previous next

YAK 3

Ɓarnar Harshe

1 Ya ku 'yan'uwana, kada yawancinku su zama masu koyarwa, domin kun sani, mu da muke koyarwa za a yi mana shari'a da ƙididdiga mafi tsanani. 2 t Domin dukanmu muna yin kuskure da yawa. In kuwa mutum ba ya shirme a maganarsa, to, shi cikakken mutum ne, yana kuwa iya kame duk sauran gaɓoɓinsa ma. 3 t Ga misali, idan mun sa linzami a bakin doki, don mu bi da shi, mukan sarrafa dukan jikinsa ma. 4 Ku dubi jiragen ruwa kuma, ko da yake suna da girma haka ƙaƙƙarfar iska kuma tana kora su, duk da haka, da ɗan ƙaramin ƙarfe ne matuƙi yake juya su duk inda ya nufa.

5 t Haka ma harshe yake, ga shi, ɗan ƙaramin abu ne, sai manyan fariya! Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake kunna wa babban jeji wuta!
6  t Harshe ma wuta ne fa! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata dukan jiki, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa Gidan Wuta ne yake zuga shi. 7 Don kuwa ana iya sarrafa kowace irin dabba, da tsuntsu, da masu jan ciki, da halittar ruwa, ɗan adam har yā sarrafa su ma, 8 t amma ba ɗan adam ɗin da zai iya sarrafa harshe, ai, mugunta ne da ba ta hanuwa, a cike yake da dafi mai kashewa. 9 t Da shi muke yabon Ubangiji Uba, da shi kuma muke zagin mutane waɗanda aka halitta da kamannin Allah. 10 Da baki ɗaya ake yabo, ake kuma zagi. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba! 11 Ashe, marmaro ɗaya ya iya ɓuɓɓugowa da ruwan daɗi da na zartsi ta ido guda?

12 t Ya 'yan'uwana, ashe, ɓaure yana iya haifar zaitun? Ko kuwa inabi ya haifi ɓaure? Haka kuma, ba dama a sami ruwan daɗi a idon ruwan zartsi.

Hikima Mai Saukowa daga Sama


13  t Ina mai hikima da fahimi a cikinku? To, ta kyakkyawan zamansa sai ya nuna aikinsa da halin tawali'u da hikima suke sawa. 14 t Amma in kuna da matsanancin kishi da sonkai a zuciyarku, kada ku yi alwashi da haka, kuna saɓa wa gaskiya. 15 t Wannan hikima ba irin wadda take saukowa daga Sama ba ce, ta duniya ce, ta son zuciya , ta Shaiɗan kuma. 16 A duk inda kishi da sonkai suke, a nan hargitsi da kowane irin mugun aiki ma suke. 17 t Amma hikimar nan ta Sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, saliha ce, mai sauƙin kai, mai tsananin jinƙai, mai yawan alheri, mai kaifi ɗaya, sahihiya kuma. 18 t Daga irin salama wanda masu sulhuntawa suke shukawa akan girbe adalci.

James 3

1 Be not many of you teachers, my brethren, knowing that we shall receive heavier judgment.2 For in many things we all stumble. If any stumbleth not in word, the same is a perfect man, able to bridle the whole body also.3 Now if we put the horses’ bridles into their mouths that they may obey us, we turn about their whole body also.4 Behold, the ships also, though they are so great and are driven by rough winds, are yet turned about by a very small rudder, whither the impulse of the steersman willeth.5 So the tongue also is a little member, and boasteth great things. Behold, how much wood is kindled by how small a fire!6 And the tongue is a fire: the world of iniquity among our members is the tongue, which defileth the whole body, and setteth on fire the wheel of nature, and is set on fire by hell.7 For every kind of beasts and birds, of creeping things and things in the sea, is tamed, and hath been tamed by mankind.8 But the tongue can no man tame; it is a restless evil, it is full of deadly poison.9 Therewith bless we the Lord and Father; and therewith curse we men, who are made after the likeness of God:10 out of the same mouth cometh forth blessing and cursing. My brethren, these things ought not so to be.11 Doth the fountain send forth from the same opening sweet water and bitter?12 Can a fig tree, my brethren, yield olives, or a vine figs? Neither can salt water yield sweet.13 Who is wise and understanding among you? let him show by his good life his works in meekness of wisdom.14 But if ye have bitter jealousy and faction in your heart, glory not and lie not against the truth.15 This wisdom is not a wisdom that cometh down from above, but is earthly, sensual, devilish.16 For where jealousy and faction are, there is confusion and every vile deed.17 But the wisdom that is from above is first pure, then peaceable, gentle, easy to be entreated, full of mercy and good fruits, without variance, without hypocrisy.18 And the fruit of righteousness is sown in peace for them that make peace.