previous next

YAH 10

Misali na Garken Tumaki

1 “Lalle hakika, ina gaya muku, wanda bai shiga garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya haura ta wani gu, to, shi ɓarawo ne, ɗan fashi kuma. 2 t Wanda kuwa ya shiga ta ƙofar, makiyayin tumakin ne. 3 t Mai tsaron ƙofar yakan buɗe masa, tumakin kuma sukan saurari murya tasa, yakan kama sunan nasa tumaki, ya kai su waje. 4 Bayan ya fitar da dukan nasa waje, sai ya shige gabansu, tumakin na biye da shi, domin sun san murya tasa. 5 Ba za su bi baƙo ba, sai dai su guje shi, don ba su san muryar baƙo ba.”

6 t Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su gane abin da ya faɗa musu ba.

Yesu Ne Makiyayi Mai Kyau


7 Don haka Yesu ya sāke ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ni ne ƙofar tumakin. 8 t Duk waɗanda suka riga ni zuwa cewa, su ne ni, ɓarayi ne, 'yan fashi kuma, amma tumakin ba su kula da su ba. 9 Ni ne ƙofar. Kowa ya shiga ta wurina zai sami ceto, ya kai ya kawo, ya kuma yi kiwo. 10 Ɓarawo yakan zo ne kawai don sata da kisa da hallakarwa. Ni kuwa na zo ne domin su sami rai, su kuma same shi a yalwace. 11 t Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau kuwa shi ne mai ba da ransa domin tumakin. 12 t Wanda yake ɗan asako kuwa, ba makiyayin gaske ba, tumakin kuma ba nasa ba, da ganin kyarkeci ya doso, sai ya watsar da tumakin, ya yi ta kansa, kyarkeci kuwa ya sure waɗansu, ya fasa sauran. 13 Ya gudu ne fa, don shi ɗan asako ne, ba abin da ya dame shi da tumakin. 14 t Ni ne Makiyayi mai kyau. Na san nawa, nawa kuma sun san ni, 15 t kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uban. Ina ba da raina maimakon tumakin. 16 t Ina kuma da waɗansu tumaki da ba na wannan garke ba ne. Su ma lalle in kawo su, za su kuwa saurari muryata, su zama garke guda, makiyayi kuma guda. 17 t Domin wannan uba yake ƙaunata, domin ina ba da raina in ɗauko shi kuma.

18 t Ba mai karɓe mini rai, don kaina nake ba da shi. Ina da ikon ba da shi, ina da ikon ɗauko shi kuma. Na karɓo wannan umarni ne daga wurin Ubana.”
19  t Saboda maganan nan fa, sai rabuwa ta sāke shiga tsakanin Yahudawa. 20 t Da yawa daga cikinsu suka ce, “Ai, mai iska ne, haukansa kawai yake yi. Don me za ku saurare shi?”

21 t Waɗansu kuwa suka ce, “A'a, wannan magana, ai, ba ta mai iska ba ce. Ashe, iska tana iya buɗe wa makaho ido?”

Yahudawa Sun Ƙi Yesu


22 Lokacin idin tsarkakewa ne kuwa a Urushalima, 23 t damuna ce kuma, Yesu kuwa na zagawa a Shirayin Sulemanu cikin Haikali, 24 t sai Yahudawa suka kewaye shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu da shakka? In dai kai ne Almasihun, ka gaya mana a fili.” 25 t Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, na faɗa muku, ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi da sunan Ubana, suke shaidata. 26 t Amma ku ba ku gaskata ba, domin ba kwa cikin tumakina. 27 t Tumakin nan nawa sukan saurari muryata, na san su, suna kuma bi na. 28 t Ina ba su rai madawwami, ba kuwa za su halaka ba har abada, ba kuma mai ƙwace su daga hannuna. 29 t Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba kuwa mai iya ƙwace su daga ikon Uban.

30 t Ni da Uba ɗaya muke.”
31  t Sai Yahudawa suka sāke ɗebo duwatsu su jajjefe shi. 32 Yesu ya amsa musu ya ce, “Na nuna muku ayyuka nagari masu yawa daga wurin Uba, a kan wanne a cikinsu za ku jajjefe ni?” 33 t Yahudawa suka amsa suka ce, “Ba don wani aiki nagari za mu jajjefe ka ba, sai don sāɓo, don kai, ga ka mutum, amma kana mai da kanka Allah.” 34 t Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a Shari'arku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne’? 35 To, in waɗanda Maganar Allah ta zo musu ya ce da su alloli (Nassi kuwa ba ya tashi), 36 t kwa ce da wanda Uba ya keɓe, ya kuma aiko duniya, ‘Sāɓo kake,’ domin na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne’? 37 t In ba ayyukan da Ubana yake yi nake yi ba, to, kada ku gaskata ni. 38 t Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uba na cikina, ni kuma ina cikin Uba.”

