previous next

YAH 6

Ciyar da Mutum Dubu Biyar

(Mat 14.13-21; Mar 6.30-44; Luka 9.10-17)

1 Bayan haka Yesu ya haye Tekun Galili, wato Tekun Tibariya. 2 t Sai taro mai yawa suka bi shi, don sun ga mu'ujizan da yake yi ga marasa lafiya. 3 t Sai Yesu ya hau dutse ya zauna a can tare da almajiransa. 4 t To, Idin Ƙetarewa, wato idin Yahudawa, ya gabato. 5 t Da Yesu ya ɗaga kai ya hango babban taro yana doso shi, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayo gurasar da mutanen nan za su ci?” 6 Ya faɗi haka ne fa domin ya gwada shi, saboda shi kansa ya san abin da zai yi. 7 Filibus ya amsa ya ce, “Ai, ko gurasar dinari metan ma ba ta isa ko wannensu ya sami kaɗan ba.” 8 t Sai Andarawas ɗan'uwan Bitrus ɗaya daga cikin almajiransa, ya ce masa, 9 t “Ga wani ɗan yaro nan da gurasa biyar na sha'ir, da kuma kifi biyu. Amma me waɗannan za su yi wa mutane masu yawa haka?” 10 Yesu ya ce, “Ku ce wa mutane su zauna.” Wuri ne kuwa mai ciyawa. Sai mazaje suka zazzaune, su wajen dubu biyar. 11 t Yesu ya ɗauki gurasar, bayan ya yi godiya ga Allah kuma, sai ya rarraba wa waɗanda suke zazzaune. Haka kuma ya yi da kifin, gwargwadon abin da ya ishe su. 12 Da suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, “Ku tattara gutsattsarin da suka saura, kada kome ya ɓata.” 13 Sai suka tattara gutsattsarin gurasar nan biyar na sha'ir da suka saura bayan kowa ya ci, suka cika kwando goma sha biyu.

14 t Da jama'a suka ga mu'ujizar da ya yi, suka ce, “Lalle, wannan shi ne annabin nan mai zuwa duniya.!”

15  t Da Yesu ya gane suna shirin zuwa su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan dutsen shi kaɗai.

Yesu na Tafiya a kan Ruwan Teku

(Mat 14.22-27; Mar 6.45-52)


16  t Da magariba ta yi, sai almajiransa suka gangara teku. 17 Suka shiga jirgi suka tasar wa haye tekun zuwa Kafarnahun. A sa'an nan duhu ya yi, Yesu kuwa bai zo wurinsu ba tukuna. 18 Sai tekun ta fara hauka saboda wata riƙaƙƙiyar iska da take busowa. 19 Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko huɗu, sai suka hango Yesu yana tafiya a kan ruwan, ya kusato jirgin. Sai suka firgita. 20 t Amma ya ce musu, “Ni ne, kada ku ji tsoro.”

21 Sa'an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin. Nan da nan sai ga jirgin a gāɓar da za su.

Taro sun Nemi Yesu


22  t Kashegari sauran taron da suka tsaya a hayin tekun suka lura ba wani jirgi a wurin, sai wani ɗan ƙarami, suka kuma lura Yesu bai shiga cikinsa tare da almajiransa ba, sai almajiran ne kaɗai suka tafi. 23 t Akwai kuwa waɗansu ƙananan jirage daga Tibariya da suka iso kusa da wurin nan da taron suka ci gurasa bayan Ubangiji ya yi godiya.

24 Sa'ad da kuwa taron suka ga ba Yesu, ba almajiransa a nan, su ma suka shiga ƙananan jiragen, suka tafi Kafarnahum neman Yesu.

