LUK 19
Yesu da Zakka
1 t Yesu ya shiga Yariko. Yana ratsa garin, 2 sai wani mutum mai suna Zakka, babba ne a cikin masu karɓar haraji, mai arziki ne kuma, 3 ya nemi ganin ko wane ne Yesu, amma ya kasa ganinsa saboda taro, don shi gajere ne. 4 t Sai ya yi gaba a guje, ya hau wani durumi don ya gan shi, don Yesu ta nan zai bi. 5 Da Yesu ya iso wurin, ya ɗaga kai ya ce masa, “Zakka, yi maza ka sauko, domin yau lalle a gidanka zan sauka.” 6 Sai ya yi hanzari ya sauko, ya karɓe shi da murna. 7 t Da suka ga haka, duk suka yi ta gunaguni, suka ce, “A! A gidan mai zunubi dai ya sauka!” 8 t Sai Zakka ya miƙe, ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji, ka ga, rabin mallakata zan ba gajiyayyu. Kowa na zalunta kuwa, zan mayar masa da ninki huɗu.” 9 t Yesu ya ce masa, “Yau kam, ceto ya sauka a gidan nan, tun da yake shi ma ɗan Ibrahim ne.
10 t Don Ɗan Mutum ya zo ne musamman garin neman abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”Misali na Fam Goma
11 t Da suka ji abubuwan nan, Yesu ya ci gaba da gaya musu wani misali, gama yana kusa da Urushalima, suna kuma tsammani Mulkin Allah zai bayyana nan da nan. 12 Sai ya ce, “Wani mutum mai asali ya tafi wata ƙasa mai nisa neman sarauta yă dawo. 13 t Sai ya kira bayinsa goma, ya ba su fam guda guda, ya kuma ce musu, ‘Ku yi ta jujjuya su har in dawo.’ 14 Amma mutanensa suka ƙi shi, har suka aiki jakadu a bayansa, cewa ba sa so ya yi mulki a kansu. 15 Ana nan, da ya samo sarautar ya dawo, sai ya yi umarni a kirawo bayin nan da ya bai wa kuɗin, ya ga ribar da suka ci a wajen jujjuyawar. 16 Sai na farko ya zo gabansa, ya ce, ‘Ya ubangiji, fam ɗinka ya jawo fam goma.’ 17 t Sai shi kuma ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki! Tun da ka yi gaskiya a kan ƙaramin abu, to, na ba ka mulkin gari goma.’ 18 Sai na biyun ya zo, ya ce, ‘Ya ubangida, fam ɗinka ya jawo fam biyar.’ 19 Shi kuma ya ce masa, ‘Kai ma na ba ka mulkin gari biyar.’ 20 Wani kuma ya zo, ya ce, ‘Ya ubangiji, ga fam ɗinka nan! Dā ma a mayani na ƙulle shi, na ajiye. 21 t Domin ina tsoronka, don kai mutum ne mai tsanani, son banza a gare ka, kakan girbi abin da ba kai ka shuka ba.’ 22 t Sai ya ce masa ‘Kai mugun bawa! Zan yi maka shari'a bisa ga abin da ka faɗa da bakinka. Ashe, ka sani ni mutum ne mai tsanani, mai son banza, ina kuma girbar abin da ba ni na shuka ba? 23 To, in haka ne, don me ba ka ajiye kuɗin nawa a banki ba, da dawowata in ƙarɓa, har da riba?” 24 Sai ya ce wa na tsaitsaye a wurin, ‘Ku karɓe fam ɗin daga gunsa, ku bai wa mai goman nan.’ 25 Suka ce masa, ‘Ya ubangiji, ai, yana da fam goma.’ 26 t ‘Ina dai gaya muku, duk mai abu a kan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai a karɓe masa.
27 Waɗannan maƙiya nawa kuwa, da ba sa so in yi mulki a kansu, ku kawo su nan a kashe su a gabana.’ ”Mutanen Urushalima sun Marabci Yesu
(Mat 21.1-11; Mar 11.1-11; Yah 12.12-19)
28 t Da Yesu ya faɗi haka, ya yi gaba zuwa Urushalima. 29 t Da ya kusato Betafaji da Betanya, a wajen dutsen da ake kira Dutsen Zaitun, ya aiki almajiransa biyu, 30 ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake gabanku. Da shigarku za ku ga wani aholaki a ɗaure, wanda ba a taɓa hawa ba. Ku kwanto shi. 31 Kowa ya tambaye ku, ‘Don me kuke kwance shi?’ ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsa.’ ” 32 t Sai waɗanda aka aika suka tafi, suka tarar kamar yadda ya faɗa musu. 33 Suna cikin kwance aholakin, masu shi suka ce musu, “Don me kuke kwance aholakin nan?” 34 Sai suka ce, “Ubangiji ne yake bukatarsa.” 35 Sai suka kawo shi wurin Yesu. Da suka shimfiɗa mayafansu a kan aholakin, suka ɗora Yesu. 36 t Yana cikin tafiya, sai mutane suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya. 37 t Da ya zo gab da gangaren Dutsen Zaitun, sai duk taron almajiran suka ɗauki murna, suna yabon Allah da murya mai ƙarfi saboda duk mu'ujizan da suka gani. 38 t Suka ce, “Albarka ta tabbata ga Sarkin nan mai zuwa da sunan Ubangiji! Salama ta tabbata a Sama, ɗaukaka kuma ga Allah!” 39 t Sai waɗansu Farisiyawa a cikin taron suka ce masa, “Malam, ka kwaɓi almajiranka mana!”
40 t Ya amsa ya ce, “Ina dai gaya muku, ko waɗannan sun yi shiru, to, duwatsu ma sai su ɗauki sowa.”
