LUK 2
Haihuwar Yesu
(Mat. 1. 18-25)
1 t A kwanakin nan Kaisar Augustas ya yi shela, cewa a rubuta dukkan mutanen da suke ƙarƙashin mulkinsa. 2 t Wannan shi ne ƙirga na fari da aka yi a zamanin Kiriniyas, mai mulkin ƙasar Suriya. 3 Kowa sai ya tafi garinsu a rubuta shi. 4 t Yusufu shi ma ya tashi daga birnin Nazarat, a ƙasar Galili, ya tafi ƙasar Yahudiya, ya je birnin Dawuda, da ake kira Baitalami (domin shi daga gidan Dawuda ne, na cikin zuriyarsa), 5 don a rubuta shi, duk da Maryamu tashinsa, wadda take kuma da ciki. 6 Sa'ad da suke can kuwa, sai lokacin haihuwarta ya yi.
7 Sai ta haifi ɗanta na fari, ta rufi shi da zanen goyo, ta kuma kwantar da shi a wani komi dabbobi, don ba su sami ɗaki a masaukin ba.Makiyaya da Mala'iku
8 A wannan yankin ƙasa kuwa waɗansu makiyaya suna kwana a filin Allah, suna tsaron garken tumakinsu da dad dare. 9 t Sai ga wani mala'ikan Ubangiji tsaye kusa da su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewayensu, har suka tsorata gaya, 10 t Sai mala'ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ga shi, albishir na kawo muku na farin ciki mai yawa, wanda zai zama na dukan mutane. 11 t Domin yau an haifa muku Mai Ceto a birnin Dawuda, wanda yake shi ne Almasihu, Ubangiji. 12 t Ga alamar da za ku gani, za ku sami jariri rufe da zanen goyo, kwance a komin dabbobi.”
13 Ba labari sai ga taron rundunar Sama tare da mala'ikan nan, suna yabon Allah, suna cewa,
14 t “Ɗaukaka ga Allah ta tabbata, can cikin Sama mafi ɗaukaka.
A duniya salama ta tabbata, ga mutanen da yake murna da su matuƙa.”
15 Da mala'iku suka tafi daga gare su suka koma Sama, sai makiyayan suka ce wa juna, “Mu tafi Baitalami yanzu, mu ga abin nan da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar da mu.” 16 Sai suka tafi da hanzari, suka sami Maryamu da Yusufu, da kuma jaririn kwance a komin dabbobi. 17 Da suka gan shi, suka bayyana maganar da aka faɗa musu game da wannan ɗan yaro. 18 Duk waɗanda suka ji kuma, suka yi ta al'ajabin abin da makiyayan nan suka faɗa musu. 19 t Maryamu kuwa sai ta riƙe duk abubuwan da aka faɗa, tana biya su a zuci.
20 t Makiyayan suka koma, suna ta ɗaukaka Allah, suna yabonsa, saboda duk abin da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.Kaciyar Yesu
21 t Da rana ta takwas ta kewayo da za a yi masa kaciya, aka sa masa suna Yesu, wato sunan da mala'ika ya faɗa kafin ya zauna a ciki.Miƙa Yesu a Haikali
22 t Da kwanakin tsarkakewarsu suka cika bisa ga Shari'ar Musa, suka kawo shi Urushalima, su miƙa shi ga Ubangiji 23 t (kamar dai yadda yake a rubuce a Shari'ar Ubangiji cewa, “Duk ɗan farin da aka haifa, za a ce da shi tsattsarka ne Ubangiji”),
24 t su kuma yi hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Shari'ar Ubangiji cewa, “Kurciyoyi biyu, ko kuwa 'yan shila biyu.”
25 t To, akwai wani mutum a Urushalima, mai suna Saminu, adali, mai bautar Allah, yana kuma ɗokin ganin ta'aziyyar Isra'ila. Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi. 26 Ruhu Mai Tsarki kuwa ya riga ya bayyana masa, cewa ba zai mutu ba sai ya ga Almasihun Ubangiji. 27 t Ruhu na iza shi, sai ya shiga Haikalin. Da iyayen suka shigo da ɗan yaron nan Yesu, su yi masa yadda ka'idar Shari'ar ta ce,
28 sai Saminu ya rungume shi, ya yi wa Allah godiya, ya ce,
29 t “Yanzu kam, ya Mamallaki,
Sai ka sallami bawanka lafiya,
Bisa ga abin da ka faɗa,
30 t Don na ga cetonka zahiri,
31 Da ka shirya a gaban kabilai duka,
32 t Haske mai bayyana wa alummai hanyarka,
Da kuma ɗaukakar jama'arka Isra'ila.”
