previous next

YAH 4

Yesu da Wata Basamariya

1  t To, da Ubangiji Yesu ya sani dai Farisiyawa sun ji labari yana samun almajirai, yana kuma yi musu baftisma fiye da Yahaya 2 (ko da yake dai ba Yesu kansa yake yin baftisma ba, almajiransa ne), 3 t sai ya bar ƙasar Yahudiya, ya koma ƙasar Galili. 4 Lalle ne kuwa yă ratsa ƙasar Samariya. 5 t Sai ya zo wani gari na ƙasar Samariya, wanda ake kira Saikar, kusa da yankin ƙasar da Yakubu ya ba ɗansa Yusufu.

6 Rijiyar Yakubu kuwa a nan take. Saboda gajiyar tafiya fa, sai Yesu ya zauna haka nan a bakin rijiyar. Wajen tsakar rana ce kuwa.
7 Sai ga wata Basamariya ta zo ɗiban ruwa. Yesu ya ce mata, “Sa mini ruwa in sha.” 8 t Almajiransa kuwa sun shiga gari sayen abinci. 9 t Sai Basamariyar ta ce masa, “Ƙaƙa kai Bayahude za ka roƙe ni ruwan sha, ni da nake Basamariya?” (Don Yahudawa ba sa cuɗanya da Samariyawa). 10 t Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda ya ce miki, ‘Sa mini ruwa in sha,’ ai, da kin roƙe shi, shi kuwa zai ba ki ruwan rai.” 11 Sai matar ta ce masa, “Ya Shugaba, ai, ba ka da guga, rijiyar kuwa da zurfi. To, ina ka sami ruwan nan na rai? 12 t Ashe, ka fi ubanmu Yakubu ne, wanda ya bar mana rijiyar, har shi da kansa, da 'yayansa, da dabbobinsa, suka sha ruwanta?” 13 Yesu ya amsa mata ya ce, “Duk mai shan ruwan nan zai sāke jin ƙishirwa. 14 t Amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada. Ruwan da zan ba shi kuwa zai zama maɓuɓɓuga a gare shi, yana ɓuɓɓugowa har ya zuwa rai madawwami.”

15 t Matar ta ce masa, “Ya Shugaba, ka ba ni ruwan nan, don kada in ƙara jin ƙishirwa, kada kuma in riƙa zuwa har nan in ɗiba.”
16 Sai Yesu ya ce mata, “Je ki, ku zo da mijinki.” 17 Sai matar ta amsa ta ce, “Ai, ba ni da miji.” Yesu ya ce mata, “Gaskiyarki da kika ce ba ki da miji, 18 don kin auri maza biyar, wanda kuke tare yanzu kuwa ba mijinki ba ne. A nan kam kin yi gaskiya.” 19 t Matar ta ce masa, “Ya Shugaba, na dai gane kai annabi ne. 20 t Kakanninmu sun yi sujada a dutsen nan. Ku kuwa kun ce a Urushalima ne wurin da ya wajaba a yi sujada yake.” 21 t Sai Yesu ya ce mata, “Uwargida, ki gaskata ni, lokaci na zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ba, ko a kan dutsen nan, ko a Urushalima, 22 t Ku kuna yi wa abin da ba ku sani ba sujada, mu kuwa muna yi wa abin da muka sani sujada, domin ceto ta hanyar Yahudawa yake. 23 t Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a ruhu, da gaskiya kuma. Lalle kuwa irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema. 24 t Allah Ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa lalle su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.” 25 t Sai matar ta ce masa, “Na san Masihi yana zuwa, wanda ake kira Almasihu. Sa'ad da ya zo kuwa, zai sanar da mu kome.”

26 t Yesu ya ce mata, “Ni ne, ni mai maganan nan da yake.”
27  t Nan take almajiransa suka dawo. Suka yi mamakin ganin yana magana da mace. Amma kuwa ba wanda ya ce, “Me kike bukata?” ko, “Don me kake magana da ita?” 28 Sai matar ta bar tulunta, ta koma gari, ta ce wa mutane, 29 t “Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi! Shin, ko wannan shi ne Almasihu?”

