previous next

LUK 21

Sadaka wadda aka Saka

(Mar 12.41-44)

1  t Yesu ya ɗaga kai ya ga waɗansu masu arziki suna saka sadakarsu a baitulmalin Haikali. 2 Sai ya ga wata gajiyayyiya da mijinta ya mutu ta saka rabin kobo biyu a ciki. 3 Sai ya ce, “Hakika, ina gaya muku, abin da gajiyayyiya gwauruwan nan ta saka a ciki, ya fi na sauran duka.

4 t Domin duk waɗannan sun bayar daga yalwarsu ne, ita kuwa daga cikin rashinta ta ba da duk kuɗinta na abinci.”

Yesu Ya Faɗi irin Rushewar da za ta Sami Haikali

(Mat 24.1-2; Mar 13.1-2)


5 Waɗansu suna zancen Haikali, da yadda aka ƙawata shi da duwatsun alfarma da keɓaɓɓun kayan sadaka, sai ya ce,

6 t “In don waɗannan abubuwa da kuke kallo ne, ai, lokaci yana zuwa da ba wani dutsen da za a bari a nan a kan ɗan'uwansa da ba a baje shi ba.”

Alamu da Tsanance-tsanance

(Mat 24.3-14; Mar 13.3-13)


7 Sai suka tambaye shi suka ce, “Malam, a yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Wace alama kuma za a gani sa'ad da suke shirin aukuwa?” 8 t Sai ya ce, “Ku kula fa kada a ɓad da ku. Don mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa su ne ni, suna kuma cewa, ‘Lokaci ya yi kusa.’ To, kada ku bi su.

9 In kuma kun ji labarin yaƙe-yaƙe da hargitsi, kada ku firgita. Lalle ne wannan ya fara aukuwa, amma ƙarshen tukuna.”
10  t Sa'an nan ya ce musu, “Al'umma za ta tasar wa al'umma, mulki ya tasar wa mulki. 11 t Za a yi raurawar ƙasa manya manya, da kuma yunwa, da annoba a wurare dabam dabam. Za a kuma yi al'amura masu bantsoro da manyan alamu daga sama. 12 Amma kafin wannan duka, za su kama ku, su tsananta muku. Za su miƙa ku ga majami'u da kurkuku, su kuma kai ku a gaban sarakuna da mahukunta saboda sunana. 13 t Wannan zai zama muku hanyar ba da shaida. 14 t Saboda haka, sai ku ƙudura a ranku, a kan ba za ku damu da yadda za ku mai da jawabi ba. 15 t Domin ni ne zan ba ku ikon hurci, da kuma hikima wadda duk abokan adawarku, ba za su iya shanyewa ko musawa ba. 16 t Ko da iyayenku ma da 'yan'uwanku, da danginku, da abokanku, sai sun bāshe ku, su kuma sa a kashe waɗansunku. 17 t Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. 18 t Amma ba gashin kanku ko ɗaya da zai yi ciwo.

19 t Jurewarku ce za ta fisshe ku.”

Yesu ya Faɗi irin Ribɗewa da za ta Sami Urushalima

(Mat 24.15-28; Mar 13.14-23)


20  t “Sa'ad da kuka ga rundunonin yaƙi sun kewaye Urushalima, sa'an nan ku tabbata ana kusan ribɗe ta. 21 t Sa'an nan waɗanda suke a ƙasar Yahudiya, su gudu su shiga duwatsu, na birni su fice, na ƙauye kuma kada su shiga birni. 22 t Saboda lokacin sakamako ne, don a cika duk abin da yake rubuce. 23 Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci! Don matsanancin ƙunci zai saukar wa ƙasar, da kuma fushin Allah ga jama'an nan.

24 t Za a kashe waɗansu da kaifin takobi, a kuma kakkama waɗansu a kai su bauta zuwa ƙasashen al'ummai duka. Al'ummai kuma za su tattake Urushalima, har ya zuwa cikar zamaninsu.”

Komowar Ɗan Mutum

(Mat 24.29-31; Mar 13.24-27)


25  t “Za a kuma ga alamu a rana, da wata, da taurari, a duniya kuma al'ummai su matsu ƙwarai, suna shan damuwa saboda ƙugin teku da na raƙuman ruwa. 26 t Mutane za su suma don tsoro, da kuma fargaban al'amuran da suke aukuwa ga duniya, don za a girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama. 27 t A sa'an nan ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa a cikin gajimare da iko da ɗaukaka mai yawa.

28 t Sa'ad da waɗannan al'amura suka fara aukuwa, sai ku ɗaga kai ku dubi sama, domin fansarku ta yi kusa.”

