previous next

YAH 15

Yesu Ne Itacen Inabi na Hakika

1  t “Ni ne itacen inabi na hakika, Ubana kuwa shi ne manomi. 2 Kowane reshe a cikina da ba ya 'ya'ya, sai ya datse shi. Kowane reshe mai yin 'ya'ya kuwa yakan tsarkake shi don ya ƙara haihuwa. 3 t Koyanzu ma ku tsarkakku ne saboda maganar da na faɗa muku. 4 t Ku zauna a cikina, ni kuma a cikinku. Kamar yadda reshen inabi, ba ya iya 'ya'ya shi kaɗai, sai ko ya zauna itacen inabin, haka ku ma ba za ku iya ba, sai kun zauna a cikina. 5 t Ni ne itacen inabin, ku kuwa rassan. Wanda ya zauna a cikina, ni kuma a cikinsa, shi ne mai yin 'ya'ya da yawa. Domin in ba game da ni ba, ba za ku iya kome ba. 6 t Duk wanda bai zauna a cikina ba, za a yar da shi can, kamar reshe, yă bushe, a kuma tattara irinsu a jefa wuta, a ƙone. 7 t In kun zauna a cikina, maganata kuma ta zauna a cikinku, za ku roƙi duk abin da kuke so, za a kuwa yi muku. 8 t Yadda ake ɗaukaka Ubana ke nan, in kuna 'ya'ya da yawa, ta haka kuma kuke tabbata almajiraina. 9 t Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, ku zauna cikin ƙaunar da nake muku. 10 t In kun bi umarnina, za ku zauna cikin ƙaunar da nake muku, kamar yadda ni na bi umarnin Ubana, na kuma zauna cikin ƙaunar da yake mini.

11 t Na gaya muku haka domin farin cikina ya kasance a cikinku, farin cikinku kuma ya zama cikakke.
12  t “Wannan fa shi ne umarnina, cewa ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. 13 t Ba ƙaunar da ta fi haka ga mutane, wato mutum yă ba da ransa saboda aminansa. 14 t Ku aminaina ne in kuna yin abin da na umarce ku. 15 t Nan gaba ba sauran in ce da ku bayi, don bawa bai san abin da ubangijinsa yake yi ba. Sai dai in ce da ku aminai, domin na sanar da ku duk abin da na jiyo wurin Ubana. 16 t Ba ku kuka zaɓe ni ba, ni ne na zaɓe ku, na sa ku ku je ku yi 'ya'ya, 'ya'yanku kuma su tabbata, domin kome kuka roƙi Uba da sunana yă ba ku.

17 t Na umarce ku haka domin ku ƙaunaci juna.”

Ƙiyayyar Duniya


18  t In duniya ta ƙi ku, ku sani sai da ta ƙi ni kafin ta ƙi ku. 19 t Da ku na duniya ne da duniya ta so abinta, amma saboda ku ba na duniya ba ne, na kuma zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku. 20 t Ku tuna da maganar da na yi muku cewa, ‘Bawa ba ya fin ubangijinsa.’ In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun kiyaye maganata, da sai su kiyaye taku ma. 21 t Duk wannan za su yi muku saboda sunana, don ba su san wanda ya aiko ni ba. 22 t Da ba domin na zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu kam, ba su da wani hanzari a kan zunubinsu. 23 Wanda ya ƙi ni ya ƙi Ubana ma. 24 t Da ba domin na yi ayyuka a cikinsu da ba wanda ya taɓa yi sai ni ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun gani, sun kuma ƙi mu, ni da Ubana duka. 25 t An yi wannan kuwa domin a cika maganar da yake a rubuce a cikin Shari'arsu cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’ 26 t Amma sa'ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, wato Ruhu na gaskiya, mai fitowa daga wurin Uba, shi ne zai shaida ni. 27 t Ku ma shaidu ne, domin tun farko kuke tare da ni.

John 15

1 I am the true vine, and my Father is the husbandman.2 Every branch in me that beareth not fruit, he taketh it away: and every branch that beareth fruit, he cleanseth it, that it may bear more fruit.3 Already ye are clean because of the word which I have spoken unto you.4 Abide in me, and I in you. As the branch cannot bear fruit of itself, except it abide in the vine; so neither can ye, except ye abide in me.5 I am the vine, ye are the branches: He that abideth in me, and I in him, the same beareth much fruit: for apart from me ye can do nothing.6 If a man abide not in me, he is cast forth as a branch, and is withered; and they gather them, and cast them into the fire, and they are burned.7 If ye abide in me, and my words abide in you, ask whatsoever ye will, and it shall be done unto you.8 Herein is my Father glorified, that ye bear much fruit; and so shall ye be my disciples.9 Even as the Father hath loved me, I also have loved you: abide ye in my love.10 If ye keep my commandments, ye shall abide in my love; even as I have kept my Father’s commandments, and abide in his love.11 These things have I spoken unto you, that my joy may be in you, and that your joy may be made full.12 This is my commandment, that ye love one another, even as I have loved you.13 Greater love hath no man than this, that a man lay down his life for his friends.14 Ye are my friends, if ye do the things which I command you.15 No longer do I call you servants; for the servant knoweth not what his lord doeth: but I have called you friends; for all things that I heard from my Father, I have made known unto you.16 Ye did not choose me, but I chose you, and appointed you, that ye should go and bear fruit, and that your fruit should abide: that whatsoever ye shall ask of the Father in my name, he may give it you.17 These things I command you, that ye may love one another.18 If the world hateth you, ye know that it hath hated me before it hated you.19 If ye were of the world, the world would love its own: but because ye are not of the world, but I chose you out of the world, therefore the world hateth you.20 Remember the word that I said unto you, A servant is not greater than his lord. If they persecuted me, they will also persecute you; if they kept my word, they will keep yours also.21 But all these things will they do unto you for my name’s sake, because they know not him that sent me.22 If I had not come and spoken unto them, they had not had sin: but now they have no excuse for their sin.23 He that hateth me hateth my Father also.24 If I had not done among them the works which none other did, they had not had sin: but now have they both seen and hated both me and my Father.25 But this cometh to pass, that the word may be fulfilled that is written in their law, They hated me without a cause.26 But when the Comforter is come, whom I will send unto you from the Father, even the Spirit of truth, which proceedeth from the Father, he shall bear witness of me:27 and ye also bear witness, because ye have been with me from the beginning.