previous next

LUK 5

An Kama Kifi Jingim

(Mat 4.18-22; Mar 1.16-20)

1  t Wata rana taro suna matsarsa domin su ji Maganar Allah, shi kuwa yana tsaye a bakin Tekun Janisarata, 2 sai ya hangi ƙananan jirage biyu a bakin tekun, masuntan kuwa sun fita daga cikinsu, suna wankin tarunansu. 3 t Sai ya shiga ɗaya jirgin, wanda yake na Bitrus, ya roƙe shi ya ɗan zakuɗa da jirgin daga bakin gaci. Sai ya zauna ya yi ta koya wa taro masu yawa daga jirgin. 4 t Da ya gama magana, ya ce wa Bitrus, “Zakuɗa da jirgin zuwa wuri mai zurfi, ku saki tarunanku, ku janyo kifi.” 5 t Bitrus ya amsa masa ya ce, “Ya Maigida, dare farai muna wahala, ba mu kama kome ba, amma tun da ka yi magana zan saki tarunan.” 6 t Da suka yi haka kuwa, suka kamo kifi jingim, har ma tarunansu suka fara kecewa. 7 Sai suka yafato abokan aikinsu a ɗaya jirgin su zo su taimake su. Suka kuwa zo, suka ciccika jiragen nan duka biyu kamar sa nutse. 8 t Da Bitrus ya ga haka, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce. “Ya Ubangiji, wane ni da za ka tsaya kusa da ni, domin ni mutum ne mai zunubi.” 9 Domin shi da waɗanda suke tare da shi duka, mamaki ya kama su saboda kifin nan da suka janyo, 10 t haka ma Yakubu da Yahaya 'ya'yan Zabadi, abokan sabgar Bitrus. Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Kada ka ji tsoro. Nan gaba mutane za ka riƙa kamowa.”

11 t Da suka kawo jiragensu gaci, suka bar kome duka suka bi shi.

Yesu Ya Warkar da Kuturu

(Mat 8.1-4; Mar 1.40-45)


12  t Wata rana Yesu na ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa ya zo. Da ya ga Yesu ya fāɗi a gabansa, ya roƙe shi ya ce, “Ya Ubangiji, in dai ka yarda kana da ikon tsarkake ni.” 13 Sai Yesu ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan take sai kuturtar ta rabu da shi. 14 t Yesu ya kwaɓe shi kada ya gaya wa kowa, ya ce, “Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi hadaya saboda tsarkakewarka, domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.” 15 t Amma duk da haka labarinsa sai ƙara yaɗuwa yake yi, har taro masu yawan gaske suka yi ta zuwa domin su saurare shi, a kuma warkar da su daga rashin lafiyarsu.

16 t Amma shi, sai ya riƙa keɓanta a wuraren da ba kowa, yana addu'a.

Yesu ya Warkar da Shanyayye

(Mat 9.1-8; Mar 2.1-12)


17  t Wata rana na koyarwa, waɗansu Farisiyawa kuwa da masanan Attaura da suka fito daga kowane gari na ƙasar Galili, da na ƙasar Yahudiya, daga kuma Urushalima, suna nan a zaune. Ikon Ubangiji na warkarwa kuwa yana nan. 18 Sai ga waɗansu mutane ɗauke da wani shanyayye a kan shimfiɗa, suna ƙoƙari su shigar da shi su ajiye shi a gaban Yesu. 19 Da suka kasa samun hanyar shigar da shi saboda taro, suka hau a kan soron, suka zura shi ta tsakanin rufin soron duk da shimfiɗarsa, suka ajiye shi a tsakiyar jama'a a gaban Yesu. 20 t Da Yesu ya ga bangaskiyarsu sai ya ce, “Malam, an gafarta maka zunubanka.” 21 t Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka fara wuswasi cewa, “Wane ne wannan da yake maganar saɓo? Wa yake iya gafarta zunubi banda Allah shi kaɗai?” 22 Da Yesu ya gane wuswasinsu, ya amsa musu ya ce, “Don me kuke wuswasi haka a zuciyarku? 23 Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi, ka yi tafiya’? 24 t Amma domin ku sakankance Ɗan Mutum na da ikon gafarta zunubi a duniya”, sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi, ka ɗauki shimfiɗarka, ka tafi gida.” 25 Nan take ya tashi a gaban idonsu, ya ɗauki abin kwanciyarsa, ya tafi gida, yana ɗaukaka Allah.

26 t Sai suka yi mamaki matuƙa, su duka, suka yi ta ɗaukaka Allah, tsoro kuma ya kama su, suka ce, “Yau mun ga al'ajabai!”

Kiran Lawi

(Mat 9.9-13; Mar 2.13-17)


27  t Bayan haka ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, a zaune, yana aiki a wurin karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.”

28 t Sai ya bar kome duka, ya tashi ya bi shi.
29  t Sai Lawi ya yi masa ƙasaitacciyar liyafa a gidansa, akwai kuwa taron masu karɓar haraji da waɗansu mutane suna ci tare da su. 30 t Sai Farisiyawa da malamansu na Attaura suka yi wa almajiransa gunaguni suka ce, “Don me kuke ci kuke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?” 31 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da magani, sai dai marasa lafiya.

32 t Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai dai masu zunubi, su tuba.”

