previous next

LUK 20

Ana Shakkar Izinin Yesu

(Mat 21.23-27; Mar 11.27-33)

1  t Wata rana yana koyar da mutane a Haikali, yana yi musu bishara, sai ga manyan firistoci da malaman Attaura, da shugabanni suka matso, 2 t suka ce masa, “Gaya mana da wane izini kake yin abubuwan nan, ko kuwa wa ya ba ka izinin?” 3 Sai ya amsa musu ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku gaya mini, 4 t baftismar da Yahaya ya yi, daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?” 5 Sai suka yi muhawwara da juna suka ce, “In mun ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’ 6 t In kuwa muka ce, ‘Ta mutum ce,’ sai duk jama'a su jajjefe mu, don sun tabbata Yahaya annabi ne.” 7 Sai suka amsa masa, suka ce, ba su san daga inda take ba.

8 Yesu ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”

Misali na Manoman da suka Yi Ijarar Garkar Inabi

(Mat 21.33-46; Mar 12.1-12)


9  t Sai ya shiga ba jama'a misalin nan, ya ce, “Wani mutum ne ya yi garkar inabi, ya ba waɗansu manoma ijararta, ya kuma tafi wata ƙasa, ya daɗe. 10 Da kakar inabi ta yi, ya aiki wani bawansa a gun manoman nan su ba shi gallar garkar. Amma manoman suka yi masa dūka, suka kore shi hannu wofi. 11 Ya kuma aiki wani bawa, shi ma suka yi masa dūka, suka wulakanta shi, suka kore shi hannu wofi. 12 Har wa yau dai ya aiki na uku, shi kuwa suka yi masa rauni, suka kore shi. 13 t Sai mai garkar ya ce, ‘Me zan yi ke nan? Zan aiki ƙaunataccen ɗana. Kila sa ga girmansa.’ 14 Amma da manoman suka gan shi, suka yi shawara da juna suka ce, ‘Ai, wannan shi ne magajin. Mu kashe shi mana, gādon ya zama namu.’ 15 Sai suka jefa shi a bayan shinge, suka kashe shi. To, me ubangijin garkan nan zai yi da su? 16 t Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba waɗansu garkar.” Da suka ji haka, suka ce, “Allah ya sawwaƙe!”

17 t Amma ya dube su, ya ce, “Wannan da yake a rubuce fa cewa,
‘Dutsen da magina suka ƙi,
Shi ne ya zama mafificin dutsen gini?’

18  t Kowa ya faɗo a kan dutsen nan, sai ya ragargaje, amma wanda dutsen nan ya faɗa wa, niƙe shi zai yi kamar gari.”

Biyan Haraji ga Kaisar

(Mat 22.15-22; Mar 12.13-17)


19  t Nan take malaman Attaura da manyan firistoci suka nema su kama Yesu, don sun lura a kansu ne ya ba da misalin, amma suna jin tsoron jama'a. 20 t Sai suka yi ta haƙwansa, suka aiki 'yan rahoto, su kuwa suka nuna kamar su masu adalci ne, da nufin su kama shi a maganarsa, su kuma ba da shi ga mai mulki ya hukunta shi. 21 t Suka tambaye shi suka ce, “Malam, ai, mun sani maganarka da koyarwarka duk gaskiya ne. Ka ɗauki kowa da kowa daidai, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi. 22 Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa babu?” 23 Shi kuwa ya gane makircinsu, ya ce musu, 24 “Ku nuna mini dinari. Surar wa da sunan wa yake a jikinsa?” Suka ce, “Na Kaisar ne.” 25 t Sai ya ce musu, “To, ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.”

26 Sai suka kasa kama shi a kan wannan magana gaban mutane. Saboda kuma mamakin amsarsa, suka yi shiru.

Tambaya a kan Tashin Matattu

(Mat 22.23-33; Mar 12.18-27)


27  t Sai waɗansu Sadukiyawa suka zo wurinsa (su da suke cewa, ba tashin matattu), 28 t suka tambaye shi suka ce, “Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan ɗan'uwan mutum ya mutu, ya bar matarsa ba ɗa, lalle mutumin ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya. 29 To, an yi waɗansu 'yan'uwa maza guda bakwai. Na farko ya yi aure, ya mutu bai bar na baya ba. 30 Na biyun, 31 da na ukun kuma suka aure ta. Haka dai, duk bakwai ɗin suka aure ta, suka mutu, ba wanda ya bar ɗa. 32 Daga baya kuma ita matar ta mutu.

33 To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai ɗin sun aure ta.”
34 Sai Yesu ya ce musu, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna aurarwa. 35 t Amma waɗanda aka ga sun cancanci samun shiga wancan zamani da kuma tashin nan daga matattu, ba za su yi aure ko aurarwa ba. 36 t Ba shi yiwuwa su sāke mutuwa, don daidai suke da mala'iku, 'ya'yan Allah ne kuwa, da yake 'ya'yan tashin matattu ne. 37 t Game da tashin matattu kuwa, ai, Musa ma ya faɗa, a labarin kurmin, inda ya kira Ubangiji, Allahn Ibrahim, da Allahn Ishaku, da Allahn Yakubu. 38 Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba. Don a wurinsa duka rayayyu ne.” 39 Sai waɗansu malaman Attaura suka amsa suka ce, “Malam, ka faɗi daidai.”