Yesu Gurasar Rai


25  t Da suka same shi a hayin tekun, suka ce masa, “Ya Shugaba, yaushe ka zo nan?” 26 t Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga mu'ujizai ba, sai don kun ci gurasar nan kun ƙoshi. 27 t Kada ku yi wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama har ya zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. Domin shi ne wanda Uba, wato Allah, ya tabbatar wa da ikon yin haka.” 28 Sai suka ce masa, “Me za mu yi mu aikata ayyukan da Allah yake so?” 29 t Yesu ya amsa musu ya ce, “Wannan shi ne aikin da Allah yake so, wato ku gaskata da wanda ya aiko.” 30 t Sai suka ce masa, “To, wace mu'ujiza za ka yi mu gani mu gaskata ka? Me za ka yi? 31 t Kakannin kakanninmu sun ci manna a jeji, yadda yake a rubuce cewa, ‘Ya ba su gurasa daga Sama su ci.’ ” 32 Sa'an nan Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ba Musa ne ya ba ku gurasar nan daga Sama ba, Ubana ne yake ba ku hakikanin Gurasa daga Sama. 33 t Ai, Gurasan Allah shi ne mai saukowa daga Sama, mai ba duniya rai.”

34 t Sai suka ce masa, “Ya Ubangiji, ka riƙa ba mu irin wannan gurasa kullum!”
35  t Yesu ya ce musu, “Ni ne gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo gare ni ba zai ji yunwa ba har abada, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada. 36 Na dai gaya muku, kun gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba. 37 t Duk wanda Uba ya ba ni zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kaɗan. 38 t Domin na sauko daga Sama, ba domin in bi nufin kaina ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni. 39 t Nufin wanda ya aiko ni kuwa, shi ne kada in yar da kowa daga cikin dukkan waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a ranar ƙarshe.

40 t Gama nufin Ubana, shi ne duk wanda yake duban Ɗan, yake kuma gaskatawa da shi, yă sami rai madawwani, ni kuma zan tashe shi a ranar ƙarshe.”
41 Sai fa Yahudawa suka yi masa gunaguni, domin ya ce, “Ni ne Gurasan da ya sauko daga Sama.” 42 t Suka ce, “Ashe, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusufu, wanda uwa tasa da ubansa duk mun san su? To, yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko ne daga sama’?” 43 Yesu ya amsa musu ya ce, “Kada ku yi gunaguni a junanku. 44 t Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uba wanda ya aiko ni ne ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe. 45 t A rubuce yake cikin littattafan annabawa cewa, ‘Dukkansu Allah ne zai koya musu.’ To, duk wanda ya ji, ya kuma koya wurin Uba, zai zo gare ni. 46 t Ba wai don wani ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda yake daga wurin Allah, shi ne ya ga Uban. 47 Lalle hakika ina gaya muku, wanda ya ba da gaskiya, yana da rai madawwami. 48 t Ni ne Gurasa mai ba da rai. 49 t Kakannin kakanninku sun ci manna a jeji, amma kuwa sun mutu. 50 t Ga Gurasa mai saukowa daga Sama, domin kowa yă ci, kada ya mutu.

51 t Ni ne Gurasan rai da ya sauko daga Sama. Kowa ya ci Gurasan nan, zai rayu har abada. Har ma gurasar da zan bayar naman jikina ne, domin duniya ta rayu.”
52  t Sai Yahudawa suka ta da husuma a junansu, suna cewa, “Yaya mutumin nan zai iya ba mu naman jikinsa mu ci?” 53 t Sai Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, in ba ku ci naman jikin Ɗan Mutum ba, kuka kuma sha jininsa, ba rai a gare ku. 54 t Duk wanda suke cin naman jikina, yake kuma shan jinina, yana da rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe. 55 Domin naman jikina abinci ne na hakika, jinina kuma abin sha ne na hakika. 56 t Duk wanda suke cin naman jikina, yake shan jinina, a cikina yake zaune, ni kuma a cikinsa. 57 t Kamar yadda rayayyen Uba ya aiko ni, nake kuma rayuwa saboda Uban, haka ma wanda yake ni ne abincinsa zai rayu saboda ni. 58 t Wannan shi ne Gurasan da ya sauko daga Sama, ba irin wadda kakannin kakanninku suka ci ba, duk da haka suka mutu. Duk mai cin Gurasan nan zai rayu har abada.”

