LUK 12
Faɗaka a kan Makirci
1 t Sa'an nan kuwa da dubban mutane suka taru har suna tattaka juna, da farko ya yi magana da almajiransa. Ya fara cewa, “Ku yi hankali da yistin Farisiyawa, wato, makirci. 2 t Ba abin da yake rufe da ba zai tonu ba, ko kuwa abin da yake ɓoye da ba za a bayyana ba.
3 Don haka, kome kuka faɗa a asirce, za a ji shi a sarari. Abin kuma da kuka yi raɗa a loloki, za a yi shelarsa daga kan sorayeWanda za a Ji Tsoro
(Mat 10.28-31)
4 t “Ya ku masoyana, ina dai gaya muku, kada ku ji tsoron masu kisan mutum, bayan sun kashe kuwa, ba abin da za su iya yi. 5 t Amma zan gaya muku wanda za ku tsorata. Ku ji tsoron wannan da in ya kashe, yana da ikon jefawa a cikin Gidan Wuta. Hakika, ina gaya muku, shi za ku ji tsoro! 6 Ashe, ba gwara biyar ne kobo biyu ba? Ko ɗayarsu kuwa Allah bai manta da ita ba.
7 t Kai! ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye yake. Kada ku ji tsoro. Ai, martabarku ta fi ta gwara masu yawa.”Bayyana Yarda da Almasihu a gaban Mutane
(Mat 10.32-33; 12.32)
8 t “Ina kuma gaya muku, kowa ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai bayyana yarda a gare shi a gaban mala'ikun Allah. 9 t Wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, za a yi musun saninsa a gaban mala'ikun Allah. 10 t Kowa ya kushe wa Ɗan Mutum, ā gafarta masa, amma wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba. 11 t Sa'ad da suka kai ku gaban majami'u, da mahukunta da shugabanni, kada ku damu da yadda za ku mai da jawabi, ko kuwa abin da za ku faɗa,
12 t domin Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya kamata ku faɗa a lokacin.”Misali na Mai Arziki Marar Azanci
13 Sai wani a cikin taron ya ce masa, “Malam, kă ce wa ɗan'uwana ya raba gādo da ni.” 14 Amma Yesu ya ce masa, “Haba kai kuwa, wa ya sa ni in zama muku alƙali, ko in raba muku gādo?” 15 t Ya kuma ce musu, “Ku kula fa, ku yi nesa da kowane irin kwaɗayi, don yawan kaya ba shi ne rai ba.” 16 Sai ya ba su misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta yi albarka ƙwarai. 17 Sai ya ce a ransa, ‘To, ƙaƙa zan yi? Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonata.’ 18 Ya kuma ce, ‘To, ga abin da zan yi. Sai in rushe rumbunana, in gina waɗansu manya, in zuba duk amfanin gonata da kayana a ciki. 19 Zan kuma ce wa raina, “Lalle ina da kaya masu yawa a jibge, tanadin shekara da shekaru. Bari in huta, in yi ta ci, in yi ta sha, ina shagali.” ’ 20 t Amma Allah ya ce masa, ‘Kai marar azanci! A daren nan za a karɓi ranka. To, kayan da ka tanada, na wa za su zama?’
21 t Haka, wanda ya tanada wa kansa dukiya yake, ba shi kuwa da wani tanadi a gun Allah.”Damuwa da Alhini
(Mat 6.25-34)
22 Sai ya ce wa almajiransa, “Don haka, ina gaya muku, kada ku damu da batun rayuwarku game da abin da za ku ci, ko kuma jikinku, abin da za ku yi sutura. 23 Domin rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi. 24 t Ku dubi dai hankaki! Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba su da taska ko rumbu, amma kuwa Allah yana cishe su. Sau nawa martabarku ta ninka ta tsuntsaye!” 25 Wane ne a cikinku don damuwarsa zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwarsa? 26 To, in ba za ku iya yin ƙaramin abu irin wannan ba, don me kuke damuwa da sauran? 27 t Ku dubi dai furanni yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baƙi, duk da haka, ina gaya muku, ko Sulemanu ma, shi da adonsa duk, bai taɓa yin adon da ya fi na ɗayansu ba. 28 t To, ga shi Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke a raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya! 29 Ku ma kada ku damu a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada kuwa ku yi alhini. 30 t Ai, al'umman duniya suna ta neman duk irin waɗannan abubuwa, ku kuwa, Ubanku ya san kuna bukatarsu.
