YAH 8
1 t Yesu kuwa ya hau Dutsen Zaitun. 2 t Da sassafe kuma ya sāke shiga Haikali. Duk mutane suka zo wurinsa, ya kuwa zauna yana koya musu. 3 Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka kawo wata mace da aka kama da zina. Da suka tsai da ita a tsaka, 4 suka ce masa, “Malam, matan nan an kama ta ne, suna cikin yin zina. 5 t To, a Attaura Musa ya umarce mu mu kashe irin waɗannan da jifa, kai kuwa me ka ce?” 6 t Sun faɗi haka ne don su gwada shi, ko sa sami hanyar kai ƙararsa. Amma Yesu ya sunkuya, ya yi ta rubutu a ƙasa da yatsa. 7 t Da suka dinga tambayarsa sai ya ɗaga, ya ce musu, “To, marar zunubi a cikinku ya fara jifanta da dutse.” 8 Sai ya sāke sunkuyawa, ya yi ta rubutu a ƙasa. 9 Su kuwa da suka ji haka suka fita da ɗaya ɗaya, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, aka bar Yesu shi kaɗai, da matar tsaye a tsakiya. 10 Sai Yesu ya ɗaga, ya ce mata, “Uwargida, ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?”
11 t Ta ce, “Babu, ya Ubangiji.” Sai Yesu ya ce, “Ni ma ban hukunta ki ba. Yi tafiyarki. Daga yau kada ki ƙara yin zunubi.”]Yesu Hasken Duniya
12 t Sai Yesu ya ƙara musu da cewa, “Ni ne Hasken duniya. Wanda yake bi na ba zai yi tafiya a duhu ba, amma zai sami hasken rai,” 13 t Saboda haka Farisiyawa suka ce masa, “Kanka kake wa shaida, shaidarka kuwa ba tabbatacciya ba ce.” 14 t Yesu ya amsa musu ya ce, “Ko na shaidi kaina, ai, shaidata tabbatacciya ce, domin na san inda na fito, da kuma inda za ni. Amma ku ba ku san inda na fito ba, ko kuma inda za ni. 15 t Ku kuna hukunci irin na duniya ne, ni kuwa ba na hukunta kowa. 16 t Amma ko da zan yi hukunci, hukuncina na gaskiya ne, domin ba ni kaɗai nake ba, ni da Uba wanda ya aiko ni ne. 17 t A Attaurarku ma a rubuce yake, cewa shaidar mutum biyu tabbatacciya ce. 18 t Ni ne nake shaidar kaina, Uba da ya aiko ni kuma yana shaidata.” 19 t Saboda haka suka ce masa, “Ina Uban naka yake?” Yesu ya amsa ya ce, “Ko ni ko Ubana, ba wanda kuka sani. Da kun san ni, da kun san Ubana ma.”
20 t Ya faɗi wannan magana ne a baitulmalin Haikali, lokacin da yake koyarwa a wurin. Duk da haka ba wanda ya kama shi, don lokacinsa bai yi ba tukuna.Inda Za Ni Ba Ku Iya Zuwa Ba
21 t Sai ya ƙara ce musu, “Zan yi tafiya, za ku kuwa neme ni, amma za ku mutu da zunubinku. Inda za ni kuwa ba za ku iya zuwa ba.” 22 Saboda haka sai Yahudawa suka ce, “Wato zai kashe kansa ke nan da ya ce, ‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba’?” 23 t Sai ya ce musu, “Ku daga ƙasa kuke, ni kuwa daga sama nake. Ku na duniyan nan ne, ni kuwa ba na duniyar nan ba ne.” 24 t Shi ya sa na ce muku za ku mutu da zunubanku. Domin in ba ku gaskata ni ne shi ba, za ku mutu da zunubanku.” 25 Sai suka ce masa, “Kai wane ne?” Yesu ya ce musu, “Daidai yadda na gaya muku. 26 t Akwai abubuwa da yawa da zan faɗa game da ku, in kuma hukunta. Amma shi wannan da ya aiko ni mai gaskiya ne. Abin da na jiyo daga gare shi kuwa, shi nake shaida wa duniya.” 27 Ba su gane maganar Uba yake yi musu ba. 28 t Sai Yesu ya ce, “Sa'ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa'an nan ne za ku gane ni ne shi, ba na yin kome kuma ni kaɗai, sai dai Uba ya koya mini, haka nake faɗa. 29 t Wanda kuwa ya aiko ni yana tare da ni, bai bar ni ni kaɗai ba, domin koyaushe ina aikata abin da yake so.”
30 t Sa'ad da Yesu yake faɗar haka, mutane da yawa suka gaskata da shi.Gaskiya Za ta 'Yanta Ku
31 t Sai Yesu ya ce wa Yahudawan nan da suka gaskata shi, “In dai kun zauna kan maganata, hakika ku almajiraina ne. 32 t Za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta 'yanta ku.”