33 Uwa tasa da ubansa kuwa suna mamakin abin da aka faɗa game da shi,
34 t Sai Saminu ya sa musu albarka, ya ce wa Maryamu uwar Yesu,
“Kin ga wannan yaro, shi aka sa ya zama sanadin faɗuwar waɗansu, tashin waɗansu kuma da yawa cikin Isra'ila,
Zai kuma zama alama wadda ake kushenta,
35 Domin tunanin zukata da yawa su bayyana.
I, ke ma, takobi zai tsaga zuciyarki.”
36 t Akwai kuma wata annabiya, mai suna Hannatu, 'yar Fanuyila, na kabilar Ashiru. Ta kuwa tsufa ƙwarai, ta yi zaman aure shekara bakwai bayan ɗaukanta na budurci, 37 t da mijinta ya mutu kuma ta yi zaman gwauranci har shekara tamanin da huɗu. Ba ta rabuwa da Haikalin, tana bauta wa Allah dare da rana ta wurin yin addu'a da azumi.
38 t Nan take ita ma ta zo, ta yi wa Allah godiya, ta kuma yi maganar ɗan yaron nan ga dukan masu sauraron fansar Urushalima.Komawa Nazarat
39 t Bayan sun ƙare kome da kome bisa ga Shari'ar Ubangiji, sai suka koma ƙasar Galili suka tafi garinsu Nazarat.
40 t Ɗan yaron kuwa ya girma, ya kawo ƙarfi, yana mai matuƙar hikima. Alherin Allah kuwa yana tare da shi.Yesu, Ɗan Saurayi, ya Shiga Haikali
41 t To, iyayensa sukan je Urushalima kowace shekara a lokacin Idin Ƙetarewa. 42 Da ya shekara goma sha biyu, sai suka tafi tare da shi bisa ga al'adarsu a lokacin Idi. 43 Da aka gama idin kuma, suna cikin komowa, sai yaron, wato Yesu, ya tsaya a Urushalima, ba da sanin iyayensa ba. 44 Su kuwa suka yi ta tafiya yini guda, suna zaton yana cikin ayari. Sai suka yi ta cigiyarsa cikin 'yan'uwansu da idon sani. 45 Da ba su same shi ba, suka koma Urushalima, suna ta cigiyarsa. 46 Sai kuma a rana uku suka same shi a Haikalin zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu, yana kuma yi musu tambayoyi. 47 t Duk waɗanda suka ji shi kuwa suka yi al'ajabin irin fahimtarsa da amsoshinsa. 48 t Da suka gan shi suka yi mamaki, sai uwa tasa ta ce masa, “Ya kai ɗana, yaya ka yi mana haka? Ga shi nan, ni da babanka muna ta nemanka duk ranmu a ɓace.” 49 t Sai ya ce musu, “Me ya sa kuka yi ta nemana? Ashe, ba ku sani wajibi ne in yi sha'anin Ubana ba?” 50 t Amma ba su fahimci maganar da ya yi musu ba.
51 t Sai ya koma Nazarat tare da su, yana yi musu biyayya. Uwa tasa kuwa na riƙe da dukan abubuwan nan a ranta.
52 t Yesu kuwa ya yi ta ƙaruwa da hikima, da girma, da kuma tagomashi wurin Allah da mutane.
Luke 2
1 Now it came to pass in those days, there went out a decree from Caesar Augustus, that all the world should be enrolled.2 This was the first enrolment made when Quirinius was governor of Syria.3 And all went to enrol themselves, every one to his own city.4 And Joseph also went up from Galilee, out of the city of Nazareth, into Judaea, to the city of David, which is called Bethlehem, because he was of the house and family of David;5 to enrol himself with Mary, who was betrothed to him, being great with child.6 And it came to pass, while they were there, the days were fulfilled that she should be delivered.7 And she brought forth her firstborn son; and she wrapped him in swaddling clothes, and laid him in a manger, because there was no room for them in the inn.8 And there were shepherds in the same country abiding in the field, and keeping watch by night over their flock.9 And an angel of the Lord stood by them, and the glory of the Lord shone round about them: and they were sore afraid.10 And the angel said unto them, Be not afraid; for behold, I bring you good tidings of great joy which shall be to all the people:11 for there is born to you this day in the city of David a Saviour, who is Christ the Lord.12 And this is the sign unto you: Ye shall find a babe wrapped in swaddling clothes, and lying in a manger.13 And suddenly there was with the angel a multitude of the heavenly host praising God, and saying,