31 t Ku ƙwallafa rai ga al'amuran Mulkin Allah, sai a ƙara muku da waɗannan abubuwa kuma.Tara Dukiya a Sama
(Mat 6.19-21)
32 t “Ya ku ɗan ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, domin Ubanku na jin daɗin ba ku rabo a cikin Mulkin. 33 t Ku sayar da mallakarku, ku bayar taimako. Ku samar wa kanku jakar kuɗi da ba ta tsufa, wato, dukiya marar yankewa ke nan a Sama, inda ba ɓarawon da zai gabato, ba kuma asun da zai ɓāta,
34 t don kuwa inda dukiyarka take, a nan zuciyarka ma take.”Bayin da suke a Faɗake
35 “Ku yi ɗamara, fitilunku na kunne. 36 Ku dai zama kamar mutane masu jiran ubangijinsu ya dawo daga gidan biki, da zarar ya ƙwanƙwasa su buɗe masa. 37 t Albarka tā tabbata ga bayin nan waɗanda ubangijinsu da zuwansa zai same su a faɗake. Hakika, ina gaya muku, zai yi ɗamara, ya ce su zauna cin abinci, sa'an nan ya bi ta kan kowannensu yana yi masa hidima. 38 In kuwa ya zo da tsakar dare ne, ko kuwa bayan tsakar dare, ya same su a faɗake, bayin nan masu albarka ne. 39 t Amma dai ku sani, da maigida zai san lokacin da ɓarawo zai zo, da ya zauna a faɗake, ya hana a shiga masa gida.
40 t Ku ma sai ku zauna a kan shiri, domin a lokacin da ba ku zata ba Ɗan Mutum zai zo.”Amintaccen Bawa ko Marar Aminci
(Mat 24.45-51)
41 Sai Bitrus ya ce, “Ya Ubangiji, mu ne kake faɗa wa wannan misali, ko kuwa na kowa da kowa ne?” 42 t Ubangiji ya ce, “Wane ne amintaccen wakilin nan mai hikima, da ubangidansa zai ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari? 43 Albarka tā tabbata ga bawan da, in ubangidansa ya dawo, zai samu yana yin haka. 44 Hakika, ina gaya muku, sai ya ɗora shi a kan dukan mallaka tasa. 45 In kuwa bawan nan ya ce a ransa, ‘Ubangijina ya jinkirta zuwansa,’ sa'an nan ya soma dūkan barori, maza da mata, ya shiga ci da sha har yana buguwa, 46 t ai, ubangijin wannan bawa zai zo a ranar da bai zata ba, a lokacin kuma da bai sani ba, yă farfasa masa jiki da bulala, ya ba shi rabonsa tare da marasa riƙon amana. 47 t Bawan nan kuma wanda ya san nufin ubangijinsa, bai yi shiri ba, bai kuma bi nufinsa ba, za a yi masa matsanancin dūka,
48 t Wanda kuwa bai san nufin ubangijinsa ba, ya kuma yi abin da ya isa dūka, za a doke shi kaɗan. Duk wanda aka ba abu mai yawa, a gunsa za a tsammaci abu mai yawa. Wanda kuma aka danƙa wa abu mai yawa, abu mafi yawa za a nema a gare shi.”Yesu Ya Kawo Rabuwa
(Mat 10.34-36)
49 “Wuta ce na zo in zuba wa duniya. Sona fa? A ce ta huru! 50 t Ina da baftismar da za a yi mini, na kuwa ɗokanta ƙwarai har a yi mini ita! 51 Kuna tsammani na zo ne in kawo salama a duniya? A'a, ina gaya muku, sai dai rabuwa. 52 Nan gaba, a gida guda mutum biyar za su kasu biyu, uku na gāba da biyu, biyu kuma na gāba da uku.
