YAH 3
Yesu da Nikodimu
1 t To, akwai wani Bafarisiye, sunansa Nikodimu, wani shugaban Yahudawa. 2 t Wannan mutum ya zo wurin Yesu da dad dare, ya ce masa, “Ya Shugaba, mun sani kai malami ne da ka zo daga wurin Allah, domin ba mai iya yin waɗannan mu'ujizan da kake yi, sai ko Allah yana tare da shi.” 3 t Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba a sāke haifar mutum ba, ba zai iya ganin Mulkin Allah ba.” 4 Nikodimu ya ce masa, “Ƙaƙa za a haifi mutum bayan ya tsufa? Wato, ya iya komawa a cikin uwa tasa ta sāke haifo shi?” 5 t Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba an haifi mutum ta ruwa da kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga Mulkin Allah ba. 6 t Abin da mutum ya haifa mutum ne, abin kuma da Ruhu ya haifa ruhu ne. 7 Kada ka yi mamaki domin na ce maka, ‘Dole a sāke haifarku.’ 8 Iska tana busawa inda ta ga dama. Kakan ji motsinta, amma ba ka san inda ta fito da inda za ta. Haka fa yake ga duk wanda Ruhu ya haifa.” 9 t Sai Nikodimu ya amsa masa ya ce, “Ƙaƙa wannan zai yiwu?” 10 t Yesu ya amsa masa ya ce, “Ashe, kai ma da kake malamin Isra'ila, ba ka fahimci waɗannan al'amura ba? 11 t Lalle hakika, ina gaya maka, abin da muka sani shi muke faɗa, muna kuma shaidar da abin da muka gani, amma kun ƙi yarda da shaidarmu. 12 In na yi muku zancen al'amuran duniya ba ku gaskata ba, yaya za ku gaskata in na yi muku zancen al'amuran sama? 13 t Ba wanda ya taɓa hawa cikin Sama sai shi wanda ya sauko daga Sama, wato, Ɗan Mutum da yake Sama. 14 t Kamar yadda Musa ya ɗaga macijin nan a jeji, haka kuma dole ne a ɗaga Ɗan Mutum,
15 t domin duk wanda ya gaskata da shi, ya sami rai madawwami.
16 t “Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami. 17 t Gama Allah bai aiko Ɗansa duniya domin yă yanke mata hukunci ba, sai dai domin duniya ta sami ceto ta wurinsa. 18 t Duk wanda ya gaskata da shi, ba za a yi masa hukunci ba. Wanda kuwa bai ba da gaskiya ba, an riga an yi masa hukunci, domin bai gaskata da sunan makaɗaicin Ɗan Allah ba. 19 t Hukuncin kuwa shi ne, haske ya shigo duniya, amma mutane suka fi ƙaunar duhu da hasken, don ayyukansu mugaye ne. 20 t Duk mai yin rashin gaskiya yakan ƙi hasken, ba ya kuma zuwa wajen hasken, don kada ayyukansa su tonu.
21 Mai aikata gaskiya kuwa yakan zo wajen hasken, domin a bayyana ayyukansa, cewa, da taimakon Allah ne aka yi su.”Shi Lalle Ya Riƙa Ƙaruwa, Ni kuwa Raguwa
22 t Bayan haka, Yesu da almajiransa suka tafi ƙasar Yahudiya. A nan ya jima da su, yana yin baftisma. 23 Yahaya kuma yana yin baftisma a Ainon kusa da Salima, domin da ruwa da yawa a can. Mutane kuwa suka yi ta zuwa ana yi musu baftisma.
24 t Domin a sa'an nan ba a sa Yahaya a kurkuku ba tukuna.
25 t Sai fa almajiran Yahaya suka tasar wa wani Bayahude da muhawara a kan maganar tsarkakewa. 26 t Suka kuma zo wurin Yahaya, suka ce masa, “Ya shugaba, wanda dā kuke tare a hayin Kogin Urdun, wanda kai kanka ma ka shaida shi, to, ga shi, yana yin baftisma, har kowa da kowa yana zuwa wurinsa.” 27 Sai Yahaya ya amsa ya ce, “Ba mai iya samun kome sai ko an ba shi daga Sama. 28 t Ku kanku ma shaiduna ne a kan na ce ba ni ne Almasihu ba, amma an aiko ni ne ni riga shi gaba. 29 t Mai amarya shi ne ango. Abokin ango kuwa da yake tsaye, yake kuma sauraron magana tasa, yakan yi farin ciki ƙwarai da jin muryar angon. Saboda haka farin cikin nan nawa ya cika.