14 Glory to God in the highest, And on earth peace among men in whom he is well pleased.
15 And it came to pass, when the angels went away from them into heaven, the shepherds said one to another, Let us now go even unto Bethlehem, and see this thing that is come to pass, which the Lord hath made known unto us.16 And they came with haste, and found both Mary and Joseph, and the babe lying in the manger.17 And when they saw it, they made known concerning the saying which was spoken to them about this child.18 And all that heard it wondered at the things which were spoken unto them by the shepherds.19 But Mary kept all these sayings, pondering them in her heart.20 And the shepherds returned, glorifying and praising God for all the things that they had heard and seen, even as it was spoken unto them.21 And when eight days were fulfilled for circumcising him, his name was called JESUS, which was so called by the angel before he was conceived in the womb.22 And when the days of their purification according to the law of Moses were fulfilled, they brought him up to Jerusalem, to present him to the Lord23 (as it is written in the law of the Lord, Every male that openeth the womb shall be called holy to the Lord),24 and to offer a sacrifice according to that which is said in the law of the Lord, A pair of turtledoves, or two young pigeons.25 And behold, there was a man in Jerusalem whose name was Simeon; and this man was righteous and devout, looking for the consolation of Israel: and the Holy Spirit was upon him.26 And it had been revealed unto him by the Holy Spirit, that he should not see death, before he had seen the Lord’s Christ.27 And he came in the Spirit into the temple: and when the parents brought in the child Jesus, that they might do concerning him after the custom of the law,28 then he received him into his arms, and blessed God, and said,
29 Now lettest thou thy servant depart, Lord, According to thy word, in peace;
30 For mine eyes have seen thy salvation,
31 Which thou hast prepared before the face of all peoples;
32 A light for revelation to the Gentiles, And the glory of thy people Israel.
33 And his father and his mother were marvelling at the things which were spoken concerning him;34 and Simeon blessed them, and said unto Mary his mother, Behold, this child is set for the falling and the rising of many in Israel; and for a sign which is spoken against;35 yea and a sword shall pierce through thine own soul; that thoughts out of many hearts may be revealed.36 And there was one Anna, a prophetess, the daughter of Phanuel, of the tribe of Asher (she was of a great age, having lived with a husband seven years from her virginity,37 and she had been a widow even unto fourscore and four years), who departed not from the temple, worshipping with fastings and supplications night and day.38 And coming up at that very hour she gave thanks unto God, and spake of him to all them that were looking for the redemption of Jerusalem.39 And when they had accomplished all things that were according to the law of the Lord, they returned into Galilee, to their own city Nazareth.40 And the child grew, and waxed strong, filled with wisdom: and the grace of God was upon him.41 And his parents went every year to Jerusalem at the feast of the passover.42 And when he was twelve years old, they went up after the custom of the feast;43 and when they had fulfilled the days, as they were returning, the boy Jesus tarried behind in Jerusalem; and his parents knew it not;44 but supposing him to be in the company, they went a day’s journey; and they sought for him among their kinsfolk and acquaintance:45 and when they found him not, they returned to Jerusalem, seeking for him.46 And it came to pass, after three days they found him in the temple, sitting in the midst of the teachers, both hearing them, and asking them questions:47 and all that heard him were amazed at his understanding and his answers.48 And when they saw him, they were astonished; and his mother said unto him, Son, why hast thou thus dealt with us? behold, thy father and I sought thee sorrowing.49 And he said unto them, How is it that ye sought me? knew ye not that I must be in my Father’s house?50 And they understood not the saying which he spake unto them.51 And he went down with them, and came to Nazareth; and he was subject unto them: and his mother kept all these sayings in her heart.52 And Jesus advanced in wisdom and stature, and in favor with God and men.