53 t Ta haka, za su rabu. Uba yana gāba da ɗansa, ɗan kuma yana gāba da ubansa, uwa tana gāba da 'ya tata, 'yar kuma tana gāba da uwa tata, suruka tana gāba da matar ɗanta, matar ɗan kuma tana gāba da suruka tata.”Gane Yanayin Lokatai
(Mat 16.1-4; Mar 8.11-13)
54 t Ya kuma ce wa taron, “In kun ga girgije yana tasowa daga yamma, nan da nan kukan ce, ‘Za a yi ruwa.’ Sai kuwa a yi. 55 In kuwa kun ga iskar kudu tana busowa, kukan ce, ‘Za a yi matsanancin zafi.’ Sai kuwa a yi.
56 t Munafukai! Kuna iya gane yanayin ƙasa da na sararin sama, amma me ya sa ba ku iya gane alamun zamanin ba?”Yi Jiyayya da Mai Ƙararka
(Mat 5.25-26)
57 “Me ya sa ku da kanku ma ba kwa iya rarrabewa da abin da yake daidai? 58 t Misali, in kuna tafiya zuwa gaban shari'a da mai ƙararku, sai ku yi ƙoƙari ku yi jiyayya da shi tun a hanya, don kada ya ja ku zuwa gaban alƙali, alƙali kuma ya miƙa wa ɗan doka, ɗan doka kuma ya jefa ku a kurkuku. 59 t Ina gaya muku, lalle ba za ku fita ba, sai kun biya duka, ba sauran ko anini.”
Luke 12
1 In the mean time, when the many thousands of the multitude were gathered together, insomuch that they trod one upon another, he began to say unto his disciples first of all, Beware ye of the leaven of the Pharisees, which is hypocrisy.2 But there is nothing covered up, that shall not be revealed; and hid, that shall not be known.3 Wherefore whatsoever ye have said in the darkness shall be heard in the light; and what ye have spoken in the ear in the inner chambers shall be proclaimed upon the housetops.4 And I say unto you my friends, Be not afraid of them that kill the body, and after that have no more that they can do.5 But I will warn you whom ye shall fear: Fear him, who after he hath killed hath power to cast into hell; yea, I say unto you, Fear him.6 Are not five sparrows sold for two pence? and not one of them is forgotten in the sight of God.7 But the very hairs of your head are all numbered. Fear not: ye are of more value than many sparrows.8 And I say unto you, Every one who shall confess me before men, him shall the Son of man also confess before the angels of God:9 but he that denieth me in the presence of men shall be denied in the presence of the angels of God.10 And every one who shall speak a word against the Son of man, it shall be forgiven him: but unto him that blasphemeth against the Holy Spirit it shall not be forgiven.11 And when they bring you before the synagogues, and the rulers, and the authorities, be not anxious how or what ye shall answer, or what ye shall say:12 for the Holy Spirit shall teach you in that very hour what ye ought to say.13 And one out of the multitude said unto him, Teacher, bid my brother divide the inheritance with me.14 But he said unto him, Man, who made me a judge or a divider over you?15 And he said unto them, Take heed, and keep yourselves from all covetousness: for a man’s life consisteth not in the abundance of the things which he possesseth.16 And he spake a parable unto them, saying, The ground of a certain rich man brought forth plentifully:17 and he reasoned within himself, saying, What shall I do, because I have not where to bestow my fruits?18 And he said, This will I do: I will pull down my barns, and build greater; and there will I bestow all my grain and my goods.19 And I will say to my soul, Soul, thou hast much goods laid up for many years; take thine ease, eat, drink, be merry.20 But God said unto him, Thou foolish one, this night is thy soul required of thee; and the things which thou hast prepared, whose shall they be?21 So is he that layeth up treasure for himself, and is not rich toward God.22 And he said unto his disciples, Therefore I say unto you, Be not anxious for your life, what ye shall eat; nor yet for your body, what ye shall put on.23 For the life is more than the food, and the body than the raiment.24 Consider the ravens, that they sow not, neither reap; which have no store-chamber nor barn; and God feedeth them: of how much more value are ye than the birds!25 And which of you by being anxious can add a cubit unto the measure of his life?26 If then ye are not able to do even that which is least, why are ye anxious concerning the rest?27 Consider