LUK 6
Almajirai suna Zagar Alkama a Ran Asabar
(Mat 12.1-8; Mar 2.23-28)
1 t Wata rana ran Asabar, yana ratsa gonakin alkama, sai almajiransa suka zāgi alkamar, suna murtsukewa suna ci. 2 t Sai waɗansu Farisiyawa suka ce, “Don me kuke yin abin da bai halatta a yi ba a ran Asabar?” 3 t Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba sa'ad da ya ji yunwa, shi da abokan tafiyarsa? 4 t Yadda ya shiga masujadar Allah, ya ɗauki keɓaɓɓiyar gurasan nan ya ci, har ma ya ba abokan tafiyarsa, wadda ba ta halatta kowa ya ci ba, sai firistoci kaɗai?”
5 t Sai ya ce musu, “Ai, Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabar.”Mai Shanyayyen Hannu
(Mat 12.9-14; Mar 3.1-6)
6 t A wata Asabar kuma ya shiga majami'a, yana koyarwa. Akwai kuwa wani mutum a ciki wanda hannunsa na dama ya shanye. 7 t Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka yi haƙwansa su ga ko yā warkar a ran Asabar, don su samu su kai ƙararsa. 8 t Shi kuwa ya san tunaninsu. Sai ya ce wa mai shanyayyen hannun, “Taso, ka tsaya nan tsakiya.” Sai ya tashi, ya tsaya a wurin. 9 Yesu ya ce musu, “Ina yi muku tambaya. Ya halatta ran Asabar a yi alheri ko mugunta? A ceci rai, ko a hallaka shi?” 10 Sai ya duddube su duke, ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Ya miƙa, hannunsa kuwa sai ya koma lafiyayye.
11 t Sai suka husata ƙwarai, suka yi shawarar abin da za su yi wa Yesu.Yesu Ya Zaɓi Almajirai Sha Biyu
(Mat 10.1-4; Mar 3.13-19)
12 t A kwanakin nan Yesu ya fita ya hau dutse domin yin addu'a. Dare farai yana addu'a ga Allah. 13 t Da gari ya waye ya kira almajiransa, ya zaɓi goma sha biyu a cikinsu, ya ce da su manzanni. 14 Su ne Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, da Yakubu, da Yahaya, da Filibus, da Bartalamawas, 15 t da Matiyu, da Toma, da Yakubu ɗan Halfa, da Saminu, wanda ake ce da shi Zaloti,
16 da Yahuza ɗan Yakubu, da kuma Yahuza Iskariyoti, wanda ya zama maci amana.Yesu Ya Hidimta wa Mutane Masu Yawa
(Mat 4.23-25)
17 t Sai ya gangaro tare da su, ya tsaya a wani sarari. Ga kuwa babban taro masu binsa, da kuma taro masu yawan gaske daga duk ƙasar Yahudiya da Urushalima, da kuma yankin ƙasar Taya da Sidon da yake bakin bahar, waɗanda suka zo su saurare shi, a kuma warkar da cuce-cucensu. 18 Waɗanda kuma baƙaƙen aljannu suke wahalshe su, aka warkar da su.
19 t Duk taron suka nema su taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka.Albarka da La'ana
(Mat 5.1-12)
20 t Sai ya ɗaga kai, ya dubi almajiransa, ya ce,
“Albarka tā tabbata gare ku, ku matalauta, domin Mulkin Allah naku ne.
21 t “Albarka tā tabbata gare ku, ku da kuke mayunwata a yanzu, domin za a ƙosar da kuke.
“Albarka tā tabbata gare ku, ku da kuke kuka a yanzu domin za ku yi dariya.
22 t “Albarka tā tabbata a gare ku sa'ad da mutane suka ƙi ku, suka kuma ware ku, suka zage ku, suka yi ƙyamar sunanku saboda Ɗan Mutum.
23 t Ku yi farin ciki a wannan rana, ku yi tsalle don murna, domin ga shi, sakamakonku mai yawa ne a Sama. Haka kakanninsu ma suka yi wa annabawa.
24 t “Amma kaitonku, ku masu arziki domin kun riga kun sami taku ta'aziyya.
25 t “Kaitonku, ku da kuke ƙosassu a yanzu, don za ku ji yunwa. “Kaitonku, ku masu dariya a yanzu, don za ku yi baƙin ciki, ku yi kuka.