30 Sai suka fito daga garin suka nufo shi.
31  t Ana cikin haka sai almajiran suka roƙe shi suka ce, “Ya shugaba, ci abinci.” 32 Amma ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku sani ba.” 33 Almajiran suka ce wa juna, “Shin, wani ya kawo masa abinci ne?” 34 t Sai Yesu ya ce musu, “Abincina shi ne in aikata nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa. 35 t Ba kuna cewa, kaka saura wata huɗu ba? Ina gaya muku fa, ku duba gonaki, ku gani, sun nuna sun isa girbi. 36 t Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare. 37 t A nan kam, wannan karin maganar gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani da girbi.’

38 Na aike ku girbin abin da ba ku yi wahalarsa ba. Waɗansu sun yi wahala, ku kuwa kun mori wahalarsu.”
39  t Samariyawa da yawa na wannan gari suka gaskata da shi saboda maganar matan nan da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.” 40 Da Samariyawa suka iso wurinsa, suka roƙe shi ya sauka a wurinsu. Ya kuwa kwana biyu a nan. 41 Waɗansu kumma da yawa fiye da na dā suka ba da gaskiya saboda magana tasa.

42 t Sa'an nan suka ce wa macen, “Yanzu kam, mun ba da gaskiya, ba don abin da kika faɗa kawai ba, domin mu ma mun ji da kanmu, mun kuma tabbata lalle wannan shi ne Mai Ceton duniya.”

Yesu Ya Warkar da Ɗan Bafada


43  t Bayan kwana biyun nan sai ya tashi daga nan ya tafi ƙasar Galili. 44 t Domin Yesu kansa ya yi shaida cewa annabi ba shi da girma a ƙasarsu.

45 t Da ya isa ƙasar Galili, sai Galilawa suka yi na'am da shi, domin sun ga duk abin da ya yi a Urushalima a lokacin idi, domin su ma sun je idin.
46  t Sai ya sāke zuwa Kana ta ƙasar Galili, inda ya mai da ruwa ruwan inabi. A Kafarnahum kuwa akwai wani bafada wanda ɗansa ba shi da lafiya. 47 t Da jin cewa Yesu ya fito ƙasar Yahudiya ya komo ƙasar Galili, sai ya tafi wurinsa, ya roƙe shi ya je ya warkar da ɗansa, don yana bakin mutuwa. 48 t Yesu ya ce masa, “In ba mu'ujizai da abubuwan al'ajabi kuka gani ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.” 49 Sai bafadan nan ya ce masa, “Ya Shugaba, ka zo tun ƙaramin ɗana bai mutu ba.” 50 Yesu ya ce masa, “Yi tafiyarka, ɗanka a raye yake.” Mutumin kuwa ya gaskata maganar da Yesu ya faɗa masa, ya yi tafiyarsa. 51 Yana cikin tafiya sai ga barorinsa sun taryo shi, suka ce masa, “Ɗanka a raya yake.” 52 Sai ya tambaye su ainihin lokacin da ya fara samun sauƙi. Suka ce masa, “Jiya da ƙarfe ɗaya na rana zazzaɓin ya sake shi.” 53 t Sai uban ya gane, daidai lokacin nan ne, Yesu ya ce masa, “Ɗanka a raye yake.” Shi da kansa kuwa ya ba da gaskiya, da jama'ar gidansa duka. 54 t Wannan kuwa ita ce mu'ujiza ta biyu da Yesu ya yi, bayan Komowarsa ƙasar Galili daga ƙasar Yahudiya.