40 t Daga nan kuma ba su yi ƙarfin halin tambayarsa wani abu ba.

Tambaya a kan Ɗan Dawuda

(Mat 22.41-46; Mar 12.35-37)


41  t Amma ya ce musu, “Ƙaƙa za su ce Almasihu ɗan Dawuda ne?

42 Domin Dawuda da kansa a Zabura ya ce,
‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,
“Zauna a damana,

43  t Sai na sa ka take maƙiyanka.” ’

44 Dawuda ya ce shi Ubangiji ne. To, ƙaƙa zai zama ɗansa?”

Yesu Ya Fallashi Malaman Attaura

(Mat 23.1-36; Mar 12.38-40; Luka 11.37-54)


45 Ya ce wa almajiransa a gaban dukan jama'a, 46 t “Ku yi hankali da malaman Attaura, masu son yawo a cikin manyan riguna, masu so a gaishe su a kasuwa, masu son mafifitan mazaunai a majami'u, da mazaunan alfarma a wurin biki. 47 Su ne masu cin kayan matan da mazansu suka mutu, masu yin doguwar addu'a don ɓad da sawu. Su za a yi wa hukunci mafi tsanani.”

Luke 20

1 And it came to pass, on one of the days, as he was teaching the people in the temple, and preaching the gospel, there came upon him the chief priests and the scribes with the elders;2 and they spake, saying unto him, Tell us: By what authority doest thou these things? or who is he that gave thee this authority?3 And he answered and said unto them, I also will ask you a question; and tell me:4 The baptism of John, was it from heaven, or from men?5 And they reasoned with themselves, saying, If we shall say, From heaven; he will say, Why did ye not believe him?6 But if we shall say, From men; all the people will stone us: for they are persuaded that John was a prophet.7 And they answered, that they knew not whence it was.8 And Jesus said unto them, Neither tell I you by what authority I do these things.9 And he began to speak unto the people this parable: A man planted a vineyard, and let it out to husbandmen, and went into another country for a long time.10 And at the season he sent unto the husbandmen a servant, that they should give him of the fruit of the vineyard: but the husbandmen beat him, and sent him away empty.11 And he sent yet another servant: and him also they beat, and handled him shamefully, and sent him away empty.12 And he sent yet a third: and him also they wounded, and cast him forth.13 And the lord of the vineyard said, What shall I do? I will send my beloved son; it may be they will reverence him.14 But when the husbandmen saw him, they reasoned one with another, saying, This is the heir; let us kill him, that the inheritance may be ours.15 And they cast him forth out of the vineyard, and killed him. What therefore will the lord of the vineyard do unto them?16 He will come and destroy these husbandmen, and will give the vineyard unto others. And when they heard it, they said, God forbid.17 But he looked upon them, and said, What then is this that is written, The stone which the builders rejected, The same was made the head of the corner?

18 Every one that falleth on that stone shall be broken to pieces; but on whomsoever it shall fall, it will scatter him as dust.19 And the scribes and the chief priests sought to lay hands on him in that very hour; and they feared the people: for they perceived that he spake this parable against them.20 And they watched him, and sent forth spies, who feigned themselves to be righteous, that they might take hold of his speech, so as to deliver him up to the rule and to the authority of the governor.21 And they asked him, saying, Teacher, we know that thou sayest and teachest rightly, and acceptest not the person of any, but of a truth teachest the way of God:22 Is it lawful for us to give tribute unto Caesar, or not?23 But he perceived their craftiness, and said unto them,24 Show me a denarius. Whose image and superscription hath it? And they said, Caesar’s.25 And he said unto them, Then render unto Caesar the things that are Caesar’s, and unto God the things that are God’s.26 And they were not able to take hold of the saying before the people: and they marvelled at his answer, and held their peace.27 And there came to him certain of the Sadducees, they that say that there is no resurrection;28 and they asked him, saying, Teacher, Moses wrote unto us, that if a man’s brother die, having a wife, and he be childless, his brother should take the wife, and raise up seed unto his brother.29 There were therefore seven brethren: and the first took a wife, and died childless;30 and the second:31 and the third took her; and likewise the seven also left no children, and died.32 Afterward the woman also died.33 In the resurrection therefore whose wife of them shall she be? for the seven had her to wife.34 And Jesus said unto them, The sons of this world marry, and are given in marriage:35 but they that are accounted worthy to attain to that world, and the resurrection from the dead, neither marry, nor are given in marriage:36 for neither can they die any more: for they are equal unto the angels; and are sons of God, being sons of the resurrection.37 But that the dead are raised, even Moses showed, in the place concerning the Bush, when he calleth the Lord the God of Abraham, and the God of Isaac, and the God of Jacob.38 Now he is not the God of the dead, but of the living: for all live unto him.39 And certain of the scribes answering said, Teacher, thou hast well said.40 For they durst not any more ask him any question.41 And he said unto them, How say they that the Christ is David’s son?42 For David himself saith in the book of Psalms, The Lord said unto my Lord, Sit thou on my right hand,

43 Till I make thine enemies the footstool of thy feet.

44 David therefore calleth him Lord, and how is he his son?45 And in the hearing of all the people he said unto his disciples,46 Beware of the scribes, who desire to walk in long robes, and love salutations in the marketplaces, and chief seats in the synagogues, and chief places at feasts;47 who devour widows’ houses, and for a pretence make long prayers: these shall receive greater condemnation.