LUK 11
Koyarwar Yesu a kan Addu'a
(Mat 6.9-15; 7.7-11)
1 t Wata rana Yesu yana addu'a a wani wuri. Bayan da ya gama, sai wani a cikin almajiransa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka koya mana addu'a, kamar yadda Yahaya ya koya wa almajiransa.”
2 t Sai ya ce musu, “In kuna addu'a ku ce,
‘Ya Uba, a kiyaye sunanka da tsarki,
Mulkinka yă zo,
3 Ka ba mu abincin yau da na kullum.
4 t Ka gafarta mana zunubanmu, gama mu ma muna gafarta wa duk wanda yake yi mana laifi.
Kada ka kai mu wurin jaraba.’ ”
5 Ya kuma gaya musu, “Misali, idan waninku yana da amini, ya je wurinsa da tsakar dare ya ce masa, ‘Wāne, ranta mini gurasa uku mana, 6 ga shi, wani abokina matafiyi ya sauka a wurina yanzu, ba ni kuwa da abincin da zan ba shi,’ 7 sa'an nan aminin ya amsa masa daga ciki ya ce, ‘Kada ka dame ni, ai, an kulle ƙofa, da ni da 'ya'yana duk mun kwanta, ba zan iya tashi in ba ka wani abu ba.’ 8 t Ina gaya muku, ko da yake ba zai tashi ya ba shi wani abu don yana amininsa ba, amma saboda nacinsa zai tashi ya ba shi ko nawa yake bukata. 9 t Ina dai gaya muku, ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku. 10 Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa. 11 Wane uba ne a cikinku, da ɗansa zai roƙe shi [gurasa, ya ba shi dutse? Ko ya roƙe shi] kifi, ya ba shi maciji? 12 Ko kuwa ya roƙe shi ƙwai, ya ba shi kunama?
13 To, ku da kuke mugaye ma kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama zai ba da Ruhu Mai Tsarki ga masu roƙonsa.”Yesu da Ba'alzabul
(Mat 12.22-30; Mar 3.20-27)
14 t Wata rana Yesu yana fitar da beben aljan. Da aljanin ya fita, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki. 15 t Amma waɗansunsu suka ce, “Ai, da ikon Ba'alzabul sarkin aljannu yake fitar da aljannu.” 16 t Waɗansu kuwa, don su gwada shi, suka nema ya nuna musu wata alama daga Sama. 17 t Shi kuwa da ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da ya rabu a kan gāba, zai lalace. Haka kuma, in gida ya rabu a kan gāba, zai baje. 18 t In kuma Shaiɗan ya rabu a kan gāba, yaya mulkinsa zai ɗore? Ga shi, kun ce da ikon Ba'alzabul nake fitar da aljannu. 19 In kuwa da ikon Ba'alzabul nake fitar da aljannu, to, 'ya'yanku fa, da ikon wa suke fitarwa? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku. 20 t Ni kuwa in da ikon Allah nake fitar da aljannu, ashe, Mulkin Allah ya zo muku ke nan. 21 In ƙaƙƙarfan mutum ya yi ɗamara sosai, yana tsaron gidansa, kayan gidansa lafiya suke. 22 In kuwa wanda ya fi shi ƙarfi ya fāɗa masa, ya kuma rinjaye shi, sai ya ƙwace duk makaman da ya dogara da su, ya kuma rarraba kayansa ganima,
23 t Wanda ba nawa ba ne, gāba yake yi da ni. Wanda kuma ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.”Komawar Baƙin Aljan
(Mat 12.43-45)
24 “Baƙin aljan, in ya rabu da mutum, sai ya bi ta wurare marasa ruwa, yana neman hutawa. In ya rasa, sai ya ce, ‘Zan koma gidana da na fito.’ 25 Sa'ad da kuwa ya komo gidan ya tarar da shi shararre, ƙawatacce,
26 t Daga nan sai ya je ya ɗebo waɗansu aljannu bakwai da suka fi shi mugunta. Sai su shiga su zauna a wurin. Wannan mutum kuwa ƙarshen zamansa ya fi na fari lalacewa.”Tabbatacciyar Albarka
27 t Yana faɗar haka, sai wata mace a taron ta ɗaga murya ta ce masa, “Albarka tā tabbata ga wadda ta haife ka, wadda ka sha mamanta.”
28 t Amma ya ce, “I, amma albarka tā fi tabbata ga waɗanda suke jin Maganar Allah, suke kuma kiyaye ta.”'Yan Zamani Mugaye suna Neman Alama
(Mat 12.38-42; Mar 8.12)
29 t Da taro ya riƙa ƙaruwa a wurinsa, sai ya fara cewa, “Wannan zamani mugun zamani ne. Suna neman ganin wata alama, amma ba wata alamar da za a nuna musu sai dai ta Yunusa. 30 Wato, kamar yadda Yunusa ya zama alama ga mutanen Nineba, haka kuma, Ɗan Mutum zai zamar wa zamanin nan. 31 t A Ranar Shari'a Sarauniyar Kudu za ta tashi tare da mutanen zamanin nan ta kā da su. Don ta zo ne daga bangon duniya tă ga hikimar Sulemanu. Ga kuma wanda ya fi Sulemanu a nan.
