YAH 2
Biki a Kana ta Galili
1 t A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta ƙasar Galili. Uwar Yesu kuwa tana nan, 2 aka kuma gayyaci Yesu da almajiransa. 3 Da ruwan inabi ya gaza, uwar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.” 4 t Yesu ya ce mata, “Iya, ai, wannan magana ba taki ba ce. Lokacina bai yi ba tukuna.” 5 t Sai uwa tasa ta ce wa barorin, “Duk abin da ya ce ku yi, sai ku yi.” 6 t A wurin kuwa akwai randuna shida na dutse a ajijjiye, bisa ga al'adar Yahudawa ta tsarkakewa, kowacce na cin wajen tulu shida shida. 7 Sai Yesu ya ce musu, “Ku cika randunan nan da ruwa.” Suka ciccika su fal. 8 Sa'an nan ya ce musu, “To, yanzu ku ɗiba, ku kai wa uban bikin.” Sai suka kai. 9 t Da uban bikin ya kurɓi ruwan da yanzu aka mayar ruwan inabi, bai kuwa san inda aka samo shi ba (amma barorin da suka ɗebo ruwan sun sani), ya yi magana da ango,
10 ya ce, “Kowa, ai, kyakkyawan ruwan inabi yakan fara bayarwa, bayan mutane sun shassha, sa'an nan kuma ya kawo wanda ya gaza na farin kyau. Amma kai ka ɓoye kyakkyawan ruwan inabin sai yanzu!”
11 t Wannan ce mu'ujizar farko da Yesu ya yi, ya kuwa yi ta ne a Kana ta ƙasar Galili, ya bayyana ɗaukakarsa. Almajiransa kuma suka gaskata da shi.
12 t Bayan haka sai ya tafi Kafarnahum, da shi da uwa tasa, da 'yan'uwansa, da kuma almajiransa, suka zauna a can 'yan kwanaki.Yesu Ya Tsabtace Haikali
(Mat 21.12-13; Mar 11.15-17; Luka 19.45-46)
13 t Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya matso, sai Yesu ya tafi Urushalima. 14 A cikin Haikali ya sami waɗansu dillalan shanu, da na tumaki, da na tattabarai, da kuma 'yan canjin kuɗi zaune wurin aikinsu. 15 Sai ya tuka bulala mai harsuna ta igiya, ya kore su duka daga Haikalin, har da tumakin da shanun, ya kuma watsar da kuɗin 'yan canjin, ya birkice teburorinsu. 16 t Ya ce da dillalan tattabarai, “Ku kwashe waɗannan daga nan, kada ku mai da Haikalin Ubana kasuwa.” 17 t Sai almajiransa suka tuna a rubuce yake cewa, “Kishin Haikalinka ya ci raina matuƙa.” 18 t Sai Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Wace mu'ujiza za ka nuna mana da kake haka?” 19 t Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe Haikalin nan, ni kuwa in ta da shi a cikin kwana uku.” 20 Yahudawa suka ce, “Sai fa da aka shekara arba'in da shida ana ginin Haikalin nan, kai kuwa a cikin kwana uku za ka ta da shi?” 21 t Amma haikalin da Yesu ya ambata jikinsa ne.
22 t Saboda haka bayan an tashe shi daga matattu, almajiransa suka tuna ya faɗi haka, suka kuma gaskata Nassi da maganar da Yesu ya faɗa.Yesu Ya San Zuciyar Kowa
23 t To, sa'ad da yake Urushalima lokacin Idin Ƙetarewa, mutane da yawa suka gaskata da sunansa, saboda ganin mu'ujizan da ya yi. 24 Amma Yesu bai amince da su ba, 25 t domin ya san zuciyar kowa, ba kuma sai wani ya shaidi mutum a wurinsa ba, domin shi kansa ya san abin da yake zuciyar ɗan adam.
John 2
1 And the third day there was a marriage in Cana of Galilee; and the mother of Jesus was there:2 and Jesus also was bidden, and his disciples, to the marriage.3 And when the wine failed, the mother of Jesus saith unto him, They have no wine.4 And Jesus saith unto her, Woman, what have I to do with thee? mine hour is not yet come.5 His mother saith unto the servants, Whatsoever he saith unto you, do it.6 Now there were six waterpots of stone set there after the Jews’ manner of purifying, containing two or three firkins apiece.7 Jesus saith unto them, Fill the waterpots with water. And they filled them up to the brim.8 And he saith unto them, Draw out now, and bear unto the ruler of the feast. And they bare it.9 And when the ruler of the feast tasted the water now become wine, and knew not whence it was (but the servants that had drawn the water knew), the ruler of the feast calleth the bridegroom,10 and saith unto him, Every man setteth on first the good wine; and when men have drunk freely, then that which is worse: thou hast kept the good wine until now.11 This beginning of his signs did Jesus in Cana of Galilee, and manifested his glory; and his disciples believed on him.12 After this he went down to Capernaum, he, and his mother, and his brethren, and his disciples; and there they abode not many days.13 And the passover of the Jews was at hand, and Jesus went up to Jerusalem.14 And he found in the temple those that sold oxen and sheep and doves, and the changers of money sitting:15 and he made a scourge of cords, and cast all out of the temple, both the sheep and the oxen; and he poured out the changers’ money, and overthrew their tables;16 and to them that sold the doves he said, Take these things hence; make not my Father’s house a house of merchandise.17 His disciples remembered that it was written, Zeal for thy house shall eat me up.18 The Jews therefore answered and said unto him, What sign showest thou unto us, seeing that thou doest these things?19 Jesus answered and said unto them, Destroy this temple, and in three days I will raise it up.20 The Jews therefore said, Forty and six years was this temple in building, and wilt thou raise it up in three days?21 But he spake of the temple of his body.22 When therefore he was raised from the dead, his disciples remembered that he spake this; and they believed the scripture, and the word which Jesus had said.23 Now when he was in Jerusalem at the passover, during the feast, many believed on his name, beholding his signs which he did.24 But Jesus did not trust himself unto them, for that he knew all men,25 and because he needed not that any one should bear witness concerning man; for he himself knew what was in man.