YAH 16
1 t “Na faɗa muku duk wannan ne domin in kawar muku da sanadin tuntuɓe. 2 t Za su fisshe ku daga jama'a. Hakika, lokaci ma na zuwa da kowa ya kashe ku, zai zaci bautar Allah yake yi. 3 t Za su yi haka ne kuwa domin ba su san Uba ko ni ba.
4 t Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin in lokacinsu ya yi ku tuna na faɗa muku.”Aikin Ruhu Mai Tsarki
“Ban faɗa muku abubuwan nan tun da farko ba, domin ina tare da ku. 5 t Yanzu kuwa za ni wurin wanda ya aiko ni, duk da haka a cikinku, ba wanda ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’ 6 Amma saboda na faɗa muku waɗannan abubuwa, ga shi baƙin ciki ya cika zuciyarku. 7 t Duk da haka ina gaya muku gaskiya, zai fiye muku in tafi, domin in ban tafi ba, Mai Taimakon nan ba zai zo gare ku ba. In kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku. 8 Sa'ad da kuwa ya zo zai faɗakar da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci. 9 t Wato a kan zunubi, domin ba su gaskata da ni ba, 10 t a kan adalci, don za ni wurin Uba, ba kuwa za ku ƙara ganina ba.
11 t a kan hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulkin duniyar nan hukunci.
12 t “Ina da sauran abubuwa da yawa da zan gaya muku tukuna, amma ba za ku iya ɗaukarsu a yanzu ba. 13 t Sa'ad da kuwa Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku cikin dukan gaskiya, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai faɗa, zai kuma sanar da ku al'amuran da za su auku. 14 Zai ɗaukaka ni, domin zai ɗauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku.
15 t Duk abin da Uba yake da shi, nawa ne. Shi ya sa na ce zai ɗauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku.”Baƙin Ciki Zai Koma Farin Ciki
16 t “Bayan ɗan lokaci kaɗan, ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma, za ku gan ni.” 17 t Sai waɗansu almajiransa suka ce wa juna, “Me yake nufi da ce mana, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’? da kuma cewa, ‘Domin za ni wurin Uba’?” 18 Suka ce, “Me yake nufi da, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ’ ɗin? Ai, ba mu san abin da yake faɗa ba.” 19 Yesu kuwa ya sani suna so su tambaye shi, sai ya ce musu, “Wato kuna tambayar juna ne abin da nake nufi da cewa, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’? 20 t Lalle hakika, ina gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, amma duniya za ta yi farin ciki. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki. 21 t Idan mace tana naƙuda takan sha wuya, don lokacin haihuwarta ya yi. Amma da zarar ta haifi jinjirin, ba ta ƙara tunawa da wahalar da ta sha, domin murnar an sami baƙon duniya. 22 t Haka ku ma yanzu kuke tare da baƙin ciki, amma zan sāke ganinku, sa'an nan zuciyarku za ta yi fari, ba kuwa mai ɗauke muku farin cikinku. 23 t A ran nan, ba za ku yi mini wata tambaya ba. Lalle hakika, ina gaya muku, kome kuka roƙi Uba zai ba ku saboda sunana.
24 t Har yanzu dai ba ku roƙi kome da sunana ba. Ku roƙa, za ku samu, domin farin cikinku ya zama cikakke.”Na Yi Nasara da Duniya
25 t “Duk wannan na faɗa muku da misalai ne. Lokaci yana zuwa da ba zan ƙara faɗa muku kome da misalai ba, sai dai in ba ku labarin Uba a sarari. 26 t A ran nan za ku yi roƙo da sunana. Ban kuwa ce muku zan roƙar muku Uba ba, 27 t domin shi Uban kansa na ƙaunarku, domin kun ƙaunace ni, kun kuma gaskata daga wurin Uban na fito.
28 t Daga wurin Uban ne na fito, na shigo duniya, har wa yau kuma zan bar duniya in koma wurin Uba.”
