previous next

YAH 13

Yesu Ya Wanke Ƙafafun Almajiransa

1  t Ana nan tun kafin Idin Ƙetarewa, da Yesu ya san lokacinsa ya yi da zai tashi daga wannan duniya ya koma wurin Uba, da yake ya ƙaunaci mutanensa da suke duniya, ya ƙaunace su har matuƙa. 2 Ana cikin cin abincin dare, Iblis kuwa ya riga ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti ɗan Saminu yă bāshe shi. 3 t Yesu kuwa, da yake ya san Uba ya sa kome a hannunsa, ya kuma sani daga wurin Allah ya fito, wurin Allah kuma zai koma, 4 sai ya tashi daga cin abincin, ya ajiye mayafinsa, ya ɗauko ɗan zane ya yi ɗamara da shi. 5 t Sa'an nan ya zuba ruwa a daro, ya fara wanke ƙafafun almajiran, yana shafe su da abin da ya yi ɗamara da shi. 6 Sai ya zo kan Bitrus, shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ashe, kai ne za ka wanke mini ƙafa?” 7 t Yesu ya amsa ya ce, “Yanzu kam, ba ka san abin da nake yi ba, amma daga baya za ka fahimta.” 8 Bitrus ya ce masa, “Wane ni! Ai, ba za ka wanke mini ƙafa ba har abada!” Yesu ya amsa masa ya ce, “In ban wanke maka ba, ba ka da rabo a gare ni.” 9 Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ba ma ƙafafuna kaɗai ba, har ma da hannuwana da kaina!” 10 t Yesu ya ce masa, “Wanda ya yi wanka ba ya bukatar wanke kome, sai ƙafafunsa kawai, domin ya riga ya tsarkaka sarai. Ku ma tsarkakakku ne, amma ba dukanku ne ba.”

11 Don ya san wanda zai bāshe shi, shi ya sa ya ce, “Ba dukanku ne tsarkakakku ba.”
12 Bayan ya wanke ƙafafunsu, ya yafa mayafinsa, sai ya sāke kishingiɗa, ya ce musu, “Kun gane abin da na yi muku? 13 t Kuna kirana Malam, da kuma Ubangiji. Daidai ne kuwa, don haka nake. 14 t Tun da yake ni Ubangijinku da kuma Malaminku, har na wanke muku ƙafa, ashe, ku ma wajibi ne ku wanke wa juna. 15 t Na yi muku ishara domin ku ma ku yi yadda na yi muku 16 t Lalle hakika, ina gaya muku, bawa ba ya fin ubangijinsa, manzo kuma ba ya fin wanda ya aiko shi. 17 t In dai kun san wannan, kuna kuma aikatawa, ku masu farin ciki ne. 18 t Ba dukanku nake nufi ba. Na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa duk domin a cika Nassi ne cewa, ‘Wanda yake cin abincina ya tasar mini.’ 19 t Tun yanzu zan sanar da ku abu tun bai faru ba, domin sa'ad da ya faru ku ba da gaskiya ni ne shi.

20 t Lalle hakika, ina gaya muku, wanda ya yi na'am da duk wanda na aiko, ya yi na'am da ni ke nan. Wanda ya yi na'am da ni kuwa, to, ya yi na'am da wanda ya aiko ni.”

Yesu Ya Ce Za a Bāshe Shi

(Mat 26.20-25; Mar 14.17-21; Luka 22.21-23)


21  t Bayan da Yesu ya faɗi haka, ya ji nauyi a ransa, ya yi shaida ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bāshe ni.” 22 Sai almajiran suka duddubi juna, suka rasa da wanda yake. 23 t Wani daga cikin almajiransa kuwa, wanda Yesu yake ƙauna, yana kishingiɗe gab da Yesu. 24 Sai Bitrus ya alamta masa ya ce, “Gaya mana, da wa yake?” 25 t Shi kuwa da yake kishingiɗe haka gab da Yesu ya karkata, ya ce masa, “Ya Ubangiji, wane ne?” 26 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan tsoma 'yar lomar nan in ba shi.” Da ya tsoma 'yar lomar kuwa, sai ya ba Yahuza, Ɗan Saminu Iskariyoti. 27 t Da karɓar 'yar loman nan Shaiɗan ya shige shi. Yesu ya ce masa, “Yi abin da za ka yi, maza.” 28 Amma cikin waɗanda suke cin abinci, ba wanda ya san dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka. 29 t Har waɗansu ma sun yi zaton Yesu ya ce masa ya yi musu sayayyar idi ne, ko kuwa ya ba gajiyayyu wani abu, don Yahuza ne yake riƙe da jakar kuɗinsu.

30 t Shi kuwa da karɓar 'yar lomar, sai ya fita, da dare ne kuwa.

