna a nan ƙasa a gabana,” 4 t ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ba ke nan, kuna zartar da hukunci da mugayen tunani? 5 t Ku saurara, ya 'yan'uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi matalautan duniyar nan su wadata da bangaskiya, har su sami gado a cikin mulkin nan da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba? 6 t Amma, kun wulakanta matalauta! Ashe, ba masu arzikin ne suke matsa muku ba? Ba su ne kuwa suke janku zuwa gaban shari'a ba?

7 Ba kuma su ne kuke saɓon sunan nan mai girma da ake kiranku da shi ba?
8  t Idan lalle kun cika muhimmin umarni yadda Nassi ya ce, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” to, madalla. 9 t Amma in kun nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan, Shari'a kuma ta same ku da laifin keta umarni. 10 t Duk wanda yake kiyaye dukkan Shari'a, amma ya saɓa a kan abu guda, ya saɓi Shari'a gaba ɗaya ke nan. 11 t Domin shi wannan da ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.” To, in ba ka yi zina ba amma ka yi kisankai, ai, ka zama mai keta Shari'a ke nan. 12 t Saboda haka, maganarku da aikinku su kasance irin na mutanen da za a yi wa shari'a bisa ga ka'idar 'yanci.

13 t Gama Shari'a marar jinƙai ce ga wanda ba ya nuna jinƙai. Amma jinƙai yana rinjayar hukunci.

Bangaskiya Ba Tare da Ayyuka Ba Banza Ce


14  t Ya ku 'yan'uwana, ina amfani mutum ya ce yana da bangaskiya, alhali kuwa ba ya aikin da zai nuna ta? Anya, bangaskiyar nan tāsa ta iya cetonsa? 15 t Misali, in wani ɗan'uwa ko 'yar'uwa suna zaman huntanci, kullum kuma abinci bai wadace su ba, 16 t waninku kuma ya ce musu, “To, ku sauka lafiya, Allah ya ba ci, da sha, da tufatarwa” ba tare da kun biya musu bukata ba, ina amfanin haka?

17 Haka ma, bangaskiya ita kaɗai, ba tare da aikin da ya nuna ta ba, banza ce.
18  t To, amma wani zai ce, “Ai, kai kana da bangaskiya, ni kuwa sai aikatawa.” To, nuna mini bangaskiya, taka ba tare da aikatawa ba, ni kuma in nuna maka aikatawata, tabbatar bangaskiyata. 19 t Ka gaskata Allah ɗaya ne? To, madalla. Ai, ko aljannu ma sun gaskata, amma suna rawar jiki don tsoro. 20 t Kai marar azanci! Wato sai an nuna maka, bangaskiya ba tare da aikatawa ba, wofiya ce? 21 t Sa'ad da kakanmu Ibrahim ya miƙa ɗansa Ishaku a bagadin hadaya, ashe, ba ta wurin aikatawa ne ya barata ba? 22 t Ka gani, ashe, bangaskiyarsa da aikatawarsa duka yi aiki tare, har ta wurin aikatawar nan bangaskiyarsa ta kammala. 23 t Aka kuma cika Nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, bangaskiyar nan tasa kuma aka lasafta ta adalci ce a gare shi,” aka kuma kira shi aminin Allah. 24 Kun ga, ashe, Allah yana kuɓutar da mutum saboda aikatawarsa ne, ba saboda bangaskiya ita kaɗai ba. 25 t Ashe, ba haka kuma Rahab karuwar nan ta sami kuɓuta saboda aikatawarta ba? Wato, sa'ad da ta sauki jakadun nan, ta fitar da su ta wata hanya dabam? 26 t To, kamar yadda jiki ba numfashi matacce ne, haka ma bangaskiya ba aikatawa matacciya ce.

James 2

1 My brethren, hold not the faith of our Lord Jesus Christ, the Lord of glory, with respect of persons.2 For if there come into your synagogue a man with a gold ring, in fine clothing, and there come in also a poor man in vile clothing;3 and ye have regard to him that weareth the fine clothing, and say, Sit thou here in a good place; and ye say to the poor man, Stand thou there, or sit under my footstool;4 Do ye not make distinctions among yourselves, and become judges with evil thoughts?5 Hearken, my beloved brethren; did not God choose them that are poor as to the world to be rich in faith, and heirs of the kingdom which he promised to them that love him?6 But ye have dishonored the poor man. Do not the rich oppress you, and themselves drag you before the judgment-seats?7 Do not they blaspheme the honorable name by which ye are called?8 Howbeit if ye fulfil the royal law, according to the scripture, Thou shalt love thy neighbor as thyself, ye do well:9 but if ye have respect of persons, ye commit sin, being convicted by the law as transgressors.10 For whosoever shall keep the whole law, and yet stumble in one point, he is become guilty of all.11 For he that said, Do not commit adultery, said also, Do not kill. Now if thou dost not commit adultery, but killest, thou art become a transgressor of the law.12 So speak ye, and so do, as men that are to be judged by a law of liberty.13 For judgment is without mercy to him that hath showed no mercy: mercy glorieth against judgment.14 What doth it profit, my brethren, if a man say he hath faith, but have not works? can that faith save him?15 If a brother or sister be naked and in lack of daily food,16 and one of you say unto them, Go in peace, be ye warmed and filled; and yet ye give them not the things needful to the body; what doth it profit?17 Even so faith, if it have not works, is dead in itself.18 Yea, a man will say, Thou hast faith, and I have works: show me thy faith apart from thy works, and I by my works will show thee my faith.19 Thou believest that God is one; thou doest well: the demons also believe, and shudder.20 But wilt thou know, O vain man, that faith apart from works is barren?21 Was not Abraham our father justified by works, in that he offered up Isaac his son upon the altar?22 Thou seest that faith wrought with his works, and by works was faith made perfect;23 and the scripture was fulfilled which saith, And Abraham believed God, and it was reckoned unto him for righteousness; and he was called the friend of God.24 Ye see that by works a man is justified, and not only by faith.25 And in like manner was not also Rahab the harlot justified by works, in that she received the messengers, and sent them out another way?26 For as the body apart from the spirit is dead, even so faith apart from works is dead.