LUK 14
Warkar da Mai Ciwon Fara
1 t Wata ranar Asabar, ya shiga gidan wani shugaba Farisiyawa garin cin abinci, mutane kuwa suna haƙwansa. 2 Sai ga wani mai ciwon fara a gabansa. 3 t Yesu ya amsa ya ce wa masanan Attaura da Farisiyawa, “Ya halatta a warkar ran Asabar ko kuwa?” 4 Sai suka yi shiru, Yesu kuwa ya riƙe shi, ya warkar da shi, ya kuma sallame shi. 5 t Sa'an nan ya ce musu, “Misali, wane ne a cikinku in yana da jaki ko takarkari ya faɗa a rijiya ran Asabar, ba zai fitar da shi nan da nan ba?”
6 Sai suka kasa ba da amsar waɗannan abubuwa.Aya ga Waɗanda aka Gayyato Biki da Mai Gayyar
7 t To, ganin yadda waɗanda aka gayyato sun zaɓi mazaunan alfarma, sai ya ba su misali ya ce, 8 “In an gayyace ka zuwa biki, kada ka zauna a mazaunin alfarma, kada ya zamana an gayyato wani wanda ya fi ka daraja, 9 wanda ya gayyato ku duka biyu kuma yă zo ya ce maka, ‘Ba mutumin nan wuri.’ Sa'an nan a kunyace ka koma mazauni mafi ƙasƙanci. 10 Amma in an gayyace ka biki, sai ka je ka zauna a wuri mafi ƙasƙanci, don in mai gayyar ya zo, sai ya ce maka, ‘Aboki, hawo nan mana.’ Za ka sami girma ke nan a gaban dukan waɗanda kuke zaune tare.
11 t Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.”
12 Ya kuma ce da mai gayyar, “In za ka kira mutum cin abinci ko biki, kada ka riƙa kiran abokanka kawai, ko 'yan'uwanka, ko danginka ko maƙwabtanka masu arziki, kada su ma su gayyace ka, su sāka maka. 13 t Amma in za ka kira biki, sai ka gayyayo gajiyayyu, da musakai, da guragu, da makafi,
14 t za ka kuwa sami albarka, da yake ba su da hanyar sāka maka. Sai kuwa a sāka maka ranar tashin masu adalci.”Misali na Babban Biki
15 t Da jin haka, sai ɗaya daga cikin abokan cinsa ya ce masa, “Albarka tā tabbata ga wanda zai ci abinci a Mulkin Allah.” 16 Amma ya ce masa, “Wani mutum ne ya shirya babban biki ya gayyaci mutane da yawa. 17 Da lokacin biki ya yi, sai ya aiki bawansa yă ce wa waɗanda aka gayyata, ‘Ku zo, duk an shirya kome,’ 18 Sai dukansu baki ɗaya suka fara kawo hanzari. Na farko ya ce masa, ‘Na sayi gona, lalle ne in je in gano ta. Ina roƙonka ka ɗauke mini,’ 19 Sai wani ya ce, ‘Na sayi shanun noma guda goma, za ni in gwada su. Ina roƙonka ka ɗauke mini.’ 20 Wani kuma ya ce, ‘Na yi aure, don haka ba zan iya zuwa ba.’ 21 t Bawan ya dawo ya ba ubangijinsa labari. Sai maigidan ya yi fushi, ya ce wa bawansa, ‘Fita maza, ka bi titi-titin birni da kwararo-kwararo, ka ɗebo gajiyayyu, da musakai, da makafi, da guragu.’ 22 Sai bawan ya ce, ‘Ya ubangiji, abin da ka umarta duk an gama, amma har yanzu da sauran wuri.’ 23 Sai ubangijin biki ya ce wa bawan, ‘Fita, ka bi gwadabe-gwadabe da hanyoyin karkara, ka rinjayi mutane su shigo, don a cika gidana.
24 t Ina gaya muku, ba ko ɗaya daga cikin mutanen da na gayyata a dā da zai ɗanɗana bikina ba.’ ”Wuyar Zama Almajiri
25 To, taro masu yawan gaske binsa. Sai ya juya ya ce musu, 26 t “Duk mai zuwa wurina, in bai fi ƙaunata da ubansa, da uwa tasa, da mata tasa, da 'ya'yansa, da 'yan'uwansa mata da maza, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba. 27 t Duk wanda bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba. 28 Misali, in wani daga cikinku yana son gina soron bene, da fari ba sai ya zauna ya yi lissafin abin da zai kashe ba, ya ga ko yana da isassun kuɗi da za su ƙare aikin? 29 Kada ya zamana bayan da ya sa harsashin ginin, yă kasa gamawa, har duk waɗanda suka gani, su fara yi masa ba'a,
30 su riƙa cewa, ‘A! Ka ga mutumin nan ya fara gini, amma ya kasa gamawa!’
