previous next

YAH 17

Addu'ar Yesu don Almajiransa

1  t Da Yesu ya faɗi haka, sai ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka domin Ɗan ya ɗaukaka ka, 2 t tun da ka ba shi iko a kan dukkan 'yan adam, yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi. 3 t Rai madawwami kuwa, shi ne su san ka, Allah Makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko. 4 t Na ɗaukaka ka a duniya da yake na cika aikin da ka ba ni in yi.

5 t Yanzu kuma, ya Uba, ka ɗaukaka ni zuwa ga zatinka da ɗaukakan nan da nake da ita tare da kai tun kafin duniya ta kasance.
6  t “Na bayyana sunanka ga mutanen da ka ba ni daga cikin duniya. Dā ma naka ne, ka kuwa ba ni su, sun kuma kiyaye maganarka. 7 Yanzu kuwa sun san duk iyakar abin da ka ba ni daga gare ka yake. 8 t Domin kuwa maganar da ka faɗa mini na faɗa musu, sun kuwa karɓa, sun kuma san hakika na fito daga wurinka ne, sun kuma gaskata kai ne ka aiko ni. 9 t Ni, roƙo nake yi dominsu. Ba duniya nake roƙa wa ba, sai dai su waɗanda ka ba ni, domin su naka ne. 10 t Dukkan nawa naka ne, duk naka kuma nawa ne, an kuma ɗaukaka ni a zukatansu. 11 t Yanzu kuma ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai tsarki, ka kiyaye su da ikon sunanka da ka ba ni, su zama ɗaya kamar yadda muke. 12 t Duk sa'ad da nake tare da su, na kiyaye su da ikon sunanka da ka ba ni. Na kāre su, ba kuwa waninsu da ya halaka, sai dai halakakken nan, domin Nassi ya cika. 13 t Amma yanzu ina zuwa wurinka. Ina faɗar wannan magana tun ina duniya, domin farin cikina ya zama cikakke a zukatansu. 14 t Na faɗa musu maganarka, duniya kuwa ta ƙi su, domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. 15 t Ba na roƙonka ka ɗauke su daga duniya, sai dai ka kāre su daga Mugun nan. 16 t Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. 17 t Ka tsarkake su cikin gaskiya. Maganarka ita ce gaskiya. 18 t Kamar yadda ka aiko ni duniya, haka ni ma na aike su duniya.

19 Saboda su ne nake miƙa kaina, domin su ma a tsarkake su cikin gaskiya.
20 “Ba kuwa waɗannan kaɗai nake roƙa wa ba, har ma masu gaskatawa da ni ta maganarsu, 21 t domin dukansu su zama ɗaya, kamar yadda kai, ya Uba, kake cikina, ni kuma nake cikinka, haka su ma su kasance cikinmu, domin duniya ta gaskata, cewa kai ne ka aiko ni. 22 t Ɗaukakar da ka yi mini, ita na yi musu, domin su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya, 23 t ni a cikinsu, kai kuma a cikina, domin su zama ɗaya sosai, duniya ta gane kai ne ka aiko ni, ta kuma gane ka ƙaunace su kamar yadda ka kaunace ni. 24 t Ya Uba, ina so waɗanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda nake, su dubi ɗaukakata da ka yi mini, domin ka ƙaunace ni tun ba a halicci duniya ba. 25 t Ya Uba mai adalci, duniya kam, ba ta san ka ba, amma ni na san ka , waɗannan kuma sun sani kai ne ka aiko ni. 26 t Na sanar da su sunanka, zan kuma sana, domin ƙaunar da ka yi mini tă kasance cikinsu, ni ma in kasance a cikinsu.”

John 17

1 These things spake Jesus; and lifting up his eyes to heaven, he said, Father, the hour is come; glorify thy Son, that the son may glorify thee:2 even as thou gavest him authority over all flesh, that to all whom thou hast given him, he should give eternal life.3 And this is life eternal, that they should know thee the only true God, and him whom thou didst send, even Jesus Christ.4 I glorified thee on the earth, having accomplished the work which thou hast given me to do.5 And now, Father, glorify thou me with thine own self with the glory which I had with thee before the world was.6 I manifested thy name unto the men whom thou gavest me out of the world: thine they were, and thou gavest them to me; and they have kept thy word.7 Now they know that all things whatsoever thou hast given me are from thee:8 for the words which thou gavest me I have given unto them; and they received them, and knew of a truth that I came forth from thee, and they believed that thou didst send me.9 I pray for them: I pray not for the world, but for those whom thou hast given me; for they are thine:10 and all things that are mine are thine, and thine are mine: and I am glorified in them.11 And I am no more in the world, and these are in the world, and I come to thee. Holy Father, keep them in thy name which thou hast given me, that they may be one, even as we are.12 While I was with them, I kept them in thy name which thou hast given me: and I guarded them, and not one of them perished, but the son of perdition; that the scripture might be fulfilled.13 But now I come to thee; and these things I speak in the world, that they may have my joy made full in themselves.14 I have given them thy word; and the world hated them, because they are not of the world, even as I am not of the world.15 I pray not that thou shouldest take them from the world, but that thou shouldest keep them from the evil one.16 They are not of the world even as I am not of the world.17 Sanctify them in the truth: thy word is truth.18 As thou didst send me into the world, even so sent I them into the world.19 And for their sakes I sanctify myself, that they themselves also may be sanctified in truth.20 Neither for these only do I pray, but for them also that believe on me through their word;21 that they may all be one; even as thou, Father, art in me, and I in thee, that they also may be in us: that the world may believe that thou didst send me.22 And the glory which thou hast given me I have given unto them; that they may be one, even as we are one;23 I in them, and thou in me, that they may be perfected into one; that the world may know that thou didst send me, and lovedst them, even as thou lovedst me.24 Father, I desire that they also whom thou hast given me be with me where I am, that they may behold my glory, which thou hast given me: for thou lovedst me before the foundation of the world.25 O righteous Father, the world knew thee not, but I knew thee; and these knew that thou didst send me;26 and I made known unto them thy name, and will make it known; that the love wherewith thou lovedst me may be in them, and I in them.