39 t Sai suka sāke ƙoƙarin kama shi, amma ya fita daga hannunsu.
40  t Sa'an nan ya sāke komawa hayin Kogin Urdun, wurin da Yahaya ya fara yin baftisma, ya zauna a can, 41 t mutane kuwa da yawa suka zo wurinsa, sai suka riƙa cewa, “Hakika, Yahaya bai yi wata mu'ujiza ba, amma duk abin da ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.” 42 t Nan fa mutane da yawa suka gaskata da shi.

John 10

1 Verily, verily, I say unto you, He that entereth not by the door into the fold of the sheep, but climbeth up some other way, the same is a thief and a robber.2 But he that entereth in by the door is the shepherd of the sheep.3 To him the porter openeth; and the sheep hear his voice: and he calleth his own sheep by name, and leadeth them out.4 When he hath put forth all his own, he goeth before them, and the sheep follow him: for they know his voice.5 And a stranger will they not follow, but will flee from him: for they know not the voice of strangers.6 This parable spake Jesus unto them: but they understood not what things they were which he spake unto them.7 Jesus therefore said unto them again, Verily, verily, I say unto you, I am the door of the sheep.8 All that came before me are thieves and robbers: but the sheep did not hear them.9 I am the door; by me if any man enter in, he shall be saved, and shall go in and go out, and shall find pasture.10 The thief cometh not, but that he may steal, and kill, and destroy: I came that they may have life, and may have it abundantly.11 I am the good shepherd: the good shepherd layeth down his life for the sheep.12 He that is a hireling, and not a shepherd, whose own the sheep are not, beholdeth the wolf coming, and leaveth the sheep, and fleeth, and the wolf snatcheth them, and scattereth them:13 he fleeth because he is a hireling, and careth not for the sheep.14 I am the good shepherd; and I know mine own, and mine own know me,15 even as the Father knoweth me, and I know the Father; and I lay down my life for the sheep.16 And other sheep I have, which are not of this fold: them also I must bring, and they shall hear my voice: and they shall become one flock, one shepherd.17 Therefore doth the Father love me, because I lay down my life, that I may take it again.18 No one taketh it away from me, but I lay it down of myself. I have power to lay it down, and I have power to take it again. This commandment received I from my Father.19 There arose a division again among the Jews because of these words.20 And many of them said, He hath a demon, and is mad; why hear ye him?21 Others said, These are not the sayings of one possessed with a demon. Can a demon open the eyes of the blind?22 And it was the feast of the dedication at Jerusalem:23 it was winter; and Jesus was walking in the temple in Solomon’s porch.24 The Jews therefore came round about him, and said unto him, How long dost thou hold us in suspense? If thou art the Christ, tell us plainly.25 Jesus answered them, I told you, and ye believe not: the works that I do in my Father’s name, these bear witness of me.26 But ye believe not, because ye are not of my sheep.27 My sheep hear my voice, and I know them, and they follow me:28 and I give unto them eternal life; and they shall never perish, and no one shall snatch them out of my hand.29 My Father, who hath given them unto me, is greater than all; and no one is able to snatch them out of the Father’s hand.30 I and the Father are one.31 The Jews took up stones again to stone him.32 Jesus answered them, Many good works have I showed you from the Father; for which of those works do ye stone me?33 The Jews answered him, For a good work we stone thee not, but for blasphemy; and because that thou, being a man, makest thyself God.34 Jesus answered them, Is it not written in your law, I said, ye are gods?35 If he called them gods, unto whom the word of God came (and the scripture cannot be broken),36 say ye of him, whom the Father sanctified and sent into the world, Thou blasphemest; because I said, I am the Son of God?37 If I do not the works of my Father, believe me not.38 But if I do them, though ye believe not me, believe the works: that ye may know and understand that the Father is in me, and I in the Father.39 They sought again to take him: and he went forth out of their hand.40 And he went away again beyond the Jordan into the place where John was at the first baptizing; and there be abode.41 And many came unto him; and they said, John indeed did no sign: but all things whatsoever John spake of this man were true.42 And many believed on him there.