YAH 11
Mutuwar Li'azaru
1 t Wani mutum ne ya yi rashin lafiya, sunansa Li'azaru na Betanya, ƙauyen su Maryamu da 'yar'uwarta Marta. 2 t Maryamun nan kuwa, wadda ɗan'uwanta Li'azaru ba shi da lafiya, ita ce wadda ta shafa wa Ubangiji man ƙanshi, ta kuma shafe ƙafafunsa da gashinta. 3 t To, 'yan'uwan nan mata suka aika masa, suka ce, “Ya Ubangiji, ga shi, wanda kake ƙaunan nan ba shi da lafiya.”
4 t Da Yesu ya ji haka ya ce, “Wannan rashin lafiya, ƙarshensa ba mutuwa ba ne, domin a ɗaukaka Allah ne, a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurinsa.”
5 Yesu kuwa na ƙaunar Marta da 'yar'uwarta, da kuma Li'azaru. 6 To, da ya ji Li'azaru ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu. 7 t Bayan haka ya ce wa almajiran, “Mu koma ƙasar Yahudiya.” 8 t Almajiran suka ce masa, “Ya Shugaba, kwana kwanan nan fa Yahudawa suke neman jifanka, za ka sāke komawa can?” 9 t Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa'a goma sha biyu ce yini ɗaya ba? Kowa yake tafiya da rana ba ya tuntuɓe, don yana ganin hasken duniyan nan. 10 Amma kowa yake tafiya da dare yakan yi tuntuɓe, don ba haske a gare shi!” 11 t Ya faɗi haka, sa'an nan ya ƙara ce musu, “Amininmu Li'azaru ya yi barci, amma za ni in tashe shi.” 12 Sai almajiran suka ce masa, “Ya Ubangiji, in dai barci ne ya ɗauke shi, ai, zai warke.” 13 t Alhali kuwa, Yesu zancen mutuwar Li'azaru yake, amma su sun ɗauka yana nufin barcin hutawa ne. 14 Sai Yesu ya gaya musu a fili, ya ce, “Li'azaru dai ya mutu. 15 Ina kuwa farin ciki da ba na nan, saboda ku domin ku ba da gaskiya. Amma mu dai je wurinsa.”
16 t Sai Toma, wanda ake kira Ɗan Tagwai, ya ce wa 'yan'uwansa almajirai, “Mu ma mu tafi, mu mutu tare da shi.”Yesu Shi Ne Tashin Matattu da Rai Kuma
17 t Da Yesu ya isa, ya tarar Li'azaru, har ya kwana huɗu a kabari. 18 t Betanya kuwa kusa da Urushalima take, misalin mil biyu. 19 t Yahudawa da yawa sun zo su yi wa Marta da Maryamu ta'aziyyar ɗan'uwansu. 20 t Da jin Yesu na zuwa, sai Marta ta je taryensa, Maryamu kuwa ta zauna a gida. 21 t Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, da kana nan da ɗan'uwana bai mutu ba. 22 t Ko yanzu ma na sani kome ka roƙi Allah zai yi maka.” 23 Yesu ya ce mata, “Ɗan'uwanki zai tashi.” 24 t Marta ta ce masa, “Na sani zai tashi a tashin matattu a ranar ƙarshe.” 25 t Yesu ya ce mata, “Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu. 26 Wanda kuwa yake raye, yake kuma gaskatawa da ni, ba zai mutu ba har abada. Kin gaskata wannan?”
27 t Ta ce masa, “I, ya Ubangiji. Na gaskata kai ne Almasihu, Ɗan Allah, shi wannan mai zuwa duniya.”Yesu Ya Yi Hawaye
28 t Da ta faɗi haka, ta je ta kirawo 'yar'uwa tata Maryamu, ta raɗa mata ta ce, “Ga Malam ya zo, yana kiranki.” 29 Ita kuwa da jin haka, ta yi maza ta tashi ta nufi wurinsa. 30 t Yesu dai bai iso ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana wurin da Marta ta tarye shi. 31 t Da Yahudawan da suke tare da ita a cikin gida, suna yi mata ta'aziyya, suka ga Maryamu ta yi maza ta tashi ta fita, suka bi ta, suna zaton za ta kabarin ne, ta yi kuka a can. 32 t Da Maryamu ta iso inda Yesu yake, ta gan shi, sai ta faɗi a gabansa ta ce masa, “Ya Ubangiji, da kana nan da dan'uwana bai mutu ba.” 33 t Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita su ma, suna kuka, sai ya nisa a ransa, ya yi juyayi gaya. 34 Ya kuma ce, “Ina kuka sa shi?” Suka ce masa, “Ya Ubangiji, zo ka gani.” 35 t Sai Yesu ya yi hawaye. 36 t Don haka Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!”
