previous next

YAH 14

Yesu Ne Hanya zuwa Wurin Uban

1  t “Kada ku damu. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. 2 t A gun Ubana akwai wurin zama da yawa. Da ba haka ne ba, da na faɗa muku, domin zan tafi in shirya muku wuri. 3 t In kuwa na je na shirya muku wuri, sai in dawo in kai ku wurina, domin inda nake, ku ma ku zama kuna can. 4 Inda za ni kuwa kun san hanya.” 5 t Sai Toma ya ce masa, “Ya Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, ƙaƙa za mu san hanyar?” 6 t Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina.

7 t Da kun san ni, da kun san Ubana ma. Amma daga yanzu kun san shi, kun kuma gan shi.”
8 Sai Filibus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka nuna mana Uban, bukatarmu ta biya ke nan.” 9 t Yesu ya ce masa, “Na daɗe tare da ku haka, amma har yanzu ba ka san ni ba, Filibus? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Nuna mana Uban’ ”? 10 t Wato ba ka gaskata ba cikin Uba nake, Uba kuma cikina? Maganar da nake faɗa muku, ba domin kaina nake faɗa ba, Uba ne da yake zaune a cikina yake yin ayyukansa.

11 t Ku gaskata ni, a cikin Uba nake, Uba kuma cikina, ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan kansu.
12  t “Lalle hakika, ina gaya muku, duk wanda yake gaskatawa da ni ayyukan da nake yi shi ma haka zai yi. Har ma, zai yi ayyukan da suka fi waɗannan, domin zan tafi wurin Uba. 13 t Duk abin da kuka roƙa da sunana kuma zan yi, domin a ɗaukaka Uban ta wurin Ɗan.

14 Kome kuke roƙa da sunana, zan yi shi.”

Alkawarin Zuwan Ruhu Mai Tsarki


15  t “In dai kuna ƙaunata, za ku bi umarnina. 16 t Ni ma zan roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimako ya kasance tare da ku har abada.

17 t Shi ne Ruhu na gaskiya, wanda duniya ba ta iya samunsa, domin ba ta ganinsa, ba ta kuma san shi ba. Ku kam, kun san shi, domin yana zaune tare da ku, zai kuma kasance a zuciyarku.
18  t “Ba zan bar ku marayu ba, zan zo wurinku. 19 t Saura ɗan lokaci kaɗan duniya ba za ta ƙara ganina ba, amma ku za ku gan ni. Saboda ni a raye nake, ku ma za ku rayu. 20 t A ran nan ne fa za ku sani, ni cikin Uba nake, ku kuma a cikina, ni kuma a cikinku. 21 t Duk wanda ya san umarnaina, yake kuma binsu, shi ne mai ƙaunata. Mai ƙaunata kuwa, Ubana zai ƙaunace shi, ni kuma zan ƙaunace shi, in bayyana kaina gare shi.” 22 t Sai Yahuza (ba Iskariyoti ba) ya ce masa, “Ya Ubangiji, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu, ba ga duniya ba?” 23 t Yesu ya amsa masa ya ce, “Kowa yake ƙaunata, zai kiyaye maganata, Ubana kuwa zai ƙaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi.

24 t Wanda ba ya ƙaunata, ba ya kiyaye maganata. Maganar da kuke ji kuwa ba tawa ba ce, ta Uba ce wanda ya aiko ni.
25 “Duk wannan na faɗa muku ne tun muna tare. 26 t Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko da sunana, shi ne zai koya muku kome, ya kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku. 27 t Na bar ku da salama. Salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada ku damu, kada kuma ku ji tsoro. 28 t Kun dai ji na ce muku zan tafi, in kuma dawo wurinku. Da kuna ƙaunata da kun yi murna saboda za ni wurin Uba, domin kuwa Uban ya fi ni. 29 t To, yanzu na faɗa muku tun bai faru ba, domin sa'ad da ya faru, ku ba da gaskiya. 30 t Ba zan ƙara yi muku magana mai yawa ba, domin mai mulkin duniyan nan yana zuwa, ba shi kuwa da wani hannu a kaina, 31 t sai dai domin duniya tă sani ina ƙaunar Uban, ina kuma yin yadda Uba ya umarce ni, ku tashi mu tafi daga nan.”

John 14

1 Let not your heart be troubled: believe in God, believe also in me.2 In my Father’s house are many mansions; if it were not so, I would have told you; for I go to prepare a place for you.3 And if I go and prepare a place for you, I come again, and will receive you unto myself; that where I am, there ye may be also.4 And whither I go, ye know the way.5 Thomas saith unto him, Lord, we know not whither thou goest; how know we the way?6 Jesus saith unto him, I am the way, and the truth, and the life: no one cometh unto the Father, but by me.7 If ye had known me, ye would have known my Father also: from henceforth ye know him, and have seen him.8 Philip saith unto him, Lord, show us the Father, and it sufficeth us.9 Jesus saith unto him, Have I been so long time with you, and dost thou not know me, Philip? he that hath seen me hath seen the Father; how sayest thou, Show us the Father?10 Believest thou not that I am in the Father, and the Father in me? the words that I say unto you I speak not from myself: but the Father abiding in me doeth his works.11 Believe me that I am in the Father, and the Father in me: or else believe me for the very works’ sake.12 Verily, verily, I say unto you, he that believeth on me, the works that I do shall he do also; and greater works than these shall he do; because I go unto the Father.13 And whatsoever ye shall ask in my name, that will I do, that the Father may be glorified in the Son.14 If ye shall ask anything in my name, that will I do.15 If ye love me, ye will keep my commandments.16 And I will pray the Father, and he shall give you another Comforter, that he may be with you for ever,17 even the Spirit of truth: whom the world cannot receive; for it beholdeth him not, neither knoweth him: ye know him; for he abideth with you, and shall be in you.18 I will not leave you desolate: I come unto you.19 Yet a little while, and the world beholdeth me no more; but ye behold me: because I live, ye shall live also.20 In that day ye shall know that I am in my Father, and ye in me, and I in you.21 He that hath my commandments, and keepeth them, he it is that loveth me: and he that loveth me shall be loved of my Father, and I will love him, and will manifest myself unto him.22 Judas (not Iscariot) saith unto him, Lord, what is come to pass that thou wilt manifest thyself unto us, and not unto the world?23 Jesus answered and said unto him, If a man love me, he will keep my word: and my Father will love him, and we will come unto him, and make our abode with him.24 He that loveth me not keepeth not my words: and the word which ye hear is not mine, but the Father’s who sent me.25 These things have I spoken unto you, while yet abiding with you.26 But the Comforter, even the Holy Spirit, whom the Father will send in my name, he shall teach you all things, and bring to your remembrance all that I said unto you.27 Peace I leave with you; my peace I give unto you: not as the world giveth, give I unto you. Let not your heart be troubled, neither let it be fearful.28 Ye heard how I said to you, I go away, and I come unto you. If ye loved me, ye would have rejoiced, because I go unto the Father: for the Father is greater than I.29 And now I have told you before it come to pass, that, when it is come to pass, ye may believe.30 I will no more speak much with you, for the prince of the world cometh: and he hath nothing in me;31 but that the world may know that I love the Father, and as the Father gave me commandment, even so I do. Arise, let us go hence.