YAH 9
Warkar da Wanda aka Haifa Makaho
1 Yesu na wucewa sai ya ga wani mutum da aka haifa makaho. 2 t Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Ya Shugaba, wa ya yi zunubi da aka haifi mutumin nan makaho, shi, ko iyayensa?” 3 t Yesu ya amsa ya ce, “Ba domin mutumin nan ko iyayensa sun yi zunubi ba, sai domin a nuna aikin Allah ne a kansa. 4 t Lalle ne mu yi aikin wanda ya aiko ni tun da sauran rana. Ai, dare zai yi sa'ad da ba mai iya aiki. 5 t Muddin ina duniya ni ne hasken duniya.” 6 t Da ya faɗi haka sai ya tofa yau a ƙasa, ya cuɗa ƙasa, ya shafa a idanun makahon, 7 t ya ce masa, “Je ka, ka wanke ido a ruwan Siluwam,” wato aikakke. Shi ke nan sai ya je ya wanke ido, ya komo yana gani. 8 t Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, suka ce, “Ashe, ba wannan ne yakan zauna yana bara ba?” 9 Waɗansu suka ce, “Shi ne mana.” Waɗansu kuwa suka ce, “A'a, kai dai, sun yi kama.” Shi kuwa ya ce, “Sosai ni ne!” 10 Sai suka ce masa, “To, ƙaƙa aka yi idanunka suka buɗe?” 11 t Ya amsa ya ce, “Mutumin nan da ake kira Yesu ne ya cuɗa ƙasa ya shafa mini a idanu, ya ce mini, ‘Je ka Siluwam ka wanke ido.’ Na kuwa je na wanke, sai na sami gani.”
12 Suka ce masa, “Ina yake?” Ya ce, “Ban sani ba.”Farisiyawa Sun Bincika Labarin Wanda aka Warkar
13 Sai suka kai wa Farisiyawa mutumin da yake makaho a dā. 14 t To, ran Asabar ne Yesu ya cuɗa ƙasar ya buɗe masa ido. 15 t Farisiyawa ma suka tambaye shi ta yadda aka yi ya sami gani. Ya ce musu, “Cuɗaɗɗiyar ƙasa ya shafa a idona, na wanke, ina gani.” 16 t Saboda haka, waɗansu Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye Asabar.” Waɗansu kuwa suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai iya yin mu'ujizai haka?” Sai rabuwa ta shiga tsakaninsu.
17 t Sai suka sāke ce wa makahon, “To, kai fa, me ka gani game da shi, da yake kai ya buɗe wa ido?” Ya ce, “Ai, annabi ne.”
18 t Yahudawa kam, ba su gaskata shi makaho ne a dā ba, ya kuma sami gani, har suka kira iyayen wanda ya sami ganin, 19 suka tambaye su suka ce, “Wannan ɗanku ne da kuke cewa an haife shi makaho? To, ta yaya yake iya gani yanzu?” 20 Sai iyayen nasa suka amsa suka ce, “Mun dai san wannan ɗanmu ne, makaho ne aka haife shi. 21 Amma ta yadda aka yi yake gani yanzu ba mu sani ba, ba mu ma san wanda ya buɗe idon ba. Ku tambaye shi, ai, ba yaro ba ne, zai faɗa da bakinsa.” 22 t Iyayensa sun faɗi haka ne don tsoron Yahudawa, don dā ma Yahudawa sun ƙulla, cewa kowa ya amsa, cewa shi ne Almasihu, za a fisshe shi daga jama'a.
23 t Shi ya sa iyayensa suka ce, “Ai, ba yaro ba ne, ku tambaye shi.”
24 t Sai suka sāke kiran mutumin nan da yake makaho a dā, suka ce masa, “Ka tsoraci Allah dai! Mu kam, mun san mutumin nan mai zunubi ne.” 25 Sai ya amsa ya ce, “Ko mai zunubi ne, ni ban sani ba. Abu ɗaya kam, na sani, dā ni makaho ne, yanzu kuwa ina gani.” 26 Sai suka ce masa, “Shin, me ya yi maka? Ta yaya ya buɗe maka ido?” 27 t Ya amsa musu ya ce, “Na riga na faɗa muku, ba ku ji ba. Don me kuke so ku sāke ji? Ko ku ma kuna so ku zama almajiransa ne?” 28 t Sai suka fāɗa shi da zagi, suna cewa, “Kai ne dai almajirin wannan ɗin, mu kam, almajiran Musa ne. 29 t Mun dai sani Allah ya yi magana da Musa, amma wannan ba mu san ta inda ya fito ba.” 30 Sai mutumin ya amsa musu ya ce, “Yau ga abin mamaki! Ashe, ba ku san ta inda ya fito ba, ga shi kuwa, ya buɗe mini ido! 31 t Mun sani Allah ba ya sauraron masu zunubi, amma duk wanda yake mai bautar Allah, yake kuma aikata nufinsa, Allah yakan saurare shi. 32 Tun da aka fara duniya ba a taɓa jin wani ya buɗe idon wanda aka haifa makaho ba. 33 t Da mutumin nan ba daga Allah ya fito ba, da ba abin da zai iya yi.”
