previous next

LUK 15

Misali na Ɓatacciyar Tunkiya

(Mat 18.12-14)

1  t To, sai duk masu karɓar haraji da masu zunubi suka yi ta matsowa wurinsa su saurare shi.

2 t Sai Farisiyawa da malaman Attaura suka riƙa gunaguni suna cewa, “Haba! Wannan mutum yana karɓar masu zunubi, har ma tare suke cin abinci!”
3  t Sai ya ba su wannan misali ya ce. 4 t “In waninku yana da tumaki ɗari, ɗayarsu ta ɓace, to, ba sai ya bar tasa'in da taran nan a makiyaya, ya bi sawun wadda ta ɓata, har ya same ta ba? 5 In kuwa ya same ta, sai ya saɓo ta a kafaɗa, yana farin ciki. 6 t In ya dawo gida, sai ya tara abokansa da maƙwabta ya ce musu, ‘Ku taya ni farin ciki, don na samo tunkiyata da ta ɓata.’

7 t Ina dai gaya muku, haka kuma, za a yi farin ciki a Sama, a kan mai zunubi guda da ya tuba, fiye da kan adalai tasa'in da tara waɗanda ba su bukatar tuba.”

Misali na Ɓataccen Kuɗi


8 “Ko kuwa wace mace ce, in tana da kuɗi azurfa guda goma, in ta yar da ɗaya, ba sai ta kunna fitila ta share gidan, ta yi ta nacin nemansa, har ta same shi ba? 9 t In kuwa ta same shi, sai ta tara ƙawayenta da maƙwabta mata, ta ce musu, ‘Ku taya ni farin ciki, don na sami kuɗin nan da na yar.’

10 t Haka nake gaya muku, abin farin ciki ne ga mala'ikun Allah in mai zunubi guda ya tuba.”

Misali na Ɓataccen Ɗa


11  t Ya kuma ce, “An yi wani mutum mai 'ya'ya biyu maza. 12 t Sai ƙaramin ya ce wa ubansa, ‘Baba, ba ni rabona na gādo.’ Sai uban ya raba musu dukiyarsa. 13 t Bayan 'yan kwanaki kaɗan sai ƙaramin ya tattara duk mallakarsa, ya kama hanya zuwa ƙasa mai nisa. A can ya fallasar da kayansa a wajen masha'a. 14 Da ya ɓad da kome kakat, aka yi babbar yunwa a ƙasar, sai ya shiga fatara. 15 t Ya je ya rāɓu da wani ɗan ƙasar, shi kuwa ya tura shi makiyayar kiwon alade. 16 Har ma ya so ya cika cikinsa da kwasfar da aladu suke ci, amma ba wanda ya ba shi wani abu 17 Amma da ya tara hankalinsa sai ya ce, ‘Kaitona! Nawa ne daga cikin barorin ubana da suke da abinci, da yake kamar ƙasa a gare su! Ga ni a nan kuwa, yunwa tana kisana! 18 t Zan tashi, in tafi gun ubana, in ce masa, “Baba, na yi wa Mai Sama zunubi, na kuma saɓa maka. 19 Ban ma cancanci a ƙara kirana ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin barorinka.” ’ 20 t Sai ya tashi, ya taho wurin ubansa. Amma tun yana daga nesa, sai ubansa ya hango shi, tausayi ya kama shi, ya yiwo gudu, ya rungume shi, ya yi ta sumbatarsa. 21 t Sai kuma ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa Mai Sama zunubi, na kuma saɓa maka. Ban ma cancanci a ƙara kirana ɗanka ba.’ 22 t Amma uban ya ce wa bayinsa, ‘Maza ku kawo riga mafi kyau, ku sa masa. Ku sa masa zobe da takalma, 23 a kuma kawo kiwataccen ɗan maraƙin nan, a yanka, mu ci, mu yi murna.

