LUK 10
Yesu Ya Aiki Saba'in Ɗin
1 t Bayan wannan Ubangiji ya zaɓi waɗansu mutum saba'in, ya aike su biyu biyu, su riga shi gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da shi kansa za shi. 2 t Ya ce musu, “Girbin na da yawa, amma masu yinsa kaɗan ne. Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi ya turo masu girbi, su yi masa girbi. 3 t To, sai ku tafi. Ga shi na aike ku kamar 'yan tumaki a tsakiyar kyarketai. 4 Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko burgami, ko takalma. Kada ku yi doguwar gaisuwa da kowa a hanya. 5 Duk gidan da kuka sauka, ku fara da cewa, ‘Salama alaikun mutanen gidan nan!’ 6 In akwai da ɗan salama a gidan, to, salamarku za ta tabbata a gare shi. In kuwa babu, za ta komo muku. 7 t Ku zauna a gidan, kuna ci kuna shan duk irin abin da suka ba ku, domin ma'aikaci ya cancanci ladansa. Kada ku riƙa sāke masauki. 8 t Duk garin da kuka shiga, in an yi na'am da ku, ku ci duk irin abin da aka kawo muku. 9 t Ku warkar da marasa lafiya da suke cikinsa, ku kuma ce musu, ‘Mulkin Allah ya kusato ku.’ 10 Amma duk garin da kuka shiga ba a yi na'am da ku ba, sai ku zaga kwararo kwararo, kuna cewa, 11 t ‘Ko da ƙurar garinku da ta ɗafe a jikin ƙafafunmu ma, mun karkaɗe muku. Amma duk da haka ku sani Mulkin Allah ya kusato.’
12 t Ina dai gaya muku, a ran nan, za a fi haƙurce wa Saduma a kan garin nan.”Tsawata wa Garuruwan da ba su Tuba Ba
(Mat 11.20-24)
13 t “Kaitonki, Korasinu! Kaitonki, Betsaida! Da mu'ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba, sun zauna sāye da tsumma, suna hurwa da toka. 14 Amma a Ranar Shari'a, za a fi haƙurce wa Taya da Sidon a kanku.
15 t Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A'a, ƙasƙantar da ke za a yi har Hades.
16 t “Duk mai sauraronku, ni yake saurare. Mai ƙinku kuma, ni yake ƙi. Duk mai ƙina kuwa, wanda ya aiko ni ne ya ƙi.”Komowar Saba'in Ɗin
17 t Sai kuma saba'in ɗin nan suka komo da farin ciki, suka ce, “Ya Ubangiji, har aljannu ma suna mana biyayya albarkacin sunanka!” 18 t Sai ya ce musu, “Na ga Shaiɗan ya faɗo daga sama kamar walƙiya. 19 t Ga shi, na ba ku ikon taka macizai da kunamai, ku kuma rinjaye a kan dukan ikon Maƙiyi, ba kuwa abin da zai cuce ku ko kaɗan.
20 t Duk da haka, kada ku yi farin ciki aljannu na yi muku biyayya, sai dai ku yi farin cikin an rubuta sunayenku a Sama.”Yesu Ya Yi Farin Ciki
(Mat 11.25-27; Mar 13.16-17)
21 t A wannan lokaci ya yi farin ciki matuƙa ta Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai. Hakika na gode maka ya Uba, domin wannan shi ne nufinka na alheri.
22 t Kowane abu Ubana ne ya mallaka mini. Ba kuwa wanda ya san ko wane ne Ɗan sai dai Uban, ko kuma ya san ko wane ne Uban sai dai Ɗan, da kuma wanda Ɗan yake so ya bayyana wa.”
23 Sai ya juya wajen almajiransa, ya ce musu a keɓance, “Albarka tā tabbata ga idanun da suka ga abin da kuka gani.
24 t Ina gaya muku, annabawa da sarakuna da yawa suna son ganin abin da kuke gani, amma ba su gani ba, suna kuma so su ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.”Basamariyen da Ya Nuna Jinƙai
25 t Sai ga wani masanin Attaura ya tashi tsaye yana gwada shi, ya ce, “Malam, me zan yi in gaji rai madawwami?” 26 Yesu ya ce musu, “Me yake rubuce a Attaura? Yaya kake karantawa?” 27 t Sai ya amsa ya ce, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan ƙarfinka, da dukkan hankalinka. Ka kuma ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.”
28 t Yesu ya ce masa, “Ka amsa daidai. Ka riƙa yin haka, za ka rayu.”
29 t Shi kuwa mutumin, don yana son baratar da kansa, ya ce wa Yesu, “To, wane ne ɗan'uwa nawa?” 30 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum ne ya tashi daga Urushalima za shi Yariko. Sai 'yan fashi suka fāɗa shi, suka tuɓe shi, suka yi masa mugun dūka, suka tafi suka bar shi rai ga Allah. 31 t Daga nan ya zamana wani firist ya biyo ta wannan hanya. Da ya gan shi sai ya zaga ta ɗaya gefen, ya wuce abinsa. 32 Haka kuma wani Balawe, da ya iso wurin ya gan shi, shi ma ya zaga ta ɗaya gefen, ya wuce abinsa. 33 t Ana nan sai hanya ta kawo wani Basamariye inda yake. Da ya gan shi, sai tausayi ya kama shi, 34 ya je wurinsa, ya ɗaɗɗaure masa raunukansa, yana zuba musu mai da ruwan inabi. Sa'an nan ya ɗora shi a kan dabbarsa, ya kai shi masauki, ya yi ta jiyyarsa. 35 Kashegari ya ɗebo dinari biyu ya ba maigidan, ya ce, ‘Ka yi jiyyarsa, duk kuma abin da ka ɓatar bayan wannan, in na dawo sai in biya ka.’ 36 To, a cikin ukun nan, wa kake tsammani ya zama ɗan'uwa ga wanda 'yan fashin suka faɗa wa?”