32 t A Ranar Shari'a mutanen Nineba za su tashi tare da mutanen zamanin nan su kā da su. Don sun tuba saboda wa'azin Yunusa. To, ga kuma wanda ya fi Yunusa a nan.”Fitilar Jiki
(Mat 5.15; 6.22-23)
33 t “Ba mai kunna fitila ya ɓoye ta a rami, ko ya rufe ta da masaki. A'a, sai dai ya ɗora ta a maɗorinta, don masu shiga su ga hasken. 34 Ido shi ne fitilar jiki. In idonka lafiyayye ne, duk jikinka zai cika da haske. In kuwa idonka da lahani, sai jikinka ya cika da duhu. 35 Saboda haka, sai ka lura ko hasken da yake a gare ka duhu ne.
36 In kuwa duk jikinka ya cika da haske, ba inda ke da duhu, ai, duk sai ya haskaka gaba ɗaya, kamar yadda hasken fitila take haskaka maka.”Yesu Ya Fallashi Farisiyawa da Masanan Attaura
(Mat 23.1-36; Mar 12.38-40; Luka 20.45-47)
37 t Yesu yana magana, sai wani Bafarisiye ya kira shi cin abinci. Ya shiga cin abincin. 38 t Sai Bafarisiyen ya yi mamakin ganin yadda Yesu zai ci abinci ba da fara wanke hannu ba. 39 t Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ku Farisiyawa kam, kukan wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki cike kuke da zalunci da mugunta. 40 t Ku marasa azanci! Ashe, wanda ya yi bayan, ba shi ya yi cikin ba?
41 t Gara ku tsarkake cikin, sa'an nan kome zai tsarkaka a gare ku.
42 t “Kaitonku, Farisiyawa! Ga shi, kuna fitar da zakkar na'ana'a da karkashi, da kuma kowane ganyen miya. Amma kun ƙi kula da aikata gaskiya da ƙaunar Allah. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da waɗancan ba. 43 t Kaitonku, Farisiyawa! Ga shi, kuna son mafifitan mazaunai a majami'u, da kuma gaisuwa a kasuwa.
44 t Kaitonku! Kuna kama da kaburburan da ba a gani, waɗanda mutane suke takawa da rashin sani.”
45 t Sai wani a cikin masanan Attaura ya amsa masa ya ce, “Malam, faɗar haka fa, mu ma, ai, ka ci mutuncinmu.” 46 t Sai Yesu ya ce, “Ku kuma kaitonku, masanan Attaura! Don kuna jibga wa mutane kaya masu wuyar ɗauka, ku da kanku ko ɗan yatsa ba kwa sawa ku tallafa musu! 47 Kaitonku! Don kuna gina gubbobin annabawan da kakanninku suka kashe. 48 t Wato, ku shaidu ne a kan kun yarda da ayyukan kakanninku, ga shi, su ne fa suka kashe su, ku kuwa wai har kuka gina musu gubbobin! 49 t Shi ya sa hikimar Allah ta ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni, su kashe waɗansu,’ 50 don alhakin jinin dukan annabawa da aka zubar tun daga farkon duniya, a bi shi a kan mutanen wannan zamani, 51 t wato, tun daga jinin Habila, har ya zuwa na Zakariya, wanda aka kashe tsakanin bagaden hadaya da Wuri Mai Tsarki. Hakika, ina gaya muku, duk za a bi shi kan mutanen wannan zamani.
52 t Kaitonku, masanan Attaura! Don kun ɗauke mabuɗin ilimi, ku kanku ba ku shiga ba, kun kuma hana masu son shiga su shiga.”
53 Da ya fito daga wurin, sai malaman Attaura da Farisiyawa suka fara matsa masa ƙwarai, suna tsokanarsa ya yi maganar abubuwa da yawa, 54 t suna haƙwansa su burma shi a cikin maganarsa.