26 t “Kaitonku in kowa na yabonku. Haka kakanninsu ma suka yi wa annabawan ƙarya.”Ƙaunar Magabta
(Mat 5.38-48; 7.12)
27 t “Amma ina gaya muku, ku masu sauraro, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa maƙiyanku alheri. 28 t Ku sa wa masu zaginku albarka. Masu wulakanta ku kuma, ku yi musu addu'a. 29 Wanda ya mare ka a kunci ɗaya, juya masa ɗaya kuncin kuma. Wanda ya ƙwace maka mayafi, kada ka hana masa taguwarka ma. 30 t Duk wanda ya roƙe ka, ka ba shi. Wanda kuma ya ƙwace maka kaya, kada ka neme shi.
31 t Yadda kuke so mutane su yi muku, to, ku yi musu haka.
32 t In masoyanku kawai kuke ƙauna wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma suna ƙaunar masoyansu. 33 In kuma sai waɗanda suke muku alheri kawai kuke yi wa alheri, wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma haka suke yi. 34 In kuma sai ga waɗanda kuke tsammani za su biya ku ne kuke ba da rance, wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma, sukan ba masu zunubi rance, don a biya su daidai. 35 t Amma ku ƙaunaci magabtanku, kuna yi musu alheri. Ku ba da rance, kada kuwa ku tsammaci biya. Ladanku kuma zai yi yawa, za ku kuma zama 'ya'yan Maɗaukaki, domin shi mai alheri ne ga masu butulci da kuma mugaye.
36 t Ku kasance masu tausayi kamar yadda Ubanku yake mai tausayi.”Kada ku Ɗora wa Kowa Laifi
(Mat 7.1-5)
37 t “Kada ku ɗora wa kowa laifi, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yi wa kowa mugun zato, ku ma ba za a yi muku ba. Ku yafe, ku ma sai a yafe muku.
38 t Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har ya yi tozo, har yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku.”
39 t Ya kuma ba su wani misali ya ce, “Makaho yana iya yi wa makaho jagora? Ashe, dukansu biyu ba sai su fāɗa a rami ba? 40 t Almajiri ba ya fin malaminsa. Amma kowa aka karantar da shi sosai, sai ya zama kamar malaminsa. 41 Don me kake duban ɗan hakin da yake a idon ɗan'uwanka, amma gungumen da yake a naka ido ba ka kula ba?
42 Ƙaƙa kuma za ka iya ce wa ɗan'uwanka, ‘Ya ɗan'uwana, bari in cire maka ɗan hakin da yake a idonka,’ alhali kuwa kai kanka ba ka ga gungumen da yake a naka ido ba? Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake a idonka tukuna sa'an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin da yake a idon ɗan'uwanka.”Akan Gane Itace ta 'Ya'yansa
(Mat 7.16-20; 12.33-35)
43 “Ba kyakkyawan itace da yake haifar munanan 'ya'ya, ba kuma mummunan itace da yake haifar kyawawan 'ya'ya. 44 t Domin kowane itace da irin 'ya'yansa ake saninsa. Ai, ba a ɗiban ɓaure a jikin ƙaya, ko kuwa inabi a jikin sarƙaƙƙiya.
45 t Mutumin kirki kam ta kyakkyawar taskar zuciyarsa yakan yi abin kirki, mugu kuwa ta mummunar taskar zuciyarsa yakan yi mugun abu. Ai, abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa.”Kafa Harsashin Gini Iri Biyu
(Mat 7.24-27)
46 t “Don me kuke kirana, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ba kwa kuwa yin abin da na faɗa muku? 47 t Duk mai zuwa wurina, yake jin maganata, yake kuma aikata ta, zan nuna muku kwatancinsa. 48 Kamar mutum yake mai gina gida, wanda ya yi haƙa mai zurfi, har ya sa harsashin ginin a kan fā. Da aka yi rigyawa, sai ruwan kogi ya bugi gidan, amma bai iya girgiza shi ba, saboda an gina shi da aminci. 49 Amma wanda ya ji maganata, bai kuwa aikata ba, kamar mutum yake wanda ya gina gida a kan turɓaya, ba harsashi. Ruwan kogi ya buge shi, nan da nan ya rushe. Wannan gida ya yi mummunar ragargajewa!”