33 t Suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne, ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya kuma za ka ce za a 'yanta mu?”
34 t Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai aikata zunubi bawan zunubi ne. 35 t Ai, bawa ba ya ɗorewa a gida har abada, ɗa kuwa yana ɗorewa. 36 In kuwa Ɗan ya 'yanta ku, za ku 'yantu, 'yantuwar gaske. 37 t Na san dai ku zuriyar Ibrahim ne, amma kuwa kuna neman kashe ni, don maganata ba ta shigarku.
38 t Ina faɗar abin da na gani a wurin Ubana, ku kuma kuna yin abin da kuka ji daga wurin naku uba.”Ubanku Iblis Ne
39 t Suka amsa masa suka ce, “Ai, Ibrahim ne ubanmu.” Yesu ya ce musu, “Da ku 'ya'yan Ibrahim ne, da sai ku yi aikin da Ibrahim ya yi. 40 t Ga shi yanzu, kuna neman kashe ni, ni mutumin da na gaya muku gaskiyar da na ji wurin Allah. Ba haka Ibrahim ya yi ba. 41 t Ku kuna aikin da ubanku yake yi ne.” Suka ce masa, “Ba a haife mu daga fasikanci ba, ubanmu ɗaya ne, wato Allah.” 42 t Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku da kun ƙaunace ni, domin daga wurin Allah na fito, ga ni nan kuwa. Ban zo domin kaina ba, shi ne ya aiko ni. 43 Don me ba kwa gane maganata? Don ba kwa iya jimirin jin maganata ne. 44 t Ku na ubanku Iblis ne, niyyarku kuwa ku aikata burin ubanku. Shi dā ma tun farko mai kisankai ne, bai zauna kan gaskiya ba, don ba ruwansa da gaskiya. Duk sa'ad da yake ƙarya, cinikinsa yake yi, don shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma. 45 t Amma domin ina faɗar gaskiya, ba kwa gaskata ni. 46 A cikinku wa zai iya haƙƙaƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya nake faɗa, to, don me ba kwa gaskata ni?
47 t Na Allah yakan saurari Maganar Allah. Abin da ya sa ba kwa sauraronta ke nan, don ku ba na Allah ba ne.”Kafin Ibrahim, Nake
48 t Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ashe, gaskiyarmu da muka ce kai Basamariye ne, kana kuma da iska.” 49 Yesu ya amsa ya ce, “Ni ba mai iska ba ne. Ubana nake girmamawa, ku kuwa wulakanta ni kuke yi. 50 t Ba ni nake nemar wa kaina girma ba, akwai mai nemar mini, shi ne kuma mai yin shari'a. 51 t Lalle hakika, ina gaya muku, kowa ya kiyaye maganata ba zai mutu ba har abada.” 52 Sai Yahudawa suka ce masa, “To, yanzu kam, mun tabbata kana da iska. Ai, Ibrahim ya mutu, haka ma annabawa, kana kuwa cewa kowa ya kiyaye maganarka ba zai mutu ba har abada. 53 t Wato ka fi ubanmu Ibrahim ne, ya kuwa mutu? Annabawa ma sun mutu! Wa ka mai da kanka ne?” 54 t Yesu ya amsa ya ce, “In ma na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba a bakin kome take ba. Ubana shi ne mai ɗaukaka ni, wanda kuke cewa, shi ne Allahnku. 55 t Ku ba ku san shi ba, amma ni na san shi. Da na ce ban san shi ba, da na zama maƙaryaci kamarku. Amma na san shi, ina kuma kiyaye magana tasa. 56 t Ubanku Ibrahim ya yi farin ciki matuƙa ya sami ganin zamanina, ya kuwa gan shi, ya yi murna.” 57 Sai Yahudawa suka ce masa, “Har yanzu ma ba ka kai shekara hamsin ba, wai kuwa har ka ga Ibrahim!” 58 t Sai Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne.” 59 t Don haka suka ɗebo duwatsu su jajjefe shi. Yesu kuwa ya ɓuya, ya fita daga Haikalin.