37 t Amma waɗansunsu suka ce, “Ashe, wanda ya buɗe wa makahon nan ido, ba zai iya hana wannan mutum mutuwa ba?”Yesu Ya Ta da Li'azaru daga Matattu
38 t Sai Yesu ya sāke nisawa a ransa, ya iso kabarin. Kabarin kuwa kogon dutse ne, da wani dutse kuma an rufe bakin. 39 t Yesu ya ce, “Ku kawar da dutsen.” Sai Marta, 'yar'uwar mamacin, ta ce masa, “Ya Ubangiji, ai, yanzu ya yi ɗoyi, don yau kwanansa huɗu ke nan da mutuwa.” 40 t Sai Yesu ya ce mata, “Ban gaya miki ba, in kin ba da gaskiya za ki ga ɗaukakar Allah?” 41 t Sai suka kawar da dutsen. Yesu kuwa ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, na gode maka da ka saurare ni. 42 t Ko dā ma na sani koyaushe kana saurarona, amma na faɗi haka ne saboda jama'ar da suke nan tsaitsaye, domin su gaskata kai ne ka aiko ni.” 43 t Da ya faɗi haka ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Li'azaru fito!”
44 t Sai mamacin ya fito, ƙafa da hannu a ɗaure da likkafani, fuska tasa kuma a naɗe da mayani. Yesu ya ce musu, “Ku kwance masa, ya tafi.”An Kulla Shawara Gāba da Yesu
(Mat 26.1-5; Mar 14.1-2; Luka 22.1-2)
45 t Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo wurin Maryamu, suka kuma ga abin da ya yi, suka gaskata da shi. 46 Amma waɗansunsu suka tafi wurin Farisiyawa, suka gaya musu abin da Yesu ya yi. 47 t Don haka manyan firistoci da Farisiyawa suka tara 'yan majalisa, suka ce, “Shin, me muke yi ne, har mutumin nan yake ta yin mu'ujizai da yawa haka? 48 In fa muka ƙyale shi kan haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma za su zo su karɓe ƙasarmu su ɗebe jama'armu.” 49 t Amma ɗayansu, wai shi Kayafa, wanda yake shi ne babban firist a shekaran nan, ya ce musu, “Ku dai ba ku san kome ba. 50 t Ba kwa lura, ai, ya fiye muku mutum ɗaya ya mutu saboda jama'a, da duk jama'a ta halaka.” 51 Ba da nufinsa ya faɗi haka ba, sai dai da yake shi ne babban firist a shekaran nan, ya yi annabci cewa, Yesu zai mutu saboda jama'a, 52 t ba ma saboda jama'a kaɗai ba, har ma yă tattaro 'ya'yan Allah da suke warwatse ko'ina su zama ɗaya.
53 t Daga ran nan fa sai suka ƙulla su kashe shi.
54 t Saboda haka, Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba, amma ya tashi daga wurin, ya tafi ƙasar da take a bakin jeji, ya shiga wani gari, mai suna Ifraimu. Nan ya zauna da almajiran.
55 t Ana nan, Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya gabato, mutane da yawa daga ƙauye suka tafi Urushalima su tsarkake kansa kafin idin. 56 t Suka yi ta neman Yesu, suna tsaitsaye a Haikali, suna ce wa juna, “Me kuka gani? Zai zo idin kuwa?” 57 Don dā ma, manyan firistoci da Farisiyawa sun yi umarni, cewa kowa ya san inda Yesu yake, ya zo ya faɗa, su kama shi.