59 Wannan kuwa a majami'a ya faɗa, sa'ad da yake koyarwa a Kafarnahum.

Kalmomin Rai


60  t Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan magana mai wuya ce, wa zai iya jinta?” 61 t Yesu kuwa, da yake ya sani a ransa almajiransa suna gunagunin wannan, sai ya ce musu, “Wato, wannan ne ya zamar muku abin tuntuɓe? 62 t Yaya ke nan in kuka ga Ɗan Mutum yana hawa inda yake dā? 63 t Ai, Ruhu shi ne mai rayarwa, jiki kam ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku ruhu ne, da kuma rai. 64 t Amma fa akwai waɗansunku da ba su ba da gaskiya ba.” Domin tun farko Yesu ya san waɗanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bāshe shi.

65 t Sai ya ƙara da cewa, “Shi ya sa na gaya muku, ba mai iya zuwa gare ni, sai ko Uba ya yardar masa.”
66  t Kan wannan da yawa daga cikin almajiransa suka koma da baya, ba su ƙara tafiya tare da shi ba. 67 t Sai Yesu ya ce wa goma sha biyun, “Ku ma kuna so ku tafi ne?” 68 t Bitrus ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangiji, gun wa za mu je? Kai kake da maganar rai madawwami. 69 t Mu kuwa mun gaskata, mun kuma tabbata kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.” 70 t Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba ni na zaɓe ku, ku goma sha biyu ba? To, ɗayanku Iblis ne.” 71 Wato, yana nufin Yahuza, ɗan Saminu Iskariyoti, don shi ne zai bāshe shi, ko da yake ɗaya daga cikin goma sha biyun nan ne.