Aya a kan Itacen Ɓaure

(Mat 24.32-35; Mar 13.28-31)


29 Sai ya ba su wani misali, ya ce, “Ku dubi itacen ɓaure da dukan itatuwa, 30 da zarar sun fara toho, kuna gani, ku da kanku kun san damuna ta yi kusa ke nan. 31 t Haka kuma sa'ad da kuka ga waɗannan al'amura suna aukuwa, ku sani Mulkin Allah ya gabato. 32 t Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba, sai duk abubuwan nan sun auku.

33 t Sararin sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”

Gargaɗi a Zauna a Faɗake


34  t “Ku kula da kanku fa, kada zuciyarku ta zarme da yawan shaye-shaye da buguwa, da kuma taraddadin wannan duniya, har ba labari ranan nan ta mamaye ku kamar tarko. 35 Don haka, za ta auka wa mazaunan duniya duk, kowa da kowa.

36 t Koyaushe ku zauna a faɗake, kuna addu'a ku sami ikon tsere wa dukan waɗannan al'amura da za su auku, ku kuma tsaya a gaban Ɗan Mutum.”
37  t Kullum da rana yakan koyar a Haikali, da dare kuma yakan fita ya kwana a dutsen da ake ce da shi Dutsen Zaitun. 38 t Da sassafe kuma dukan mutane sukan zo wurinsa a Haikali su saurare shi.

Luke 21

1 And he looked up, and saw the rich men that were casting their gifts into the treasury.2 And he saw a certain poor widow casting in thither two mites.3 And he said, Of a truth I say unto you, This poor widow cast in more than they all:4 for all these did of their superfluity cast in unto the gifts; but she of her want did cast in all the living that she had.5 And as some spake of the temple, how it was adorned with goodly stones and offerings, he said,6 As for these things which ye behold, the days will come, in which there shall not be left here one stone upon another, that shall not be thrown down.7 And they asked him, saying, Teacher, when therefore shall these things be? and what shall be the sign when these things are about to come to pass?8 And he said, Take heed that ye be not led astray: for many shall come in my name, saying, I am he; and, The time is at hand: go ye not after them.9 And when ye shall hear of wars and tumults, be not terrified: for these things must needs come to pass first; but the end is not immediately.10 Then said he unto them, Nation shall rise against nation, and kingdom against kingdom;11 and there shall be great earthquakes, and in divers places famines and pestilences; and there shall be terrors and great signs from heaven.12 But before all these things, they shall lay their hands on you, and shall persecute you, delivering you up to the synagogues and prisons, bringing you before kings and governors for my name’s sake.13 It shall turn out unto you for a testimony.14 Settle it therefore in your hearts, not to meditate beforehand how to answer:15 for I will give you a mouth and wisdom, which all your adversaries shall not be able to withstand or to gainsay.16 But ye shall be delivered up even by parents, and brethren, and kinsfolk, and friends; and some of you shall they cause to be put to death.17 And ye shall be hated of all men for my name’s sake.18 And not a hair of your head shall perish.19 In your patience ye shall win your souls.20 But when ye see Jerusalem compassed with armies, then know that her desolation is at hand.21 Then let them that are in Judaea flee unto the mountains; and let them that are in the midst of her depart out; and let not them that are in the country enter therein.22 For these are days of vengeance, that all things which are written may be fulfilled.23 Woe unto them that are with child and to them that give suck in those days! for there shall be great distress upon the land, and wrath unto this people.24 And they shall fall by the edge of the sword, and shall be led captive into all the nations: and Jerusalem shall be trodden down of the Gentiles, until the times of the Gentiles be fulfilled.25 And there shall be signs in sun and moon and stars; and upon the earth distress of nations, in perplexity for the roaring of the sea and the billows;26 men fainting for fear, and for expectation of the things which are coming on the world: for the powers of the heavens shall be shaken.27 And then shall they see the Son of man coming in a cloud with power and great glory.28 But when these things begin to come to pass, look up, and lift up your heads; because your redemption draweth nigh.29 And he spake to them a parable: Behold the fig tree, and all the trees:30 when they now shoot forth, ye see it and know of your own selves that the summer is now nigh.31 Even so ye also, when ye see these things coming to pass, know ye that the kingdom of God is nigh.32 Verily I say unto you, This generation shall not pass away, till all things be accomplished.33 Heaven and earth shall pass away: but my words shall not pass away.34 But take heed to yourselves, lest haply your hearts be overcharged with surfeiting, and drunkenness, and cares of this life, and that day come on you suddenly as a snare:35 for so shall it come upon all them that dwell on the face of all the earth.36 But watch ye at every season, making supplication, that ye may prevail to escape all these things that shall come to pass, and to stand before the Son of man.37 And every day he was teaching in the temple; and every night he went out, and lodged in the mount that is called Olivet.38 And all the people came early in the morning to him in the temple, to hear him.