John 11
1 Now a certain man was sick, Lazarus of Bethany, of the village of Mary and her sister Martha.2 And it was that Mary who anointed the Lord with ointment, and wiped his feet with her hair, whose brother Lazarus was sick.3 The sisters therefore sent unto him, saying, Lord, behold, he whom thou lovest is sick.4 But when Jesus heard it, he said, This sickness is not unto death, but for the glory of God, that the Son of God may be glorified thereby.5 Now Jesus loved Martha, and her sister, and Lazarus.6 When therefore he heard that he was sick, he abode at that time two days in the place where he was.7 Then after this he saith to the disciples, Let us go into Judaea again.8 The disciples say unto him, Rabbi, the Jews were but now seeking to stone thee; and goest thou thither again?9 Jesus answered, Are there not twelve hours in the day? If a man walk in the day, he stumbleth not, because he seeth the light of this world.10 But if a man walk in the night, he stumbleth, because the light is not in him.11 These things spake he: and after this he saith unto them, Our friend Lazarus is fallen asleep; but I go, that I may awake him out of sleep.12 The disciples therefore said unto him, Lord, if he is fallen asleep, he will recover.13 Now Jesus had spoken of his death: but they thought that he spake of taking rest in sleep.14 Then Jesus therefore said unto them plainly, Lazarus is dead.15 And I am glad for your sakes that I was not there, to the intent ye may believe; nevertheless let us go unto him.16 Thomas therefore, who is called Didymus, said unto his fellow-disciples, Let us also go, that we may die with him.17 So when Jesus came, he found that he had been in the tomb four days already.18 Now Bethany was nigh unto Jerusalem, about fifteen furlongs off;19 and many of the Jews had come to Martha and Mary, to console them concerning their brother.20 Martha therefore, when she heard that Jesus was coming, went and met him: but Mary still sat in the house.21 Martha therefore said unto Jesus, Lord, if thou hadst been here, my brother had not died.22 And even now I know that, whatsoever thou shalt ask of God, God will give thee.23 Jesus saith unto her, Thy brother shall rise again.24 Martha saith unto him, I know that he shall rise again in the resurrection at the last day.25 Jesus said unto her, I am the resurrection, and the life: he that believeth on me, though he die, yet shall he live;26 and whosoever liveth and believeth on me shall never die. Believest thou this?27 She saith unto him, Yea, Lord: I have believed that thou art the Christ, the Son of God, even he that cometh into the world.28 And when she had said this, she went away, and called Mary her sister secretly, saying, The Teacher is here, and calleth thee.29 And she, when she heard it, arose quickly, and went unto him.30 (Now Jesus was not yet come into the village, but was still in the place where Martha met him.)31 The Jews then who were with her in the house, and were consoling her, when they saw Mary, that she rose up quickly and went out, followed her, supposing that she was going unto the tomb to weep there.32 Mary therefore, when she came where Jesus was, and saw him, fell down at his feet, saying unto him, Lord, if thou hadst been here, my brother had not died.33 When Jesus therefore saw her weeping, and the Jews also weeping who came with her, he groaned in the spirit, and was troubled,34 and said, Where have ye laid him? They say unto him, Lord, come and see.35 Jesus wept.36 The Jews therefore said, Behold how he loved him!37 But some of them said, Could not this man, who opened the eyes of him that was blind, have caused that this man also should not die?38 Jesus therefore again groaning in himself cometh to the tomb. Now it was a cave, and a stone lay against it.39 Jesus saith, Take ye away the stone. Martha, the sister of him that was dead, saith unto him, Lord, by this time the body decayeth; for he hath been dead four days.40 Jesus saith unto her, Said I not unto thee, that, if thou believedst, thou shouldest see the glory of God?41 So they took away the stone. And Jesus lifted up his eyes, and said, Father, I thank thee that thou heardest me.42 And I knew that thou hearest me always: but because of the multitude that standeth around I said it, that they may believe that thou didst send me.43 And when he had thus spoken, he cried with a loud voice, Lazarus, come forth.44 He that was dead came forth, bound hand and foot with grave-clothes; and his face was bound about with a napkin. Jesus saith unto them, Loose him, and let him go.45 Many therefore of the Jews, who came to Mary and beheld that which he did, believed on him.46 But some of them went away to the Pharisees, and told them the things which Jesus had done.47 The chief priests therefore and the Pharisees gathered a council, and said, What do we? for this man doeth many signs.48 If we let him thus alone, all men will believe on him: and the Romans will come and take away both our place and our nation.49 But a certain one of them, Caiaphas, being high priest that year, said unto them, Ye know nothing at all,50 nor do ye take account that it is expedient for you that one man should die for the people, and that the whole nation perish not.51 Now this he said not of himself: but, being high priest that year, he prophesied that Jesus should die for the nation;52 and not for the nation only, but that he might also gather together into one the children of God that are scattered abroad.53 So from that day forth they took counsel that they might put him to death.54 Jesus therefore walked no more openly among the Jews, but departed thence into the country near to the wilderness, into a city called Ephraim; and there he tarried with the disciples.55 Now the passover of the Jews was at hand: and many went up to Jerusalem out of the country before the passover, to purify themselves.56 They sought therefore for Jesus, and spake one with another, as they stood in the temple, What think ye? That he will not come to the feast?57 Now the chief priests and the Pharisees had given commandment, that, if any man knew where he was, he should show it, that they might take him.