Luke 6
1 Now it came to pass on a sabbath, that he was going through the grainfields; and his disciples plucked the ears, and did eat, rubbing them in their hands.2 But certain of the Pharisees said, Why do ye that which it is not lawful to do on the sabbath day?3 And Jesus answering them said, Have ye not read even this, what David did, when he was hungry, he, and they that were with him;4 how he entered into the house of God, and took and ate the showbread, and gave also to them that were with him; which it is not lawful to eat save for the priests alone?5 And he said unto them, The Son of man is lord of the sabbath.6 And it came to pass on another sabbath, that he entered into the synagogue and taught: and there was a man there, and his right hand was withered.7 And the scribes and the Pharisees watched him, whether he would heal on the sabbath; that they might find how to accuse him.8 But he knew their thoughts; and he said to the man that had his hand withered, Rise up, and stand forth in the midst. And he arose and stood forth.9 And Jesus said unto them, I ask you, Is it lawful on the sabbath to do good, or to do harm? to save a life, or to destroy it?10 And he looked round about on them all, and said unto him, Stretch forth thy hand. And he did so: and his hand was restored.11 But they were filled with madness; and communed one with another what they might do to Jesus.12 And it came to pass in these days, that he went out into the mountain to pray; and he continued all night in prayer to God.13 And when it was day, he called his disciples; and he chose from them twelve, whom also he named apostles:14 Simon, whom he also named Peter, and Andrew his brother, and James and John, and Philip and Bartholomew,15 and Matthew and Thomas, and James the son of Alphaeus, and Simon who was called the Zealot,16 and Judas the son of James, and Judas Iscariot, who became a traitor;17 and he came down with them, and stood on a level place, and a great multitude of his disciples, and a great number of the people from all Judaea and Jerusalem, and the sea coast of Tyre and Sidon, who came to hear him, and to be healed of their diseases;18 and they that were troubled with unclean spirits were healed.19 And all the multitude sought to touch him; for power came forth from him, and healed them all.20 And he lifted up his eyes on his disciples, and said, Blessed are ye poor: for yours is the kingdom of God.21 Blessed are ye that hunger now: for ye shall be filled. Blessed are ye that weep now: for ye shall laugh.22 Blessed are ye, when men shall hate you, and when they shall separate you from their company, and reproach you, and cast out your name as evil, for the Son of man’s sake.23 Rejoice in that day, and leap for joy: for behold, your reward is great in heaven; for in the same manner did their fathers unto the prophets.24 But woe unto you that are rich! for ye have received your consolation.25 Woe unto you, ye that are full now! for ye shall hunger. Woe unto you, ye that laugh now! for ye shall mourn and weep.26 Woe unto you, when all men shall speak well of you! for in the same manner did their fathers to the false prophets.27 But I say unto you that hear, Love your enemies, do good to them that hate you,28 bless them that curse you, pray for them that despitefully use you.29 To him that smiteth thee on the one cheek offer also the other; and from him that taketh away thy cloak withhold not thy coat also.30 Give to every one that asketh thee; and of him that taketh away thy goods ask them not again.31 And as ye would that men should do to you, do ye also to them likewise.32 And if ye love them that love you, what thank have ye? for even sinners love those that love them.33 And if ye do good to them that do good to you, what thank have ye? for even sinners do the same.34 And if ye lend to them of whom ye hope to receive, what thank have ye? even sinners lend to sinners, to receive again as much.35 But love your enemies, and do them good, and lend, never despairing; and your reward shall be great, and ye shall be sons of the Most High: for he is kind toward the unthankful and evil.36 Be ye merciful, even as your Father is merciful.37 And judge not, and ye shall not be judged: and condemn not, and ye shall not be condemned: release, and ye shall be released:38 give, and it shall be given unto you; good measure, pressed down, shaken together, running over, shall they give into your bosom. For with what measure ye mete it shall be measured to you again.39 And he spake also a parable unto them, Can the blind guide the blind? shall they not both fall into a pit?40 The disciple is not above his teacher: but every one when he is perfected shall be as his teacher.41 And why beholdest thou the mote that is in thy brother’s eye, but considerest not the beam that is in thine own eye?42 Or how canst thou say to thy brother, Brother, let me cast out the mote that is in thine eye, when thou thyself beholdest not the beam that is in thine own eye? Thou hypocrite, cast out first the beam out of thine own eye, and then shalt thou see clearly to cast out the mote that is in thy brother’s eye.43 For there is no good tree that bringeth forth corrupt fruit; nor again a corrupt tree that bringeth forth good fruit.44 For each tree is known by its own fruit. For of thorns men do not gather figs, nor of a bramble bush gather they grapes.45 The good man out of the good treasure of his heart bringeth forth that which is good; and the evil man out of the evil treasure bringeth forth that which is evil: for out of the abundance of the heart his mouth speaketh.46 And why call ye me, Lord, Lord, and do not the things which I say?47 Every one that cometh unto me, and heareth my words, and doeth them, I will show you to whom he is like:48 he is like a man building a house, who digged and went deep, and laid a foundation upon the rock: and when a flood arose, the stream brake against that house, and could not shake it: because it had been well builded.49 But he that heareth, and doeth not, is like a man that built a house upon the earth without a foundation; against which the stream brake, and straightway it fell in; and the ruin of that house was great.