29 t Sai almajiransa suka ce, “Yauwa! Yanzu ne fa kake magana a sarari, ba da misali ba! 30 Yanzu ne muka tabbata ka san kome, ba sai wani ya tambaye ka ba. Ta haka muka gaskata daga wurin Allah ka fito.” 31 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ashe, yanzu kun gaskata? 32 t To, lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansu, ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka kuwa ba ni kaɗai nake ba, domin Uba na tare da ni. 33 t Na faɗa muku wannan ne domin a gare ni ku sami salama. A duniya kuna shan wuya, amma dai ku yi farin ciki, ai, na yi nasara da duniya.”
John 16
1 These things have I spoken unto you, that ye should not be caused to stumble.2 They shall put you out of the synagogues: yea, the hour cometh, that whosoever killeth you shall think that he offereth service unto God.3 And these things will they do, because they have not known the Father, nor me.4 But these things have I spoken unto you, that when their hour is come, ye may remember them, how that I told you. And these things I said not unto you from the beginning, because I was with you.5 But now I go unto him that sent me; and none of you asketh me, Whither goest thou?6 But because I have spoken these things unto you, sorrow hath filled your heart.7 Nevertheless I tell you the truth: It is expedient for you that I go away; for if I go not away, the Comforter will not come unto you; but if I go, I will send him unto you.8 And he, when he is come, will convict the world in respect of sin, and of righteousness, and of judgment:9 of sin, because they believe not on me;10 of righteousness, because I go to the Father, and ye behold me no more;11 of judgment, because the prince of this world hath been judged.12 I have yet many things to say unto you, but ye cannot bear them now.13 Howbeit when he, the Spirit of truth, is come, he shall guide you into all the truth: for he shall not speak from himself; but what things soever he shall hear, these shall he speak: and he shall declare unto you the things that are to come.14 He shall glorify me: for he shall take of mine, and shall declare it unto you.15 All things whatsoever the Father hath are mine: therefore said I, that he taketh of mine, and shall declare it unto you.16 A little while, and ye behold me no more; and again a little while, and ye shall see me.17 Some of his disciples therefore said one to another, What is this that he saith unto us, A little while, and ye behold me not; and again a little while, and ye shall see me: and, Because I go to the Father?18 They said therefore, What is this that he saith, A little while? We know not what he saith.19 Jesus perceived that they were desirous to ask him, and he said unto them, Do ye inquire among yourselves concerning this, that I said, A little while, and ye behold me not, and again a little while, and ye shall see me?20 Verily, verily, I say unto you, that ye shall weep and lament, but the world shall rejoice: ye shall be sorrowful, but your sorrow shall be turned into joy.21 A woman when she is in travail hath sorrow, because her hour is come: but when she is delivered of the child, she remembereth no more the anguish, for the joy that a man is born into the world.22 And ye therefore now have sorrow: but I will see you again, and your heart shall rejoice, and your joy no one taketh away from you.23 And in that day ye shall ask me no question. Verily, verily, I say unto you, if ye shall ask anything of the Father, he will give it you in my name.24 Hitherto have ye asked nothing in my name: ask, and ye shall receive, that your joy may be made full.25 These things have I spoken unto you in dark sayings: the hour cometh, when I shall no more speak unto you in dark sayings, but shall tell you plainly of the Father.26 In that day ye shall ask in my name: and I say not unto you, that I will pray the Father for you;27 for the Father himself loveth you, because ye have loved me, and have believed that I came forth from the Father.28 I came out from the Father, and am come into the world: again, I leave the world, and go unto the Father.29 His disciples say, Lo, now speakest thou plainly, and speakest no dark saying.30 Now know we that thou knowest all things, and needest not that any man should ask thee: by this we believe that thou camest forth from God.31 Jesus answered them, Do ye now believe?32 Behold, the hour cometh, yea, is come, that ye shall be scattered, every man to his own, and shall leave me alone: and yet I am not alone, because the Father is with me.33 These things have I spoken unto you, that in me ye may have peace. In the world ye have tribulation: but be of good cheer; I have overcome the world.