31 “Ko kuwa wane sarki ne, in za shi yaƙi da wani sarki, da fari ba ya zauna ya yi shawara, ya ga ko shi mai mutum dubu goma zai iya karawa da mai dubu ashirin ba? 32 In kuwa ba zai iya ba, to, tun wancan yana nesa, sai ya aiki jakadu, su tambayo sharuɗan amana.
33 t Haka ma, kowannenku in bai saki duk abin da ya mallaka ba, ba zai iya zama almajirina ba.”Sānannen Gishiri
(Mat 5.13; Mar 9.50)
34 t “Gishiri abu ne mai kyau, amma in gishiri ya sāne, da me za a daɗaɗa shi? 35 t Ba shi da wani amfani a gona, ko a taki, sai dai a zubar kawai. Duk mai kunnen ji, ya ji.”
Luke 14
1 And it came to pass, when he went into the house of one of the rulers of the Pharisees on a sabbath to eat bread, that they were watching him.2 And behold, there was before him a certain man that had the dropsy.3 And Jesus answering spake unto the lawyers and Pharisees, saying, Is it lawful to heal on the sabbath, or not?4 But they held their peace. And he took him, and healed him, and let him go.5 And he said unto them, Which of you shall have an ass or an ox fallen into a well, and will not straightway draw him up on a sabbath day?6 And they could not answer again unto these things.7 And he spake a parable unto those that were bidden, when he marked how they chose out the chief seats; saying unto them,8 When thou art bidden of any man to a marriage feast, sit not down in the chief seat; lest haply a more honorable man than thou be bidden of him,9 and he that bade thee and him shall come and say to thee, Give this man place; and then thou shalt begin with shame to take the lowest place.10 But when thou art bidden, go and sit down in the lowest place; that when he that hath bidden thee cometh, he may say to thee, Friend, go up higher: then shalt thou have glory in the presence of all that sit at meat with thee.11 For everyone that exalteth himself shall be humbled; and he that humbleth himself shall be exalted.12 And he said to him also that had bidden him, When thou makest a dinner or a supper, call not thy friends, nor thy brethren, nor thy kinsmen, nor rich neighbors; lest haply they also bid thee again, and a recompense be made thee.13 But when thou makest a feast, bid the poor, the maimed, the lame, the blind:14 and thou shalt be blessed; because they have not wherewith to recompense thee: for thou shalt be recompensed in the resurrection of the just.15 And when one of them that sat at meat with him heard these things, he said unto him, Blessed is he that shall eat bread in the kingdom of God.16 But he said unto him, A certain man made a great supper; and he bade many:17 and he sent forth his servant at supper time to say to them that were bidden, Come; for all things are now ready.18 And they all with one consent began to make excuse. The first said unto him, I have bought a field, and I must needs go out and see it; I pray thee have me excused.19 And another said, I have bought five yoke of oxen, and I go to prove them; I pray thee have me excused.20 And another said, I have married a wife, and therefore I cannot come.21 And the servant came, and told his lord these things. Then the master of the house being angry said to his servant, Go out quickly into the streets and lanes of the city, and bring in hither the poor and maimed and blind and lame.22 And the servant said, Lord, what thou didst command is done, and yet there is room.23 And the lord said unto the servant, Go out into the highways and hedges, and constrain them to come in, that my house may be filled.24 For I say unto you, that none of those men that were bidden shall taste of my supper.25 Now there went with him great multitudes: and he turned, and said unto them,26 If any man cometh unto me, and hateth not his own father, and mother, and wife, and children, and brethren, and sisters, yea, and his own life also, he cannot be my disciple.27 Whosoever doth not bear his own cross, and come after me, cannot be my disciple.28 For which of you, desiring to build a tower, doth not first sit down and count the cost, whether he have wherewith to complete it?29 Lest haply, when he hath laid a foundation, and is not able to finish, all that behold begin to mock him,30 saying, This man began to build, and was not able to finish.31 Or what king, as he goeth to encounter another king in war, will not sit down first and take counsel whether he is able with ten thousand to meet him that cometh against him with twenty thousand?32 Or else, while the other is yet a great way off, he sendeth an ambassage, and asketh conditions of peace.33 So therefore whosoever he be of you that renounceth not all that he hath, he cannot be my disciple.34 Salt therefore is good: but if even the salt have lost its savor, wherewith shall it be seasoned?35 It is fit neither for the land nor for the dunghill: men cast it out. He that hath ears to hear, let him hear.