LUK 13
Tuba ko Halaka
1 t Nan take waɗansu da suke a wurin suka ba shi labarin Galilawan da Bilatus ya sa aka kashe, har jininsu ya gauraya da na yankan da suka yi na hadaya. 2 t Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Kuna tsammani waɗannan Galilawa sun fi duk sauran Galilawa zunubi ne, don sun sha wannan azaba? 3 Ina gaya muku ba haka ba ne! In kuwa ba ku tuba ba, duk za ku halaka kamarsu. 4 t Ko kuwa goma sha takwas ɗin nan da hasumiya ta faɗo a kansu, a Siluwam, ta kashe su, kuna tsammani sun fi duk sauran mutanen Urushalima laifi ne?
5 t Ina gaya muku ba haka ba ne! In kuwa ba ku tuba ba, duk za ku hallaka kamarsu.”Misali na Ɓaure Marar 'Ya'ya
6 t Sai ya ba su misalin nan ya ce, “Wani mutum yana da ɓaure a garkar inabinsa. Sai ya zo neman 'ya'ya, amma bai samu ba. 7 t Sai ya ce wa mai kula da garkar, ‘Ka ga, yau shekara uku ke nan nake zuwa neman 'ya'yan wannan ɓaure, amma ba na samu. A sare shi. Ƙaƙa zai tsare wuri a banza?’ 8 Sai ya amsa masa ya ce, ‘Ubangijina, bar shi dai bana ma, in yi masa kaftu, in zuba masa taki.
9 In ya yi 'ya'ya, to, in kuwa bai yi ba, sai a sare.’ ”Warkar da Tanƙwararriyar Mace a Ran Asabar
10 t Wata rana yana koyarwa a wata majami'a ran Asabar, 11 t sai ga wata mace wadda inna ta shanye tun shekara goma sha takwas, duk ta tanƙware, ko kaɗan ba ta iya miƙewa. 12 Da Yesu ya gan ta, sai ya kira ta ya ce mata, “Uwargida, an raba ki da rashin lafiyarki!” 13 t Sai ya ɗora mata hannu, nan take ta miƙe, ta kuma ɗaukaka Allah. 14 t Amma shugaban majami'a ya ji haushi, don Yesu ya warkar ran Asabar. Sai ya ce wa jama'a, “Akwai ranaku har shida da ya kamata a yi aiki. Ku zo mana a ranakun nan a warkar da ku, ba ran Asabar ba.” 15 t Amma Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Munafukai! Ashe, kowannenku ba ya kwance takarkarinsa ko jakinsa a turke, ya kai shi banruwa ran Asabar? 16 t Ashe, bai kamata matar nan 'yar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya ɗaure, yau shekara goma sha takwas, a kwance ta daga wannan ƙuƙumi a ran Asabar ba?”
17 t Da ya faɗi haka, sai duk abokan adawarsa suka kunyata, duk taron kuwa suka yi ta farin ciki da abubuwan al'ajabi da yake yi.Misali na Ƙwayar Mastad
(Mat 13.31-32; Mar 4.30-32)
18 t Sai Yesu ya ce, “Da me Mulkin Allah yake kama? Da me kuma zan kwatanta shi?
19 t Kamar ƙwayar mastad yake, wadda wani mutum ya je ya shuka a lambunsa, ta kuma girma ta zama itace, har tsuntsaye suka yi sheƙarsu a rassanta.”Misali na Yisti
(Mat 13.33)
20 Ya sāke cewa, “Da me zan kwatanta Mulkin Allah?
21 t Kamar yisti yake wanda wata mace ta ɗauka ta cuɗa da mudu uku na garin alkama, har duk garin ya gama da yistin.”Ƙunƙuntar Ƙofa
(Mat 7.13-14, 21-23)
22 t Sai ya ɗauki hanyarsa ta zuwa birane da ƙauyuka, yana koyarwa, yana dosar Urushalima. 23 Sai wani ya ce masa, “Ya Ubangiji, waɗanda za su sami ceto kam, kaɗan ne?” Sai ya ce musu, 24 t “Ku yi famar shiga ta ƙunƙuntar ƙofa. Don ina gaya muku, mutane da yawa za su nemi shiga, amma ba su iya ba. 25 t In dai maigida ya riga ya tashi ya rufe ƙofa, kun kuma fara tsayawa daga waje, kuna ƙwanƙwasa ƙofar, kuna cewa, ‘Ya Ubangiji, buɗe mana,’ sai ya amsa muku ya ce, ‘Ku kam, ban san daga inda kuke ba.’ 26 Sa'an nan za ku fara cewa, ‘Ai, mun ci mun sha a gabanka, har ka koyar a kan titi-titinmu.’ 27 t Shi kuwa sai ya ce, ‘Ina dai gaya muku, ku kam, ban san daga inda kuke ba. Ku tafi daga wurina, dukanku ku masu aikata mugunta!’ 28 t Sa'ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, da dukan annabawa a Mulkin Allah, ku kuwa ana korarku, a nan ne za ku yi kuka da cizon baki. 29 t Za a zo daga gabas da yamma, kudu da arewa, a zauna cin abinci a Mulkin Allah.