Tambaya a kan Azumi

(Mat 9.14-17; Mar 2.18-22)


33  t Sai suka ce masa, “Almajiran Yahaya suna azumi a kai a kai, suna kuma addu'a, haka kuma almajiran Farisiyawa, amma naka suna ci suna sha.” 34 t Sai Yesu ya ce musu, “Wato kwa iya sa abokan ango su yi azumi tun angon yana tare da su? 35 t Ai, lokaci na zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi.” 36 Ya kuma yi musu misali, ya ce, “Ba mai tsage ƙyalle a jikin sabuwar tufa ya yi maho a tsohuwar tufa da shi. In ma an yi, ai, sai ya kece sabuwar tufar, sabon ƙyallen kuma ba zai dace da tsohuwar tufar ba. 37 Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ma an ɗura, sai sabon ruwan inabin ya fasa salkunan, ya zube, salkunan kuma su lalace. 38 Sabon ruwan inabi, ai, sai sababbin salkuna. 39 Ba wanda zai so shan sabon ruwan inabin bayan ya sha tsohon, don ya ce, ‘Ai, tsohon yana da kyau.’ ”

Luke 5

1 Now it came to pass, while the multitude pressed upon him and heard the word of God, that he was standing by the lake of Gennesaret;2 and he saw two boats standing by the lake: but the fishermen had gone out of them, and were washing their nets.3 And he entered into one of the boats, which was Simon’s, and asked him to put out a little from the land. And he sat down and taught the multitudes out of the boat.4 And when he had left speaking, he said unto Simon, Put out into the deep, and let down your nets for a draught.5 And Simon answered and said, Master, we toiled all night, and took nothing: but at thy word I will let down the nets.6 And when they had done this, they inclosed a great multitude of fishes; and their nets were breaking;7 and they beckoned unto their partners in the other boat, that they should come and help them. And they came, and filled both the boats, so that they began to sink.8 But Simon Peter, when he saw it, fell down at Jesus’ knees, saying, Depart from me; for I am a sinful man, O Lord.9 For he was amazed, and all that were with him, at the draught of the fishes which they had taken;10 and so were also James and John, sons of Zebedee, who were partners with Simon. And Jesus said unto Simon, Fear not; from henceforth thou shalt catch men.11 And when they had brought their boats to land, they left all, and followed him.12 And it came to pass, while he was in one of the cities, behold, a man full of leprosy: and when he saw Jesus, he fell on his face, and besought him, saying, Lord, if thou wilt, thou canst make me clean.13 And he stretched forth his hand, and touched him, saying, I will; be thou made clean. And straightway the leprosy departed from him.14 And he charged him to tell no man: but go thy way, and show thyself to the priest, and offer for thy cleansing, according as Moses commanded, for a testimony unto them.15 But so much the more went abroad the report concerning him: and great multitudes came together to hear, and to be healed of their infirmities.16 But he withdrew himself in the deserts, and prayed.17 And it came to pass on one of those days, that he was teaching; and there were Pharisees and doctors of the law sitting by, who were come out of every village of Galilee and Judaea and Jerusalem: and the power of the Lord was with him to heal.18 And behold, men bring on a bed a man that was palsied: and they sought to bring him in, and to lay him before him.19 And not finding by what way they might bring him in because of the multitude, they went up to the housetop, and let him down through the tiles with his couch into the midst before Jesus.20 And seeing their faith, he said, Man, thy sins are forgiven thee.21 And the scribes and the Pharisees began to reason, saying, Who is this that speaketh blasphemies? Who can forgive sins, but God alone?22 But Jesus perceiving their reasonings, answered and said unto them, Why reason ye in your hearts?23 Which is easier, to say, Thy sins are forgiven thee; or to say, Arise and walk?24 But that ye may know that the Son of man hath authority on earth to forgive sins (he said unto him that was palsied), I say unto thee, Arise, and take up thy couch, and go unto thy house.25 And immediately he rose up before them, and took up that whereon he lay, and departed to his house, glorifying God.26 And amazement took hold on all, and they glorified God; and they were filled with fear, saying, We have seen strange things to-day.27 And after these things he went forth, and beheld a publican, named Levi, sitting at the place of toll, and said unto him, Follow me.28 And he forsook all, and rose up and followed him.29 And Levi made him a great feast in his house: and there was a great multitude of publicans and of others that were sitting at meat with them.30 And the Pharisees and their scribes murmured against his disciples, saying, Why do ye eat and drink with the publicans and sinners?31 And Jesus answering said unto them, They that are in health have no need of a physician; but they that are sick.32 I am not come to call the righteous but sinners to repentance.33 And they said unto him, The disciples of John fast often, and make supplications; likewise also the disciples of the Pharisees; but thine eat and drink.34 And Jesus said unto them, Can ye make the sons of the bride-chamber fast, while the bridegroom is with them?35 But the days will come; and when the bridegroom shall be taken away from them, then will they fast in those days.36 And he spake also a parable unto them: No man rendeth a piece from a new garment and putteth it upon an old garment; else he will rend the new, and also the piece from the new will not agree with the old.37 And no man putteth new wine into old wine-skins; else the new wine will burst the skins, and itself will be spilled, and the skins will perish.38 But new wine must be put into fresh wine-skins.39 And no man having drunk old wine desireth new; for he saith, The old is good.