John 6

1 After these things Jesus went away to the other side of the sea of Galilee, which is the sea of Tiberias.2 And a great multitude followed him, because they beheld the signs which he did on them that were sick.3 And Jesus went up into the mountain, and there he sat with his disciples.4 Now the passover, the feast of the Jews, was at hand.5 Jesus therefore lifting up his eyes, and seeing that a great multitude cometh unto him, saith unto Philip, Whence are we to buy bread, that these may eat?6 And this he said to prove him: for he himself knew what he would do.7 Philip answered him, Two hundred shillings’ worth of bread is not sufficient for them, that every one may take a little.8 One of his disciples, Andrew, Simon Peter’s brother, saith unto him,9 There is a lad here, who hath five barley loaves, and two fishes: but what are these among so many?10 Jesus said, Make the people sit down. Now there was much grass in the place. So the men sat down, in number about five thousand.11 Jesus therefore took the loaves; and having given thanks, he distributed to them that were set down; likewise also of the fishes as much as they would.12 And when they were filled, he saith unto his disciples, Gather up the broken pieces which remain over, that nothing be lost.13 So they gathered them up, and filled twelve baskets with broken pieces from the five barley loaves, which remained over unto them that had eaten.14 When therefore the people saw the sign which he did, they said, This is of a truth the prophet that cometh into the world.15 Jesus therefore perceiving that they were about to come and take him by force, to make him king, withdrew again into the mountain himself alone.16 And when evening came, his disciples went down unto the sea;17 and they entered into a boat, and were going over the sea unto Capernaum. And it was now dark, and Jesus had not yet come to them.18 And the sea was rising by reason of a great wind that blew.19 When therefore they had rowed about five and twenty or thirty furlongs, they behold Jesus walking on the sea, and drawing nigh unto the boat: and they were afraid.20 But he saith unto them, It is I; be not afraid.21 They were willing therefore to receive him into the boat: and straightway the boat was at the land whither they were going.22 On the morrow the multitude that stood on the other side of the sea saw that there was no other boat there, save one, and that Jesus entered not with his disciples into the boat, but that his disciples went away alone23 (howbeit there came boats from Tiberias nigh unto the place where they ate the bread after the Lord had given thanks):24 when the multitude therefore saw that Jesus was not there, neither his disciples, they themselves got into the boats, and came to Capernaum, seeking Jesus.25 And when they found him on the other side of the sea, they said unto him, Rabbi, when camest thou hither?26 Jesus answered them and said, Verily, verily, I say unto you, Ye seek me, not because ye saw signs, but because ye ate of the loaves, and were filled.27 Work not for the food which perisheth, but for the food which abideth unto eternal life, which the Son of man shall give unto you: for him the Father, even God, hath sealed.28 They said therefore unto him, What must we do, that we may work the works of God?29 Jesus answered and said unto them, This is the work of God, that ye believe on him whom he hath sent.30 They said therefore unto him, What then doest thou for a sign, that we may see, and believe thee? what workest thou?31 Our fathers ate the manna in the wilderness; as it is written, He gave them bread out of heaven to eat.32 Jesus therefore said unto them, Verily, verily, I say unto you, It was not Moses that gave you the bread out of heaven; but my Father giveth you the true bread out of heaven.33 For the bread of God is that which cometh down out of heaven, and giveth life unto the world.34 They said therefore unto him, Lord, evermore give us this bread.35 Jesus said unto them. I am the bread of life: he that cometh to me shall not hunger, and he that believeth on me shall never thirst.36 But I said unto you, that ye have seen me, and yet believe not.37 All that which the Father giveth me shall come unto me; and him that cometh to me I will in no wise cast out.38 For I am come down from heaven, not to do mine own will, but the will of him that sent me.39 And this is the will of him that sent me, that of all that which he hath given me I should lose nothing, but should raise it up at the last day.40 For this is the will of my Father, that every one that beholdeth the Son, and believeth on him, should have eternal life; and I will raise him up at the last day.41 The Jews therefore murmured concerning him, because he said, I am the bread which came down out of heaven.42 And they said, Is not this Jesus, the son of Joseph, whose father and mother we know? how doth he now say, I am come down out of heaven?43 Jesus answered and said unto them, Murmur not among yourselves.44 No man can come to me, except the Father that sent me draw him: and I will raise him up in the last day.45 It is written in the prophets, And they shall all be taught of God. Every one that hath heard from the Father, and hath learned, cometh unto me.46 Not that any man hath seen the Father, save he that is from God, he hath seen the Father.47 Verily, verily, I say unto you, He that believeth hath eternal life.48 I am the bread of life.49 Your fathers ate the manna in the wilderness, and they died.50 This is the bread which cometh down out of heaven, that a man may eat thereof, and not die.51 I am the living bread which came down out of heaven: if any man eat of this bread, he shall live for ever: yea and the bread which I will give is my flesh, for the life of the world.52 The Jews therefore strove one with another, saying, How can this man give us his flesh to eat?53 Jesus therefore said unto them, Verily, verily, I say unto you, Except ye eat the flesh of the Son of man and drink his blood, ye have not life in yourselves.54 He that eateth my flesh and drinketh my blood hath eternal life: and I will raise him up at the last day.55 For my flesh is meat indeed, and my blood is drink indeed.56 He that eateth my flesh and drinketh my blood abideth in me, and I in him.57 As the living Father sent me, and I live because of the Father; so he that eateth me, he also shall live because of me.58 This is the bread which came down out of heaven: not as the fathers ate, and died; he that eateth this bread shall live for ever.59 These things said he in the synagogue, as he taught in Capernaum.60 Many therefore of his disciples, when they heard this, said, This is a hard saying; who can hear it?61 But Jesus knowing in himself that his disciples murmured at this, said unto them, Doth this cause you to stumble?62 What then if ye should behold the Son of man ascending where he was before?63 It is the spirit that giveth life; the flesh profiteth nothing: the words that I have spoken unto you are spirit, and are life.64 But there are some of you that believe not. For Jesus knew from the beginning who they were that believed not, and who it was that should betray him.65 And he said, For this cause have I said unto you, that no man can come unto me, except it be given unto him of the Father.66 Upon this many of his disciples went back, and walked no more with him.67 Jesus said therefore unto the twelve, Would ye also go away?68 Simon Peter answered him, Lord, to whom shall we go? thou hast the words of eternal life.69 And we have believed and know that thou art the Holy One of God.70 Jesus answered them, Did not I choose you the twelve, and one of you is a devil?71 Now he spake of Judas the son of Simon Iscariot, for he it was that should betray him, being one of the twelve.