Sabon Umarni


31  t Bayan ya fita kuma sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum, aka kuma ɗaukaka Allah ta wurinsa. 32 t Allah kuma zai ɗaukaka shi zuwa ga zatinsa, nan da nan kuwa zai ɗaukaka shi. 33 t Ya ku 'ya'yana ƙanana, saura ɗan lokaci kaɗan ina tare da ku. Za ku neme ni, amma kamar yadda na faɗa wa Yahudawa cewa, ‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba,’ haka nake faɗa muku yanzu. 34 t Sabon umarni nake ba ku, shi ne ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma, ku ƙaunaci juna.

35 t Ta haka, kowa zai gane ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.”

Bitrus Zai Yi Musun Sanin Yesu

(Mat 26.31-35; Mar 14.27-31; Luka 22.31-34)


36  t Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Inda za ni, ba za ka iya bina yanzu ba, amma daga baya za ka bi ni.” 37 Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, don me, ba zan iya binka a yanzu ba? Ai, zan ba da raina saboda kai.” 38 t Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, za ka ba da ranka saboda ni? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara, za ka yi musun sanina sau uku.”

John 13

1 Now before the feast of the passover, Jesus knowing that his hour was come that he should depart out of this world unto his Father, having loved his own that were in the world, he loved them unto the end.2 And during supper, the devil having already put into the heart of Judas Iscariot, Simon’s son, to betray him,3 Jesus, knowing that the Father had given all the things into his hands, and that he came forth from God, and goeth unto God,4 riseth from supper, and layeth aside his garments; and he took a towel, and girded himself.5 Then he poureth water into the basin, and began to wash the disciples’ feet, and to wipe them with the towel wherewith he was girded.6 So he cometh to Simon Peter. He saith unto him, Lord, dost thou wash my feet?7 Jesus answered and said unto him, What I do thou knowest not now; but thou shalt understand hereafter.8 Peter saith unto him, Thou shalt never wash my feet. Jesus answered him, If I wash thee not, thou hast no part with me.9 Simon Peter saith unto him, Lord, not my feet only, but also my hands and my head.10 Jesus saith to him, He that is bathed needeth not save to wash his feet, but is clean every whit: and ye are clean, but not all.11 For he knew him that should betray him; therefore said he, Ye are not all clean.12 So when he had washed their feet, and taken his garments, and sat down again, he said unto them, Know ye what I have done to you?13 Ye call me, Teacher, and, Lord: and ye say well; for so I am.14 If I then, the Lord and the Teacher, have washed your feet, ye also ought to wash one another’s feet.15 For I have given you an example, that ye also should do as I have done to you.16 Verily, verily, I say unto you, a servant is not greater than his lord; neither one that is sent greater than he that sent him.17 If ye know these things, blessed are ye if ye do them.18 I speak not of you all: I know whom I have chosen: but that the scripture may be fulfilled: He that eateth my bread lifted up his heel against me.19 From henceforth I tell you before it come to pass, that, when it is come to pass, ye may believe that I am he.20 Verily, verily, I say unto you, he that receiveth whomsoever I send receiveth me; and he that receiveth me receiveth him that sent me.21 When Jesus had thus said, he was troubled in the spirit, and testified, and said, Verily, verily, I say unto you, that one of you shall betray me.22 The disciples looked one on another, doubting of whom he spake.23 There was at the table reclining in Jesus’ bosom one of his disciples, whom Jesus loved.24 Simon Peter therefore beckoneth to him, and saith unto him, Tell us who it is of whom he speaketh.25 He leaning back, as he was, on Jesus’ breast saith unto him, Lord, who is it?26 Jesus therefore answereth, He it is, for whom I shall dip the sop, and give it him. So when he had dipped the sop, he taketh and giveth it to Judas, the son of Simon Iscariot.27 And after the sop, then entered Satan into him. Jesus therefore saith unto him, What thou doest, do quickly.28 Now no man at the table knew for what intent he spake this unto him.29 For some thought, because Judas had the bag, that Jesus said unto him, Buy what things we have need of for the feast; or, that he should give something to the poor.30 He then having received the sop went out straightway: and it was night.31 When therefore he was gone out, Jesus saith, Now is the Son of man glorified, and God is glorified in him;32 and God shall glorify him in himself, and straightway shall he glorify him.33 Little children, yet a little while I am with you. Ye shall seek me: and as I said unto the Jews, Whither I go, ye cannot come; so now I say unto you.34 A new commandment I give unto you, that ye love one another; even as I have loved you, that ye also love one another.35 By this shall all men know that ye are my disciples, if ye have love one to another.36 Simon Peter saith unto him, Lord, whither goest thou? Jesus answered, Whither I go, thou canst not follow now; but thou shalt follow afterwards.37 Peter saith unto him, Lord, why cannot I follow thee even now? I will lay down my life for thee.38 Jesus answereth, Wilt thou lay down thy life for me? Verily, verily, I say unto thee, The cock shall not crow, till thou hast denied me thrice.