41 t Da ya matso kusa, ya kuma hangi birnin, sai ya yi masa kuka, 42 ya ce, “Da ma a ce a yanzu kun san abubuwan da suke kawo salama. Amma ga shi, a yanzu a ɓoye suke a gare ku. 43 t Don lokaci zai auko muku da maƙiyanku za su yi muku ƙawanya, su yi muku zobe, su kuma tsattsare ku ta kowane gefe,
44 t su fyaɗa ku a ƙasa, ku mutanen birni duka, ba kuma za su bar wani dutse a kan ɗan'uwansa ba a birninku, don ba ku fahimci lokacin da ake sauko muku da alheri ba.”Yesu Ya Tsabtace Haikali
(Mat 21.12-17; Mar 11.15-19; Yah 12.13-22)
45 Sai ya shiga Haikali, ya fara korar masu sayarwa,
46 t ya ce musu, “Ai, a rubuce yake cewa, ‘Ɗakina zai kasance ɗakin addu'a.’ Amma ku kun maishe shi kogon 'yan fashi.”
47 t Kowace rana ya yi ta koyarwa a Haikali. Amma manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabannin jama'a suka nema su hallaka shi. 48 Suka kuwa rasa abin da za su yi, saboda maganarsa ta ɗauke wa duk jama'a hankali.
Luke 19
1 And he entered and was passing through Jericho.2 And behold, a man called by name Zacchaeus; and he was a chief publican, and he was rich.3 And he sought to see Jesus who he was; and could not for the crowd, because he was little of stature.4 And he ran on before, and climbed up into a sycomore tree to see him: for he was to pass that way.5 And when Jesus came to the place, he looked up, and said unto him, Zacchaeus, make haste, and come down; for to-day I must abide at thy house.6 And he made haste, and came down, and received him joyfully.7 And when they saw it, they all murmured, saying, He is gone in to lodge with a man that is a sinner.8 And Zacchaeus stood, and said unto the Lord, Behold, Lord, the half of my goods I give to the poor; and if I have wrongfully exacted aught of any man, I restore fourfold.9 And Jesus said unto him, To-day is salvation come to this house, forasmuch as he also is a son of Abraham.10 For the Son of man came to seek and to save that which was lost.11 And as they heard these things, he added and spake a parable, because he was nigh to Jerusalem, and because they supposed that the kingdom of God was immediately to appear.12 He said therefore, A certain nobleman went into a far country, to receive for himself a kingdom, and to return.13 And he called ten servants of his, and gave them ten pounds, and said unto them, Trade ye herewith till I come.14 But his citizens hated him, and sent an ambassage after him, saying, We will not that this man reign over us.15 And it came to pass, when he was come back again, having received the kingdom, that he commanded these servants, unto whom he had given the money, to be called to him, that he might know what they had gained by trading.16 And the first came before him, saying, Lord, thy pound hath made ten pounds more.17 And he said unto him, Well done, thou good servant: because thou wast found faithful in a very little, have thou authority over ten cities.18 And the second came, saying, Thy pound, Lord, hath made five pounds.19 And he said unto him also, Be thou also over five cities.20 And another came, saying, Lord, behold, here is thy pound, which I kept laid up in a napkin:21 for I feared thee, because thou art an austere man: thou takest up that which thou layedst not down, and reapest that which thou didst not sow.22 He saith unto him, Out of thine own mouth will I judge thee, thou wicked servant. Thou knewest that I am an austere man, taking up that which I laid not down, and reaping that which I did not sow;23 then wherefore gavest thou not my money into the bank, and I at my coming should have required it with interest?24 And he said unto them that stood by, Take away from him the pound, and give it unto him that hath the ten pounds.25 And they said unto him, Lord, he hath ten pounds.26 I say unto you, that unto every one that hath shall be given; but from him that hath not, even that which he hath shall be taken away from him.27 But these mine enemies, that would not that I should reign over them, bring hither, and slay them before me.28 And when he had thus spoken, he went on before, going up to Jerusalem.29 And it came to pass, when he drew nigh unto Bethphage and Bethany, at the mount that is called Olivet, he sent two of the disciples,30 saying, Go your way into the village over against you; in which as ye enter ye shall find a colt tied, whereon no man ever yet sat: loose him, and bring him.31 And if any one ask you, Why do ye loose him? thus shall ye say, The Lord hath need of him.32 And they that were sent went away, and found even as he had said unto them.33 And as they were loosing the colt, the owners thereof said unto them, Why loose ye the colt?34 And they said, The Lord hath need of him.35 And they brought him to Jesus: and they threw their garments upon the colt, and set Jesus thereon.36 And as he went, they spread their garments in the way.37 And as he was now drawing nigh, even at the descent of the mount of Olives, the whole multitude of the disciples began to rejoice and praise God with a loud voice for all the mighty works which they had seen;38 saying, Blessed is the King that cometh in the name of the Lord: peace in heaven, and glory in the highest.39 And some of the Pharisees from the multitude said unto him, Teacher, rebuke thy disciples.40 And he answered and said, I tell you that, if these shall hold their peace, the stones will cry out.41 And when he drew nigh, he saw the city and wept over it,42 saying, If thou hadst known in this day, even thou, the things which belong unto peace! but now they are hid from thine eyes.43 For the days shall come upon thee, when thine enemies shall cast up a bank about thee, and compass thee round, and keep thee in on every side,44 and shall dash thee to the ground, and thy children within thee; and they shall not leave in thee one stone upon another; because thou knewest not the time of thy visitation.45 And he entered into the temple, and began to cast out them that sold,46 saying unto them, It is written, And my house shall be a house of prayer: but ye have made it a den of robbers.47 And he was teaching daily in the temple. But the chief priests and the scribes and the principal men of the people sought to destroy him:48 and they could not find what they might do; for the people all hung upon him, listening.