34 t Suka amsa masa suka ce, “Kai da aka haifa a baƙin zunubi ne za ka koya mana?” Sai suka kore shi.Makanta ta Ruhu
35 Yesu ya ji labari sun kore shi. Da ya same shi, ya ce, “Ka gaskata da Ɗan Mutum ko?” 36 t Ya amsa ya ce, “Wane ne shi, ya Shugaba, da zan gaskata da shi?” 37 t Yesu ya ce masa, “Ai, ka gan shi, shi ne ma mai magana da kai.” 38 t Sai ya ce, “Ya Ubangiji, na ba da gaskiya,” ya kuma yi masa sujada. 39 t Yesu ya ce, “Na shigo duniyan nan ne don rarrabewa, domin waɗanda ba sa gani su gani, waɗanda suke gani kuma su makance.” 40 t Da Farisiyawan nan da suke tare da shi suka ji haka, suka ce masa, “Wato mu ma makafi ne?” 41 t Yesu ya ce musu, “Ai, da makafi ne ku, da ba ku da zunubi. Amma da yake kun ce kuna gani, to, zunubinku ya tabbata.
John 9
1 And as he passed by, he saw a man blind from his birth.2 And his disciples asked him, saying, Rabbi, who sinned, this man, or his parents, that he should be born blind?3 Jesus answered, Neither did this man sin, nor his parents: but that the works of God should be made manifest in him.4 We must work the works of him that sent me, while it is day: the night cometh, when no man can work.5 When I am in the world, I am the light of the world.6 When he had thus spoken, he spat on the ground, and made clay of the spittle, and anointed his eyes with the clay,7 and said unto him, Go, wash in the pool of Siloam (which is by interpretation, Sent). He went away therefore, and washed, and came seeing.8 The neighbors therefore, and they that saw him aforetime, that he was a beggar, said, Is not this he that sat and begged?9 Others said, It is he: others said, No, but he is like him. He said, I am he.10 They said therefore unto him, How then were thine eyes opened?11 He answered, The man that is called Jesus made clay, and anointed mine eyes, and said unto me, Go to Siloam, and wash: so I went away and washed, and I received sight.12 And they said unto him, Where is he? He saith, I know not.13 They bring to the Pharisees him that aforetime was blind.14 Now it was the sabbath on the day when Jesus made the clay, and opened his eyes.15 Again therefore the Pharisees also asked him how he received his sight. And he said unto them, He put clay upon mine eyes, and I washed, and I see.16 Some therefore of the Pharisees said, This man is not from God, because he keepeth not the sabbath. But others said, How can a man that is a sinner do such signs? And there was division among them.17 They say therefore unto the blind man again, What sayest thou of him, in that he opened thine eyes? And he said, He is a prophet.18 The Jews therefore did not believe concerning him, that he had been blind, and had received his sight, until they called the parents of him that had received his sight,19 and asked them, saying, Is this your son, who ye say was born blind? How then doth he now see?20 His parents answered and said, We know that this is our son, and that he was born blind:21 but how he now seeth, we know not; or who opened his eyes, we know not: ask him; he is of age; he shall speak for himself.22 These things said his parents, because they feared the Jews: for the Jews had agreed already, that if any man should confess him to be Christ, he should be put out of the synagogue.23 Therefore said his parents, He is of age; ask him.24 So they called a second time the man that was blind, and said unto him, Give glory to God: we know that this man is a sinner.25 He therefore answered, Whether he is a sinner, I know not: one thing I know, that, whereas I was blind, now I see.26 They said therefore unto him, What did he to thee? How opened he thine eyes?27 He answered them, I told you even now, and ye did not hear; wherefore would ye hear it again? would ye also become his disciples?28 And they reviled him, and said, Thou art his disciple; but we are disciples of Moses.29 We know that God hath spoken unto Moses: but as for this man, we know not whence he is.30 The man answered and said unto them, Why, herein is the marvel, that ye know not whence he is, and yet he opened mine eyes.31 We know that God heareth not sinners: but if any man be a worshipper of God, and do his will, him he heareth.32 Since the world began it was never heard that any one opened the eyes of a man born blind.33 If this man were not from God, he could do nothing.34 They answered and said unto him, Thou wast altogether born in sins, and dost thou teach us? And they cast him out.35 Jesus heard that they had cast him out; and finding him, he said, Dost thou believe on the Son of God?36 He answered and said, And who is he, Lord, that I may believe on him?37 Jesus said unto him, Thou hast both seen him, and he it is that speaketh with thee.38 And he said, Lord, I believe. And he worshipped him.39 And Jesus said, For judgment came I into this world, that they that see not may see; and that they that see may become blind.40 Those of the Pharisees who were with him heard these things, and said unto him, Are we also blind?41 Jesus said unto them, If ye were blind, ye would have no sin: but now ye say, We see: your sin remaineth.