previous next

LUK 18

Misali na wadda Mijinta Ya Mutu da Alƙali

1  t Ya kuma ba su wani misali cewa ya kamata kullum su yi addu'a, kada kuma su karai. 2 Ya ce, “A wani gari an yi wani alƙali marar tsoron Allah, marar kula da mutane. 3 t A garin nan kuwa da wata wadda mijinta ya mutu, sai ta riƙa zuwa wurinsa, tana ce masa, ‘Ka shiga tsakanina da abokin gābana.’ 4 Da fari ya ƙi, amma daga baya sai ya ce a ransa, ‘Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane, 5 t amma saboda gwauruwar nan ta dame ni, sai in bi mata hakkinta, don kada ta gajishe ni da yawan zuwa.’ ” 6 t Sai Ubangiji ya ce, “Ku ji fa abin da alƙalin nan marar gaskiya ya faɗa! 7 t Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke yi masa kuka dare da rana hakkinsu ba? Zai yi jinkiri a wajen taimakonsu ne?

8 t Ina gaya muku, zai biya musu hakkinsu, da wuri kuwa. Amma kuwa sa'ad da Ɗan Mutum ya zo, zai tarar da bangaskiya a duniya ne?”

Misali na Bafarisiye da Mai Karɓar Haraji


9  t Sai kuma ya ba da misalin nan ga waɗansu masu amince wa kansu, wai su masu adalci ne, har suna raina sauran mutane, ya ce, 10 t “Waɗansu mutum biyu suka shiga Haikali yin addu'a, ɗaya Bafarisiye, ɗaya kuma mai karɓar haraji. 11 t Sai Bafarisiyen ya miƙe, ya yi addu'a ga kansa ya ce, ‘Ya Allah, na gode maka, da yake ni ba kamar sauran mutane nake ba, mazambata, marasa adalci, mazinata, ko ma kamar mai karɓar harajin nan. 12 t Duk mako ina azumi sau biyu. Kome na samu nakan fitar da zakka.’ 13 t Mai karɓar haraji kuwa yana tsaye daga can nesa, bai yarda ya ɗaga kai sama ba, sai dai yana bugun ƙirjinsa, yana cewa, ‘Ya Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi!’

14 t Ina dai gaya muku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar ɗayan ba. Don duk mai ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuwa, ɗaukaka shi za a yi.”

Yesu Ya sa wa 'Yan Yara Albarka

(Mat 19.13-15; Mar 10.13-16)


15 Waɗansu suka kawo masa 'yan yaransu domin ya taɓa su. Ganin haka sai almajiransa suka kwaɓe su. 16 Amma Yesu ya kira 'yan yara wurinsa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai, Mulkin Allah na irinsu ne.

17 t Hakika, ina gaya muku, duk wanda bai yi na'am da Mulkin Allah kamar yadda ƙaramin yaro yake yi ba, ba zai shiga Mulkin ba har abada.”

Shugaban Jama'a Mai Arziki

(Mat 19.16-30; Mar 10.17-31)


18  t Wani shugaban jama'a ya tambaye shi ya ce, “Malam managarci, me zan yi in gaji rai madawwami?” 19 Sai Yesu ya ce masa, “Don me ka kira ni managarci? Ai, ba wani Managarci, sai Allah kaɗai. 20 t Kā dai san umarnan nan, ‘Kada ka yi zina. Kada ka yi kisankai. Kada ka yi sata. Kada ka yi shaidar zur. Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ” 21 Sai ya ce, “Ai, duk na kiyaye waɗannan tun ƙuruciyata.” 22 t Da Yesu ya ji haka, ya ce masa, “Har yanzu abu guda ne kawai ya rage maka, ka sayar da duk mallakarka, ka rarraba wa gajiyayyu, za ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.” 23 Da jin haka, sai ya yi baƙin ciki gaya, don shi mai arziki ne da gaske. 24 t Yesu kuwa da ya gan shi haka, ya ce, “Kai! Da ƙyar kamar me masu dukiya su shiga Mulkin Allah! 25 Ai, zai fiye wa raƙumi sauƙi ya bi ta kafar allura, da mai arziki ya shiga Mulkin Allah.” 26 Waɗanda suka ji wannan magana suka ce, “To, in haka ne, wa zai sami ceto ke nan?”

27 t Amma Yesu ya ce, “Abin da ya fi ƙarfin mutum, mai yiwuwa ne a gun Allah.”
28  t Sai Bitrus ya ce, “To, ai, ga shi, mun bar mallakarmu, mun bi ka.” 29 Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, ba wanda zai bar gida, ko matarsa, ko 'yan'uwansa, ko iyayensa, ko kuma 'ya'yansa, saboda Mulkin Allah,

30 t sa'an nan ya kasa samun ninkinsu mai yawa a yanzu, a Lahira kuma ya sami rai madawwami.”

Yesu Ya Sāke Faɗar irin Mutuwar da zai Yi

(Mat 20.17-19; Mar 10.32-34)


31  t Sai ya keɓe sha biyun nan, ya ce musu, “Ga shi, za mu Urushalima, duk abin da yake rubuce kuma game da Ɗan Mutum, ta hannun annabawa zai tabbata. 32 t Gama za a bāshe shi ga al'ummai, a yi masa ba'a, a wulakanta shi, a kuma tofa masa yau. 33 t Za su yi masa bulala, su kashe shi, a rana ta uku kuma ya tashi.”