John 8
1 but Jesus went unto the mount of Olives.2 And early in the morning he came again into the temple, and all the people came unto him; and he sat down, and taught them.3 And the scribes and the Pharisees bring a woman taken in adultery; and having set her in the midst,4 they say unto him, Teacher, this woman hath been taken in adultery, in the very act.5 Now in the law Moses commanded us to stone such: what then sayest thou of her?6 And this they said, trying him, that they might have whereof to accuse him. But Jesus stooped down, and with his finger wrote on the ground.7 But when they continued asking him, he lifted up himself, and said unto them, He that is without sin among you, let him first cast a stone at her.8 And again he stooped down, and with his finger wrote on the ground.9 And they, when they heard it, went out one by one, beginning from the eldest, even unto the last: and Jesus was left alone, and the woman, where she was, in the midst.10 And Jesus lifted up himself, and said unto her, Woman, where are they? did no man condemn thee?11 And she said, No man, Lord. And Jesus said, Neither do I condemn thee: go thy way; from henceforth sin no more.12 Again therefore Jesus spake unto them, saying, I am the light of the world: he that followeth me shall not walk in the darkness, but shall have the light of life.13 The Pharisees therefore said unto him, Thou bearest witness of thyself; thy witness is not true.14 Jesus answered and said unto them, Even if I bear witness of myself, my witness is true; for I know whence I came, and whither I go; but ye know not whence I come, or whither I go.15 Ye judge after the flesh; I judge no man.16 Yea and if I judge, my judgment is true; for I am not alone, but I and the Father that sent me.17 Yea and in your law it is written, that the witness of two men is true.18 I am he that beareth witness of myself, and the Father that sent me beareth witness of me.19 They said therefore unto him, Where is thy Father? Jesus answered, Ye know neither me, nor my Father: if ye knew me, ye would know my Father also.20 These words spake he in the treasury, as he taught in the temple: and no man took him; because his hour was not yet come.21 He said therefore again unto them, I go away, and ye shall seek me, and shall die in your sin: whither I go, ye cannot come.22 The Jews therefore said, Will he kill himself, that he saith, Whither I go, ye cannot come?23 And he said unto them, Ye are from beneath; I am from above: ye are of this world; I am not of this world.24 I said therefore unto you, that ye shall die in your sins: for except ye believe that I am he, ye shall die in your sins.25 They said therefore unto him, Who art thou? Jesus said unto them, Even that which I have also spoken unto you from the beginning.26 I have many things to speak and to judge concerning you: howbeit he that sent me is true; and the things which I heard from him, these speak I unto the world.27 They perceived not that he spake to them of the Father.28 Jesus therefore said, When ye have lifted up the Son of man, then shall ye know that I am he, and that I do nothing of myself, but as the Father taught me, I speak these things.29 And he that sent me is with me; he hath not left me alone; for I do always the things that are pleasing to him.30 As he spake these things, many believed on him.31 Jesus therefore said to those Jews that had believed him, If ye abide in my word, then are ye truly my disciples;32 and ye shall know the truth, and the truth shall make you free.33 They answered unto him, We are Abraham’s seed, and have never yet been in bondage to any man: how sayest thou, Ye shall be made free?34 Jesus answered them, Verily, verily, I say unto you, Every one that committeth sin is the bondservant of sin.35 And the bondservant abideth not in the house for ever: the son abideth for ever.36 If therefore the Son shall make you free, ye shall be free indeed.37 I know that ye are Abraham’s seed: yet ye seek to kill me, because my word hath not free course in you.38 I speak the things which I have seen with my Father: and ye also do the things which ye heard from your father.39 They answered and said unto him, Our father is Abraham. Jesus saith unto them, If ye were Abraham’s children, ye would do the works of Abraham.40 But now ye seek to kill me, a man that hath told you the truth, which I heard from God: this did not Abraham.41 Ye do the works of your father. They said unto him, We were not born of fornication; we have one Father, even God.42 Jesus said unto them, If God were your Father, ye would love me: for I came forth and am come from God; for neither have I come of myself, but he sent me.43 Why do ye not understand my speech? Even because ye cannot hear my word.44 Ye are of your father the devil, and the lusts of your father it is your will to do. He was a murderer from the beginning, and standeth not in the truth, because there is no truth in him. When he speaketh a lie, he speaketh of his own: for he is a liar, and the father thereof.45 But because I say the truth, ye believe me not.46 Which of you convicteth me of sin? If I say truth, why do ye not believe me?47 He that is of God heareth the words of God: for this cause ye hear them not, because ye are not of God.48 The Jews answered and said unto him, Say we not well that thou art a Samaritan, and hast a demon?49 Jesus answered, I have not a demon; but I honor my Father, and ye dishonor me.50 But I seek not mine own glory: there is one that seeketh and judgeth.51 Verily, verily, I say unto you, If a man keep my word, he shall never see death.52 The Jews said unto him, Now we know that thou hast a demon. Abraham died, and the prophets; and thou sayest, If a man keep my word, he shall never taste of death.53 Art thou greater than our father Abraham, who died? and the prophets died: whom makest thou thyself?54 Jesus answered, If I glorify myself, my glory is nothing: it is my Father that glorifieth me; of whom ye say, that he is your God;55 and ye have not known him: but I know him; and if I should say, I know him not, I shall be like unto you, a liar: but I know him, and keep his word.56 Your father Abraham rejoiced to see my day; and he saw it, and was glad.57 The Jews therefore said unto him, Thou art not yet fifty years old, and hast thou seen Abraham?58 Jesus said unto them, Verily, verily, I say unto you, Before Abraham was born, I am.59 They took up stones therefore to cast at him: but Jesus hid himself, and went out of the temple.