37 Sai ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.” Sai Yesu ya ce masa, “Kai ma, ka je ka riƙa yin haka.”Yesu Ya Ziyarci Marta da Maryamu
38 t Suna tafiya, sai ya shiga wani ƙauye, wata mace kuma mai suna Marta ta sauke da shi a gidanta. 39 t Tana kuwa da 'yar'uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana sauraron magana tasa. 40 t Marta kuwa yawan hidimomi ya ɗauke mata hankali, sai ta je gunsa, ta ce, “Ya Ubangiji, ba ka kula ba, 'yar'uwata ta bar ni ina hidima ni kaɗai? Gaya mata ta taimake ni mana.” 41 t Amma Ubangiji ya amsa mata ya ce, “Marta, Marta! Hankalinki a tashe yake, kina kuma damuwa kan abu da yawa. 42 t Bukatu kima ne, ta ainihi ɗaya ce. Maryamu ta zaɓi abu mai kyau, ba kuwa za a karɓe mata ba.”
Luke 10
1 Now after these things the Lord appointed seventy others, and sent them two and two before his face into every city and place, whither he himself was about to come.2 And he said unto them, The harvest indeed is plenteous, but the laborers are few: pray ye therefore the Lord of the harvest, that he send forth laborers into his harvest.3 Go your ways; behold, I send you forth as lambs in the midst of wolves.4 Carry no purse, no wallet, no shoes; and salute no man on the way.5 And into whatsoever house ye shall enter, first say, Peace be to this house.6 And if a son of peace be there, your peace shall rest upon him: but if not, it shall turn to you again.7 And in that same house remain, eating and drinking such things as they give: for the laborer is worthy of his hire. Go not from house to house.8 And into whatsoever city ye enter, and they receive you, eat such things as are set before you:9 and heal the sick that are therein, and say unto them, The kingdom of God is come nigh unto you.10 But into whatsoever city ye shall enter, and they receive you not, go out into the streets thereof and say,11 Even the dust from your city, that cleaveth to our feet, we wipe off against you: nevertheless know this, that the kingdom of God is come nigh.12 I say unto you, it shall be more tolerable in that day for Sodom, than for that city.13 Woe unto thee, Chorazin! woe unto thee, Bethsaida! for if the mighty works had been done in Tyre and Sidon, which were done in you, they would have repented long ago, sitting in sackcloth and ashes.14 But it shall be more tolerable for Tyre and Sidon in the judgment, than for you.15 And thou, Capernaum, shalt thou be exalted unto heaven? thou shalt be brought down unto Hades.16 He that heareth you heareth me; and he that rejecteth you rejecteth me; and he that rejecteth me rejecteth him that sent me.17 And the seventy returned with joy, saying, Lord, even the demons are subject unto us in thy name.18 And he said unto them, I beheld Satan fallen as lightning from heaven.19 Behold, I have given you authority to tread upon serpents and scorpions, and over all the power of the enemy: and nothing shall in any wise hurt you.20 Nevertheless in this rejoice not, that the spirits are subject unto you; but rejoice that your names are written in heaven.21 In that same hour he rejoiced in the Holy Spirit, and said, I thank thee, O Father, Lord of heaven and earth, that thou didst hide these things from the wise and understanding, and didst reveal them unto babes: yea, Father; for so it was well-pleasing in thy sight.22 All things have been delivered unto me of my Father: and no one knoweth who the Son is, save the Father; and who the Father is, save the Son, and he to whomsoever the Son willeth to reveal him.23 And turning to the disciples, he said privately, Blessed are the eyes which see the things that ye see:24 for I say unto you, that many prophets and kings desired to see the things which ye see, and saw them not; and to hear the things which ye hear, and heard them not.25 And behold, a certain lawyer stood up and made trial of him, saying, Teacher, what shall I do to inherit eternal life?26 And he said unto him, What is written in the law? how readest thou?27 And he answering said, Thou shalt love the Lord thy God with all thy heart, and with all thy soul, and with all thy strength, and with all thy mind; and thy neighbor as thyself.28 And he said unto him, Thou hast answered right: this do, and thou shalt live.29 But he, desiring to justify himself, said unto Jesus, And who is my neighbor?30 Jesus made answer and said, A certain man was going down from Jerusalem to Jericho; and he fell among robbers, who both stripped him and beat him, and departed, leaving him half dead.31 And by chance a certain priest was going down that way: and when he saw him, he passed by on the other side.32 And in like manner a Levite also, when he came to the place, and saw him, passed by on the other side.33 But a certain Samaritan, as he journeyed, came where he was: and when he saw him, he was moved with compassion,34 and came to him, and bound up his wounds, pouring on them oil and wine; and he set him on his own beast, and brought him to an inn, and took care of him.35 And on the morrow he took out two shillings, and gave them to the host, and said, Take care of him; and whatsoever thou spendest more, I, when I come back again, will repay thee.36 Which of these three, thinkest thou, proved neighbor unto him that fell among the robbers?37 And he said, He that showed mercy on him. And Jesus said unto him, Go, and do thou likewise.38 Now as they went on their way, he entered into a certain village: and a certain woman named Martha received him into her house.39 And she had a sister called Mary, who also sat at the Lord’s feet, and heard his word.40 But Martha was cumbered about much serving; and she came up to him, and said, Lord, dost thou not care that my sister did leave me to serve alone? bid her therefore that she help me.41 But the Lord answered and said unto her, Martha, Martha, thou art anxious and troubled about many things:42 but one thing is needful: for Mary hath chosen the good part, which shall not be taken away from her.