34 t Amma ko ɗaya ba su fahimci waɗannan abubuwa ba, domin zancen nan a ɓoye yake daga gare su, ba su ma gane abin da aka faɗa ba.

Warkar da Makaho Mai Bara a kusa da Yariko

(Mat 20.29-34; Mar 10.46-52)


35  t Da ya kusato Yariko, ga wani makaho zaune a gefen hanya, yana bara. 36 Da ya ji taro na wucewa, sai ya tambaya ko mene ne. 37 t Suka ce masa, “Ai, Yesu Banazare ne yake wucewa.” 38 t Sai ya ɗaga murya ya ce, “Ya Yesu Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!” 39 t Sai waɗanda suke gaba suka kwaɓe shi ya yi shiru. Amma ƙara ɗaga murya yake yi ƙwarai da gaske, yana cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!” 40 Sai Yesu ya tsaya, ya yi umarni a kawo shi wurinsa. Da ya zo kusa, ya tambaye shi, 41 “Me kake so in yi maka?” Ya ce, “Ya Ubangiji, in sami gani!” 42 t Yesu ya ce masa, “Karɓi ganin gari, bangaskiyarka ta warkar da kai.” 43 t Nan take ya sami gani, ya bi Yesu, yana ɗaukaka Allah. Ganin haka, sai duk jama'a suka yabi Allah.

Luke 18

1 And he spake a parable unto them to the end that they ought always to pray, and not to faint;2 saying, There was in a city a judge, who feared not God, and regarded not man:3 and there was a widow in that city; and she came oft unto him, saying, Avenge me of mine adversary.4 And he would not for a while: but afterward he said within himself, Though I fear not God, nor regard man;5 yet because this widow troubleth me, I will avenge her, lest she wear me out by her continual coming.6 And the Lord said, Hear what the unrighteous judge saith.7 And shall not God avenge his elect, that cry to him day and night, and yet he is longsuffering over them?8 I say unto you, that he will avenge them speedily. Nevertheless, when the Son of man cometh, shall he find faith on the earth?9 And he spake also this parable unto certain who trusted in themselves that they were righteous, and set all others at nought:10 Two men went up into the temple to pray; the one a Pharisee, and the other a publican.11 The Pharisee stood and prayed thus with himself, God, I thank thee, that I am not as the rest of men, extortioners, unjust, adulterers, or even as this publican.12 I fast twice in the week; I give tithes of all that I get.13 But the publican, standing afar off, would not lift up so much as his eyes unto heaven, but smote his breast, saying, God, be thou merciful to me a sinner.14 I say unto you, This man went down to his house justified rather than the other: for every one that exalteth himself shall be humbled; but he that humbleth himself shall be exalted.15 And they were bringing unto him also their babes, that he should touch them: but when the disciples saw it, they rebuked them.16 But Jesus called them unto him, saying, Suffer the little children to come unto me, and forbid them not: for to such belongeth the kingdom of God.17 Verily I say unto you, Whosoever shall not receive the kingdom of God as a little child, he shall in no wise enter therein.18 And a certain ruler asked him, saying, Good Teacher, what shall I do to inherit eternal life?19 And Jesus said unto him, Why callest thou me good? none is good, save one, even God.20 Thou knowest the commandments, Do not commit adultery, Do not kill, Do not steal, Do not bear false witness, Honor thy father and mother.21 And he said, All these things have I observed from my youth up.22 And when Jesus heard it, he said unto him, One thing thou lackest yet: sell all that thou hast, and distribute unto the poor, and thou shalt have treasure in heaven: and come, follow me.23 But when he heard these things, he became exceeding sorrowful; for he was very rich.24 And Jesus seeing him said, How hardly shall they that have riches enter into the kingdom of God!25 For it is easier for a camel to enter in through a needle’s eye, than for a rich man to enter into the kingdom of God.26 And they that heard it said, Then who can be saved?27 But he said, The things which are impossible with men are possible with God.28 And Peter said, Lo, we have left our own, and followed thee.29 And he said unto them, Verily I say unto you, There is no man that hath left house, or wife, or brethren, or parents, or children, for the kingdom of God’s sake,30 who shall not receive manifold more in this time, and in the world to come eternal life.31 And he took unto him the twelve, and said unto them, Behold, we go up to Jerusalem, and all the things that are written through the prophets shall be accomplished unto the Son of man.32 For he shall be delivered up unto the Gentiles, and shall be mocked, and shamefully treated, and spit upon:33 and they shall scourge and kill him: and the third day he shall rise again.34 And they understood none of these things; and this saying was hid from them, and they perceived not the things that were said.35 And it came to pass, as he drew nigh unto Jericho, a certain blind man sat by the way side begging:36 and hearing a multitude going by, he inquired what this meant.37 And they told him that Jesus of Nazareth passeth by.38 And he cried, saying, Jesus, thou son of David, have mercy on me.39 And they that went before rebuked him, that he should hold his peace: but he cried out the more a great deal, Thou son of David, have mercy on me.40 And Jesus stood, and commanded him to be brought unto him: and when he was come near, he asked him,41 What wilt thou that I should do unto thee? And he said, Lord, that I may receive my sight.42 And Jesus said unto him, Receive thy sight; thy faith hath made thee whole.43 And immediately he received his sight, and followed him, glorifying God: and all the people, when they saw it, gave praise unto God.