30 Shi kam, lalle ne ya riƙa ƙaruwa, ni kuwa in riƙa raguwa.Wanda Ya Zo daga Sama
31 t “Mai zuwa daga Sama yana Sama da kowa. Wanda yake na ƙasa asalinsa kuwa na ƙasa ne, maganar ƙasa kuma yake yi. Mai zuwan nan daga Sama yana Sama da kowa. 32 t Abin da ya ji, ya kuma gani, shi yake shaidarwa, duk da haka ba wanda yake yarda da shaidarsa. 33 Duk wanda ya yarda da shaidarsa, ya haƙƙaƙe, cewa, Allah mai gaskiya ne. 34 t Domin wanda Allah ya aiko, zantuttukan Allah yake faɗa, gama Allah yana ba da Ruhu ba da iyakancewa ba. 35 t Uban yana ƙaunar Ɗan, ya kuma sa kome a hannunsa. 36 t Wanda ya gaskata da Ɗan, yana da rai madawwami. Wanda ya ƙi bin Ɗan kuwa, ba zai sami rai ba, sai dai fushin Allah ya tabbata a gare shi.”
John 3
1 Now there was a man of the Pharisees, named Nicodemus, a ruler of the Jews:2 the same came unto him by night, and said to him, Rabbi, we know that thou art a teacher come from God; for no one can do these signs that thou doest, except God be with him.3 Jesus answered and said unto him, Verily, verily, I say unto thee, Except one be born anew, he cannot see the kingdom of God.4 Nicodemus saith unto him, How can a man be born when he is old? can he enter a second time into his mother’s womb, and be born?5 Jesus answered, Verily, verily, I say unto thee, Except one be born of water and the Spirit, he cannot enter into the kingdom of God!6 That which is born of the flesh is flesh; and that which is born of the Spirit is spirit.7 Marvel not that I said unto thee, Ye must be born anew.8 The wind bloweth where it will, and thou hearest the voice thereof, but knowest not whence it cometh, and whither it goeth: so is every one that is born of the Spirit.9 Nicodemus answered and said unto him, How can these things be?10 Jesus answered and said unto him, Art thou the teacher of Israel, and understandest not these things?11 Verily, verily, I say unto thee, We speak that which we know, and bear witness of that which we have seen; and ye receive not our witness.12 If I told you earthly things and ye believe not, how shall ye believe if I tell you heavenly things?13 And no one hath ascended into heaven, but he that descended out of heaven, even the Son of man, who is in heaven.14 And as Moses lifted up the serpent in the wilderness, even so must the Son of man be lifted up;15 that whosoever believeth may in him have eternal life.16 For God so loved the world, that he gave his only begotten Son, that whosoever believeth on him should not perish, but have eternal life.17 For God sent not the Son into the world to judge the world; but that the world should be saved through him.18 He that believeth on him is not judged: he that believeth not hath been judged already, because he hath not believed on the name of the only begotten Son of God.19 And this is the judgment, that the light is come into the world, and men loved the darkness rather than the light; for their works were evil.20 For every one that doeth evil hateth the light, and cometh not to the light, lest his works should be reproved.21 But he that doeth the truth cometh to the light, that his works may be made manifest, that they have been wrought in God.22 After these things came Jesus and his disciples into the land of Judea; and there he tarried with them, and baptized.23 And John also was baptizing in Enon near to Salim, because there was much water there: and they came, and were baptized.24 For John was not yet cast into prison.25 There arose therefore a questioning on the part of John’s disciples with a Jew about purifying.26 And they came unto John, and said to him, Rabbi, he that was with thee beyond the Jordan, to whom thou hast borne witness, behold, the same baptizeth, and all men come to him.27 John answered and said, A man can receive nothing, except it have been given him from heaven.28 Ye yourselves bear me witness, that I said, I am not the Christ, but, that I am sent before him.29 He that hath the bride is the bridegroom: but the friend of the bridegroom, that standeth and heareth him, rejoiceth greatly because of the bridegroom’s voice: this my joy therefore is made full.30 He must increase, but I must decrease.31 He that cometh from above is above all: he that is of the earth is of the earth, and of the earth he speaketh: he that cometh from heaven is above all.32 What he hath seen and heard, of that he beareth witness; and no man receiveth his witness.33 He that hath received his witness hath set his seal to this, that God is true.34 For he whom God hath sent speaketh the words of God: for he giveth not the Spirit by measure.35 The Father loveth the Son, and hath given all things into his hand.36 He that believeth on the Son hath eternal life; but he that obeyeth not the Son shall not see life, but the wrath of God abideth on him.