John 4

1 When therefore the Lord knew that the Pharisees had heard that Jesus was making and baptizing more disciples than John2 (although Jesus himself baptized not, but his disciples),3 he left Judea, and departed again into Galilee.4 And he must needs pass through Samaria.5 So he cometh to a city of Samaria, called Sychar, near to the parcel of ground that Jacob gave to his son Joseph:6 and Jacob’s well was there. Jesus therefore, being wearied with his journey, sat thus by the well. It was about the sixth hour.7 There cometh a woman of Samaria to draw water: Jesus saith unto her, Give me to drink.8 For his disciples were gone away into the city to buy food.9 The Samaritan woman therefore saith unto him, How is it that thou, being a Jew, askest drink of me, who am a Samaritan woman? (For Jews have no dealings with Samaritans.)10 Jesus answered and said unto unto her, If thou knewest the gift of God, and who it is that saith to thee, Give me to drink; thou wouldest have asked of him, and he would have given thee living water.11 The woman saith unto him, Sir, thou hast nothing to draw with, and the well is deep: whence then hast thou that living water?12 Art thou greater than our father Jacob, who gave us the well, and drank thereof himself, and his sons, and his cattle?13 Jesus answered and said unto her, Every one that drinketh of this water shall thirst again:14 but whosoever drinketh of the water that I shall give him shall never thirst; but the water that I shall give him shall become in him a well of water springing up unto eternal life.15 The woman saith unto him, Sir, give me this water, that I thirst not, neither come all the way hither to draw.16 Jesus saith unto her, Go, call thy husband, and come hither.17 The woman answered and said unto him, I have no husband. Jesus saith unto her, Thou saidst well, I have no husband:18 for thou hast had five husbands; and he whom thou now hast is not thy husband: this hast thou said truly.19 The woman saith unto him, Sir, I perceive that thou art a prophet.20 Our fathers worshipped in this mountain; and ye say, that in Jerusalem is the place where men ought to worship.21 Jesus saith unto her, Woman, believe me, the hour cometh, when neither in this mountain, nor in Jerusalem, shall ye worship the Father.22 Ye worship that which ye know not: we worship that which we know; for salvation is from the Jews.23 But the hour cometh, and now is, when the true worshippers shall worship the Father in spirit and truth: for such doth the Father seek to be his worshippers.24 God is a Spirit: and they that worship him must worship in spirit and truth.25 The woman saith unto him, I know that Messiah cometh (he that is called Christ): when he is come, he will declare unto us all things.26 Jesus saith unto her, I that speak unto thee am he.27 And upon this came his disciples; and they marvelled that he was speaking with a woman; yet no man said, What seekest thou? or, Why speakest thou with her?28 So the woman left her waterpot, and went away into the city, and saith to the people,29 Come, see a man, who told me all things that ever I did: can this be the Christ?30 They went out of the city, and were coming to him.31 In the mean while the disciples prayed him, saying, Rabbi, eat.32 But he said unto them, I have meat to eat that ye know not.33 The disciples therefore said one to another, Hath any man brought him aught to eat?34 Jesus saith unto them, My meat is to do the will of him that sent me, and to accomplish his work.35 Say not ye, There are yet four months, and then cometh the harvest? behold, I say unto you, Lift up your eyes, and look on the fields, that they are white already unto harvest.36 He that reapeth receiveth wages, and gathereth fruit unto life eternal; that he that soweth and he that reapeth may rejoice together.37 For herein is the saying true, One soweth, and another reapeth.38 I sent you to reap that whereon ye have not labored: others have labored, and ye are entered into their labor.39 And from that city many of the Samaritans believed on him because of the word of the woman, who testified, He told me all things that ever I did.40 So when the Samaritans came unto him, they besought him to abide with them: and he abode there two days.41 And many more believed because of his word;42 and they said to the woman, Now we believe, not because of thy speaking: for we have heard for ourselves, and know that this is indeed the Saviour of the world.43 And after the two days he went forth from thence into Galilee.44 For Jesus himself testified, that a prophet hath no honor in his own country.45 So when he came into Galilee, the Galilaeans received him, having seen all the things that he did in Jerusalem at the feast: for they also went unto the feast.46 He came therefore again unto Cana of Galilee, where he made the water wine. And there was a certain nobleman, whose son was sick at Capernaum.47 When he heard that Jesus was come out of Judaea into Galilee, he went unto him, and besought him that he would come down, and heal his son; for he was at the point of death.48 Jesus therefore said unto him, Except ye see signs and wonders, ye will in no wise believe.49 The nobleman saith unto him, Sir, come down ere my child die.50 Jesus saith unto him, Go thy way; thy son liveth. The man believed the word that Jesus spake unto him, and he went his way.51 And as he was now going down, his servants met him, saying, that his son lived.52 So he inquired of them the hour when he began to amend. They said therefore unto him, Yesterday at the seventh hour the fever left him.53 So the father knew that it was at that hour in which Jesus said unto him, Thy son liveth: and himself believed, and his whole house.54 This is again the second sign that Jesus did, having come out of Judaea into Galilee.