the lilies, how they grow: they toil not, neither do they spin; yet I say unto you, Even Solomon in all his glory was not arrayed like one of these.28 But if God doth so clothe the grass in the field, which to-day is, and to-morrow is cast into the oven; how much more shall he clothe you, O ye of little faith?29 And seek not ye what ye shall eat, and what ye shall drink, neither be ye of doubtful mind.30 For all these things do the nations of the world seek after: but your Father knoweth that ye have need of these things.31 Yet seek ye his kingdom, and these things shall be added unto you.32 Fear not, little flock; for it is your Father’s good pleasure to give you the kingdom.33 Sell that which ye have, and give alms; make for yourselves purses which wax not old, a treasure in the heavens that faileth not, where no thief draweth near, neither moth destroyeth.34 For where your treasure is, there will your heart be also.35 Let your loins be girded about, and your lamps burning;36 and be ye yourselves like unto men looking for their lord, when he shall return from the marriage feast; that, when he cometh and knocketh, they may straightway open unto him.37 Blessed are those servants, whom the lord when he cometh shall find watching: verily I say unto you, that he shall gird himself, and make them sit down to meat, and shall come and serve them.38 And if he shall come in the second watch, and if in the third, and find them so blessed are those servants.39 But know this, that if the master of the house had known in what hour the thief was coming, he would have watched, and not have left his house to be broken through.40 Be ye also ready: for in an hour that ye think not the Son of man cometh.41 And Peter said, Lord, speakest thou this parable unto us, or even unto all?42 And the Lord said, Who then is the faithful and wise steward, whom his lord shall set over his household, to give them their portion of food in due season?43 Blessed is that servant, whom his lord when he cometh shall find so doing.44 Of a truth I say unto you, that he will set him over all that he hath.45 But if that servant shall say in his heart, My lord delayeth his coming; and shall begin to beat the menservants and the maidservants, and to eat and drink, and to be drunken;46 the lord of that servant shall come in a day when he expecteth not, and in an hour when he knoweth not, and shall cut him asunder, and appoint his portion with the unfaithful.47 And that servant, who knew his lord’s will, and made not ready, nor did according to his will, shall be beaten with many stripes;48 but he that knew not, and did things worthy of stripes, shall be beaten with few stripes. And to whomsoever much is given, of him shall much be required: and to whom they commit much, of him will they ask the more.49 I came to cast fire upon the earth; and what do I desire, if it is already kindled?50 But I have a baptism to be baptized with; and how am I straitened till it be accomplished!51 Think ye that I am come to give peace in the earth? I tell you, Nay; but rather division:52 for there shall be from henceforth five in one house divided, three against two, and two against three.53 They shall be divided, father against son, and son against father; mother against daughter, and daughter against her mother; mother in law against her daughter in law, and daughter in law against her mother in law.54 And he said to the multitudes also, When ye see a cloud rising in the west, straightway ye say, There cometh a shower; and so it cometh to pass.55 And when ye see a south wind blowing, ye say, There will be a scorching heat; and it cometh to pass.56 Ye hypocrites, ye know how to interpret the face of the earth and the heaven; but how is it that ye know not how to interpret this time?57 And why even of yourselves judge ye not what is right?58 For as thou art going with thine adversary before the magistrate, on the way give diligence to be quit of him; lest haply he drag thee unto the judge, and the judge shall deliver thee to the officer, and the officer shall cast thee into prison.59 I say unto thee, Thou shalt by no means come out thence, till thou have paid the very last mite.