LUK 16
Misali na Wakili Marar Gaskiya
1 t Ya kuma ce wa almajiransa, “An yi wani mai arziki da yake da wakili. Sai aka sari wakilin a wurinsa a kan yana fallasar masa da dukiya. 2 Sai ya kira shi ya ce masa, ‘Labarin me nake ji naka? Kawo lissafin wakilcinka, don ba sauran ka zama wakilina.’ 3 Sai wakilin ya ce a ransa, ‘Ƙaƙa zan yi, da yake maigida zai karɓe wakilci daga hannuna? Ga shi, ba ni da ƙarfin noma, in yi roƙo kuwa, ina jin kunya. 4 Yauwa! Na san abin da zan yi, don in an fisshe ni daga wakilcin, mutane su karɓe ni a gidajensu.’ 5 Sai ya kira mabartan maigidansa da ɗaya ɗaya, ya ce wa na farko, ‘Nawa maigida yake bin ka?’ 6 Ya ce, ‘Garwa ɗari ta mai.’ Sai ya ce masa, ‘Ga takardarka, maza ka zauna, ka rubutu hamsin,’ 7 Ya kuma ce wa wani, ‘Kai fa, nawa ake binka?’ Sai ya ce, ‘Buhu ɗari na alkama.’ Ya ce masa, ‘Ga takardarka, ka rubuta tamanin.’ 8 t Sai maigidan ya yaba wa wakilin nan marar gaskiya saboda wayonsa. Don 'yan zamani a ma'ammalarsu da mutanen zamaninsu, sun fi mutanen haske wayo.
9 t Ina gaya muku, ku yi abokai ta dukiya, ko da yake aba ce wadda take iya aikata mugunta, don sa'ad da ta ƙare su karɓe ku a gidaje masu dawwama.
10 t “Wanda yake da aminci a ƙaramin abu, mai aminci ne a babban abu. Wanda yake marar gaskiya a ƙaramin abu, marar gaskiya ne a babban abu. 11 t Idan fa ba ku yi aminci da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya? 12 In kuma ba ku yi aminci da kayan wani ba, wa zai ba ku halaliyarku?
13 t Ba baran da zai iya bauta wa iyayengiji biyu, ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kuwa ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.”Shari'a da Mulkin Allah
14 t Farisiyawa kuwa da yake masu son kuɗi ne, da jin haka, suka yi masa tsaki.
15 t Sai ya ce musu, “Ku ne masu baratar da kanku a gaban mutane. Amma Allah ya san zukatanku. Abin da mutane suke girmamawa ƙwarai, ai, abin ƙyama ne a gun Allah.
16 t “Attaura da litattafan annabawa suna nan har ya zuwa ga Yahaya, daga lokacin nan kuwa ake yin bisharar Mulkin Allah, kowa kuma yana kutsawa zuwa ciki.
17 t Duk da haka, zai fi sauƙi sararin sama da ƙasa su shuɗe, da ɗigo ɗaya na Attaura ya gushe.”Koyarwar Yesu a kan Kisan Aure
(Mat 19.1-12; Mar 10.1-12)
18 t “Kowa ya saki mata tasa ya auri wata, ya yi zina ke nan. Wanda ma ya auri sakakkiya ya yi zina.”Mai Arziki da Li'azaru
19 t “An yi wani mai arziki, mai sa tufafin jan alharini da farare masu ƙawa, yana shan daularsa a kowace rana. 20 t An kuma ajiye wani gajiyayye a ƙofarsa, mai suna Li'azaru, wanda duk jikinsa miki ne. 21 t Shi kuwa yana marmarin ya ƙoshi da suɗin mai arzikin nan. Har ma karnuka sukan zo suna lasar miyakunsa. 22 Ana nan sai gajiyayyen nan ya mutu, mala'iku kuma suka ɗauke shi, suka kai shi wurin Ibraham. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi. 23 Yana a cikin Hades yana shan azaba, sai ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim daga nesa, da Li'azaru a wurinsa. 24 t Sai ya yi kira ya ce, ‘Baba Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiko Li'azaru ya tsoma kan yatsarsa a ruwa ya sanyaya harshena, don azaba nake sha a cikin wannan wuta.’ 25 t Amma Ibraham ya ce, ‘Ɗana, ka tuna fa, a zamanka na duniya ka sha duniyarka, Li'azaru kuwa ya sha wuya. Amma yanzu daɗi ake ba shi, kai kuwa kana shan azaba. 26 Banda wannan ma duka, tsakaninmu da ku akwai wani gawurtaccen rami mai zurfi, zaunanne, don waɗanda suke son ƙetarewa zuwa wurinku kada su iya, kada kuma kowa ya ƙetaro zuwa wurinmu daga can.’ 27 Sai mai arzikin ya ce, ‘To, ina roƙonka, Baba, ka aika shi zuwa gidan ubana, 28 t don ina da 'yan'uwa biyar maza, ya je ya yi musu gargaɗi, kada su ma su zo wurin azabar nan.’ 29 t Amma Ibrahim ya ce, ‘Ai, suna da littattafan Musa da na annabawa, su saurare su mana.’ 30 t Sai ya ce, ‘A'a, Baba Ibrahim, in dai wani daga cikin matattu ya je wurinsu sa tuba.’ 31 Ibrahim ya ce masa, ‘In dai har ba su saurari littattafan Musa da na annabawa ba, ko da wani ya tashi daga cikin matattu ma, ba za su rinjayu ba.’ ”
Luke 16