30 t Ga shi fa, waɗansu da suke na ƙarshe za su zama na farko, waɗansu kuwa da suke na farko za su koma na ƙarshe.”Yesu Ya Ji Juyayin Urushalima
(Mat 23.37-39)
31 t Nan take waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce masa, “Ai, sai ka tashi, ka fita daga nan, gama Hirudus yana son kashe ka.” 32 t Sai ya ce musu, “Ku tafi ku gaya wa dilan nan cewa, ‘Ka ga, yau ina fitar da aljannu, ina warkarwa, gobe ma haka, a rana ta uku kuwa zan gama aikina.
33 t Duk da haka, lalle ne in ci gaba da tafiyata yau da gobe, da kuma jibi, don kuwa bai dace a kashe annabi ba, in ba a Urushalima ba.’
34 t “Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko gare ku! Sau nawa ne ina so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta a cikin fikafikanta, amma kun ƙi! 35 t Ga shi, an bar muku gidanku a yashe! ina kuwa gaya muku, ba za ku ƙara ganina ba, sai ran da kuka ce, ‘Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.’ ”
Luke 13
1 Now there were some present at that very season who told him of the Galilaeans, whose blood Pilate had mingled with their sacrifices.2 And he answered and said unto them, Think ye that these Galilaeans were sinners above all the Galilaeans, because they have suffered these things?3 I tell you, Nay: but, except ye repent, ye shall all in like manner perish.4 Or those eighteen, upon whom the tower in Siloam fell, and killed them, think ye that they were offenders above all the men that dwell in Jerusalem?5 I tell you, Nay: but, except ye repent, ye shall all likewise perish.6 And he spake this parable; A certain man had a fig tree planted in his vineyard; and he came seeking fruit thereon, and found none.7 And he said unto the vinedresser, Behold, these three years I come seeking fruit on this fig tree, and find none: cut it down; why doth it also cumber the ground?8 And he answering saith unto him, Lord, let it alone this year also, till I shall dig about it, and dung it:9 and if it bear fruit thenceforth, well; but if not, thou shalt cut it down.10 And he was teaching in one of the synagogues on the sabbath day.11 And behold, a woman that had a spirit of infirmity eighteen years; and she was bowed together, and could in no wise lift herself up.12 And when Jesus saw her, he called her, and said to her, Woman, thou art loosed from thine infirmity.13 And he laid his hands upon her: and immediately she was made straight, and glorified God.14 And the ruler of the synagogue, being moved with indignation because Jesus had healed on the sabbath, answered and said to the multitude, There are six days in which men ought to work: in them therefore come and be healed, and not on the day of the sabbath.15 But the Lord answered him, and said, Ye hypocrites, doth not each one of you on the sabbath loose his ox or his ass from the stall, and lead him away to watering?16 And ought not this woman, being a daughter of Abraham, whom Satan had bound, lo, these eighteen years, to have been loosed from this bond on the day of the sabbath?17 And as he said these things, all his adversaries were put to shame: and all the multitude rejoiced for all the glorious things that were done by him.18 He said therefore, Unto what is the kingdom of God like? and whereunto shall I liken it?19 It is like unto a grain of mustard seed, which a man took, and cast into his own garden; and it grew, and became a tree; and the birds of the heaven lodged in the branches thereof.20 And again he said, Whereunto shall I liken the kingdom of God?21 It is like unto leaven, which a woman took and hid in three measures of meal, till it was all leavened.22 And he went on his way through cities and villages, teaching, and journeying on unto Jerusalem.23 And one said unto him, Lord, are they few that are saved? And he said unto them,24 Strive to enter in by the narrow door: for many, I say unto you, shall seek to enter in, and shall not be able.25 When once the master of the house is risen up, and hath shut to the door, and ye begin to stand without, and to knock at the door, saying, Lord, open to us; and he shall answer and say to you, I know you not whence ye are;26 then shall ye begin to say, We did eat and drink in thy presence, and thou didst teach in our streets;27 and he shall say, I tell you, I know not whence ye are; depart from me, all ye workers of iniquity.28 There shall be the weeping and the gnashing of teeth, when ye shall see Abraham, and Isaac, and Jacob, and all the prophets, in the kingdom of God, and yourselves cast forth without.29 And they shall come from the east and west, and from the north and south, and shall sit down in the kingdom of God.30 And behold, there are last who shall be first, and there are first who shall be last.31 In that very hour there came certain Pharisees, saying to him, Get thee out, and go hence: for Herod would fain kill thee.32 And he said unto them, Go and say to that fox, Behold, I cast out demons and perform cures to-day and to-morrow, and the third day I am perfected.33 Nevertheless I must go on my way to-day and to-morrow and the day following: for it cannot be that a prophet perish out of Jerusalem.34 O Jerusalem, Jerusalem, that killeth the prophets, and stoneth them that are sent unto her! how often would I have gathered thy children together, even as a hen gathereth her own brood under her wings, and ye would not!35 Behold, your house is left unto you desolate: and I say unto you, Ye shall not see me, until ye shall say, Blessed is he that cometh in the name of the Lord.