Luke 11
1 And it came to pass, as he was praying in a certain place, that when he ceased, one of his disciples said unto him, Lord, teach us to pray, even as John also taught his disciples.2 And he said unto them, When ye pray, say, Father, Hallowed be thy name. Thy kingdom come.3 Give us day by day our daily bread.4 And forgive us our sins; for we ourselves also forgive every one that is indebted to us. And bring us not into temptation.5 And he said unto them, Which of you shall have a friend, and shall go unto him at midnight, and say to him, Friend, lend me three loaves;6 for a friend of mine is come to me from a journey, and I have nothing to set before him;7 and he from within shall answer and say, Trouble me not: the door is now shut, and my children are with me in bed; I cannot rise and give thee?8 I say unto you, Though he will not rise and give him because he is his friend, yet because of his importunity he will arise and give him as many as he needeth.9 And I say unto you, Ask, and it shall be given you; seek, and ye shall find; knock, and it shall be opened unto you.10 For every one that asketh receiveth; and he that seeketh findeth; and to him that knocketh it shall be opened.11 And of which of you that is a father shall his son ask a loaf, and he give him a stone? or a fish, and he for a fish give him a serpent?12 Or if he shall ask an egg, will he give him a scorpion?13 If ye then, being evil, know how to give good gifts unto your children, how much more shall your heavenly Father give the Holy Spirit to them that ask him?14 And he was casting out a demon that was dumb. And it came to pass, when the demon was gone out, the dumb man spake; and the multitudes marvelled.15 But some of them said, By Beelzebub the prince of the demons casteth he out demons.16 And others, trying him, sought of him a sign from heaven.17 But he, knowing their thoughts, said unto them, Every kingdom divided against itself is brought to desolation; and a house divided against a house falleth.18 And if Satan also is divided against himself, how shall his kingdom stand? because ye say that I cast out demons by Beelzebub.19 And if I by Beelzebub cast out demons, by whom do your sons cast them out? therefore shall they be your judges.20 But if I by the finger of God cast out demons, then is the kingdom of God come upon you.21 When the strong man fully armed guardeth his own court, his goods are in peace:22 but when a stronger than he shall come upon him, and overcome him, he taketh from him his whole armor wherein he trusted, and divideth his spoils.23 He that is not with me is against me; and he that gathereth not with me scattereth.24 The unclean spirit when he is gone out of the man, passeth through waterless places, seeking rest, and finding none, he saith, I will turn back unto my house whence I came out.25 And when he is come, he findeth it swept and garnished.26 Then goeth he, and taketh to him seven other spirits more evil than himself; and they enter in and dwell there: and the last state of that man becometh worse than the first.27 And it came to pass, as he said these things, a certain woman out of the multitude lifted up her voice, and said unto him, Blessed is the womb that bare thee, and the breasts which thou didst suck.28 But he said, Yea rather, blessed are they that hear the word of God, and keep it.29 And when the multitudes were gathering together unto him, he began to say, This generation is an evil generation: it seeketh after a sign; and there shall no sign be given to it but the sign of Jonah.30 For even as Jonah became a sign unto the Ninevites, so shall also the Son of man be to this generation.31 The queen of the south shall rise up in the judgment with the men of this generation, and shall condemn them: for she came from the ends of the earth to hear the wisdom of Solomon; and behold, a greater than Solomon is here.32 The men of Nineveh shall stand up in the judgment with this generation, and shall condemn it: for they repented at the preaching of Jonah; and behold, a greater than Jonah is here.33 No man, when he hath lighted a lamp, putteth it in a cellar, neither under the bushel, but on the stand, that they which enter in may see the light.34 The lamp of thy body is thine eye: when thine eye is single, thy whole body also is full of light; but when it is evil, thy body also is full of darkness.35 Look therefore whether the light that is in thee be not darkness.36 If therefore thy whole body be full of light, having no part dark, it shall be wholly full of light, as when the lamp with its bright shining doth give thee light.37 Now as he spake, a Pharisee asketh him to dine with him: and he went in, and sat down to meat.38 And when the Pharisee saw it, he marvelled that he had not first bathed himself before dinner.39 And the Lord said unto him, Now ye the Pharisees cleanse the outside of the cup and of the platter; but your inward part is full of extortion and wickedness.40 Ye foolish ones, did not he that made the outside make the inside also?41 But give for alms those things which are within; and behold, all things are clean unto you.42 But woe unto you Pharisees! for ye tithe mint and rue and every herb, and pass over justice and the love of God: but these ought ye to have done, and not to leave the other undone.43 Woe unto you Pharisees! for ye love the chief seats in the synagogues, and the salutations in the marketplaces.44 Woe unto you! for ye are as the tombs which appear not, and the men that walk over them know it not.45 And one of the lawyers answering saith unto him, Teacher, in saying this thou reproachest us also.46 And he said, Woe unto you lawyers also! for ye load men with burdens grievous to be borne, and ye yourselves touch not the burdens with one of your fingers.47 Woe unto you! for ye build the tombs of the prophets, and your fathers killed them.48 So ye are witnesses and consent unto the works of your fathers: for they killed them, and ye build their tombs.49 Therefore also said the wisdom of God, I will send unto them prophets and apostles; and some of them they shall kill and persecute;50 that the blood of all the prophets, which was shed from the foundation of the world, may be required of this generation;51 from the blood of Abel unto the blood of Zachariah, who perished between the altar and the sanctuary: yea, I say unto you, it shall be required of this generation.52 Woe unto you lawyers! for ye took away the key of knowledge: ye entered not in yourselves, and them that were entering in ye hindered.53 And when he was come out from thence, the scribes and the Pharisees began to press upon him vehemently, and to provoke him to speak of many things;54 laying wait for him, to catch something out of his mouth.