1 And he said also unto the disciples, There was a certain rich man, who had a steward; and the same was accused unto him that he was wasting his goods.2 And he called him, and said unto him, What is this that I hear of thee? render the account of thy stewardship; for thou canst be no longer steward.3 And the steward said within himself, What shall I do, seeing that my lord taketh away the stewardship from me? I have not strength to dig; to beg I am ashamed.4 I am resolved what to do, that, when I am put out of the stewardship, they may receive me into their houses.5 And calling to him each one of his lord’s debtors, he said to the first, How much owest thou unto my lord?6 And he said, A hundred measures of oil. And he said unto him, Take thy bond, and sit down quickly and write fifty.7 Then said he to another, And how much owest thou? And he said, A hundred measures of wheat. He saith unto him, Take thy bond, and write fourscore.8 And his lord commended the unrighteous steward because he had done wisely: for the sons of this world are for their own generation wiser than the sons of the light.9 And I say unto you, Make to yourselves friends by means of the mammon of unrighteousness; that, when it shall fail, they may receive you into the eternal tabernacles.10 He that is faithful in a very little is faithful also in much: and he that is unrighteous in a very little is unrighteous also in much.11 If therefore ye have not been faithful in the unrighteous mammon, who will commit to your trust the true riches?12 And if ye have not been faithful in that which is another’s, who will give you that which is your own?13 No servant can serve two masters: for either he will hate the one, and love the other; or else he will hold to one, and despise the other. Ye cannot serve God and mammon.14 And the Pharisees, who were lovers of money, heard all these things; and they scoffed at him.15 And he said unto them, Ye are they that justify yourselves in the sight of men; but God knoweth your hearts: for that which is exalted among men is an abomination in the sight of God.16 The law and the prophets were until John: from that time the gospel of the kingdom of God is preached, and every man entereth violently into it.17 But it is easier for heaven and earth to pass away, than for one tittle of the law to fall.18 Every one that putteth away his wife, and marrieth another, committeth adultery: and he that marrieth one that is put away from a husband committeth adultery.19 Now there was a certain rich man, and he was clothed in purple and fine linen, faring sumptuously every day:20 and a certain beggar named Lazarus was laid at his gate, full of sores,21 and desiring to be fed with the crumbs that fell from the rich man’s table; yea, even the dogs come and licked his sores.22 And it came to pass, that the beggar died, and that he was carried away by the angels into Abraham’s bosom: and the rich man also died, and was buried.23 And in Hades he lifted up his eyes, being in torments, and seeth Abraham afar off, and Lazarus in his bosom.24 And he cried and said, Father Abraham, have mercy on me, and send Lazarus, that he may dip the tip of his finger in water, and cool my tongue; for I am in anguish in this flame.25 But Abraham said, Son, remember that thou in thy lifetime receivedst thy good things, and Lazarus in like manner evil things: but now here he is comforted and thou art in anguish.26 And besides all this, between us and you there is a great gulf fixed, that they that would pass from hence to you may not be able, and that none may cross over from thence to us.27 And he said, I pray thee therefore, father, that thou wouldest send him to my father’s house;28 for I have five brethren; that he may testify unto them, lest they also come into this place of torment.29 But Abraham saith, They have Moses and the prophets; let them hear them.30 And he said, Nay, father Abraham: but if one go to them from the dead, they will repent.31 And he said unto him, If they hear not Moses and the prophets, neither will they be persuaded, if one rise from the dead.