24 t Don ɗan nan nawa dā ya mutu ne, amma a yanzu ya komo, dā ya ɓata, amma a yanzu an same shi.’ Sai suka yi ta farin ciki.
25 “A sa'an nan kuwa, babban ɗansa yana gona. Yana dawowa, ya yi kusa da gida ke nan, sai ya ji ana kaɗe-kaɗe da raye-raye. 26 Sai ya kira wani baran gidan, ya tambayi dalilin wannan abu. 27 Shi kuwa ya ce masa, ‘Ai, ɗan'uwanka ne ya dawo, tsohonku ya yanka kiwataccen ɗan maraƙin nan saboda ya sadu da shi lafiya ƙalau.’ 28 t Amma wan ya yi fushi, ya ƙi shiga. Ubansa kuwa ya fito, ya yi ta rarrashinsa. 29 Amma ya amsa wa ubansa ya ce, ‘Dubi yawan shekarun nan da na bauta maka. Ban taɓa ta da umarninka ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan taure ba, da za mu yi shagali tare da abokaina. 30 t Amma da ɗan nan naka ya zo, wanda ya fallasar da dukiyarka a kan karuwai, ga shi, ka yanka masa kiwataccen ɗan maraƙin nan!’ 31 Sai uban ya ce masa, ‘Ya ɗana, ai, kullum kana tare da ni, duk abin da yake nawa naka ne. 32 t Ai kuwa, daidai ne a yi ta murna da farin ciki, don ɗan'uwan nan naka dā ya mutu, a yanzu ya komo, dā ya ɓata, amma an same shi.’ ”

Luke 15

1 Now all the publicans and sinners were drawing near unto him to hear him.2 And both the Pharisees and the scribes murmured, saying, This man receiveth sinners, and eateth with them.3 And he spake unto them this parable, saying,4 What man of you, having a hundred sheep, and having lost one of them, doth not leave the ninety and nine in the wilderness, and go after that which is lost, until he find it?5 And when he hath found it, he layeth it on his shoulders, rejoicing.6 And when he cometh home, he calleth together his friends and his neighbors, saying unto them, Rejoice with me, for I have found my sheep which was lost.7 I say unto you, that even so there shall be joy in heaven over one sinner that repenteth, more than over ninety and nine righteous persons, who need no repentance.8 Or what woman having ten pieces of silver, if she lose one piece, doth not light a lamp, and sweep the house, and seek diligently until she find it?9 And when she hath found it, she calleth together her friends and neighbors, saying, Rejoice with me, for I have found the piece which I had lost.10 Even so, I say unto you, there is joy in the presence of the angels of God over one sinner that repenteth.11 And he said, A certain man had two sons:12 and the younger of them said to his father, Father, give me the portion of thy substance that falleth to me. And he divided unto them his living.13 And not many days after, the younger son gathered all together and took his journey into a far country; and there he wasted his substance with riotous living.14 And when he had spent all, there arose a mighty famine in that country; and he began to be in want.15 And he went and joined himself to one of the citizens of that country; and he sent him into his fields to feed swine.16 And he would fain have filled his belly with the husks that the swine did eat: and no man gave unto him.17 But when he came to himself he said, How many hired servants of my father’s have bread enough and to spare, and I perish here with hunger!18 I will arise and go to my father, and will say unto him, Father, I have sinned against heaven, and in thy sight:19 I am no more worthy to be called your son: make me as one of thy hired servants.20 And he arose, and came to his father. But while he was yet afar off, his father saw him, and was moved with compassion, and ran, and fell on his neck, and kissed him.21 And the son said unto him, Father, I have sinned against heaven, and in thy sight: I am no more worthy to be called thy son.22 But the father said to his servants, Bring forth quickly the best robe, and put it on him; and put a ring on his hand, and shoes on his feet:23 and bring the fatted calf, and kill it, and let us eat, and make merry:24 for this my son was dead, and is alive again; he was lost, and is found. And they began to be merry.25 Now his elder son was in the field: and as he came and drew nigh to the house, he heard music and dancing.26 And he called to him one of the servants, and inquired what these things might be.27 And he said unto him, Thy brother is come; and thy father hath killed the fatted calf, because he hath received him safe and sound.28 But he was angry, and would not go in: and his father came out, and entreated him.29 But he answered and said to his father, Lo, these many years do I serve thee, and I never transgressed a commandment of thine; and yet thou never gavest me a kid, that I might make merry with my friends:30 but when this thy son came, who hath devoured thy living with harlots, thou killedst for him the fatted calf.31 And he said unto him, Son, thou art ever with me, and all that is mine is thine.32 But it was meet to make merry and be glad: for this thy brother was dead, and is alive again; and was lost, and is found.