previous next

LUK 7

Yesu Ya Warkar da Bawan Wani Jarumi

(Mat 8.5-13)

1  t Bayan da Yesu ya ƙare jawabinsa duka a gaban jama'a, ya shiga Kafarnahum. 2 To, sai bawan wani jarumi, wanda Ubangijinsa yake jin daɗinsa, ya yi rashin lafiya, har ya kai ga bakin mutuwa. 3 Da jarumin ɗin ya ji labarin Yesu, sai ya aiki waɗansu shugabannin Yahudawa wurinsa, su roƙe shi ya zo ya warkar da bawa nasa. 4 Da suka isa wurin Yesu sai suka roƙe shi ƙwarai suka ce, “Ai, ya cancanci a yi masa haka, 5 don yana ƙaunar jama'armu, shi ne ma ya gina mana majami'armu.” 6 Sai Yesu ya tafi tare da su. Da ya matso kusa da gidan, sai jarumin ɗin ya aiki aminansa wurinsa su ce masa, “Ya Ubangiji, kada ka wahalar da kanka. Ban ma isa har ka zo gidana ba. 7 t Shi ya sa ban ga ma na isa in zo wurinka ba, amma kă yi magana kawai, yarona kuwa sai ya warke. 8 Don ni ma a hannun wani nake, da kuma soja a hannuna, in ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai ya je, wani kuwa in ce masa, ‘Zo,’ sai ya zo, in ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai ya yi.” 9 Da Yesu ya ji haka, ya yi mamakinsa, ya kuma juya ya ce wa taron da suke biye da shi, “Ina gaya muku, ko a cikin Isra'ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba.”

10 Da waɗanda aka aika suka koma gidan, suka sami bawan garau.

Yesu Ya Tā da Ɗan Mace wadda Mijinta Ya Mutu


11 Ba da daɗewa ba, Yesu ya tafi wani gari, wai shi Nayin, almajiransa da kuma babban taro suka tafi da shi. 12 Ya kusaci ƙofar garin ke nan, sai ga wani mamaci ana ɗauke da shi, shi kaɗai ne wajen uwa tasa, mijinta kuwa ya mutu. Mutanen gari da yawa sun rako ta. 13 t Da Ubangiji ya gan ta, ya ji tausayinta, ya kuma ce mata, “Daina kuka.” 14 t Sa'an nan ya matso, ya taɓa makarar, masu ɗauka kuma suka tsaya cik. Sai Yesu ya ce, “Samari, na ce maka ka tashi.” 15 Mamacin ya tashi zaune, ya fara magana. Yesu kuwa ya ba da shi ga uwa tasa. 16 t Sai tsoro ya kama su duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Lalle, wani annabi mai girma ya bayyana a cikinmu,” da kuma, “Allah ya kula da jama'arsa.”

17 t Wannan labarin nasa kuwa ya bazu a dukan ƙasar Yahudiya da kewayenta.

'Yan Saƙo daga Yahaya Maibaftisma

(Mat 11.2-19)


18  t Sai almajiran Yahaya suka gaya masa dukan abubuwan nan. 19 Sai Yahaya ya kira almajiransa biyu, ya aike su gun Ubangiji yana tambaya, “Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?” 20 Da mutanen nan suka isa wurinsa, suka ce, “Yahaya Maibaftisma ne ya aiko mu gare ka, yana tambaya, ‘Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?’ ” 21 t Nan take Yesu ya warkar da mutane da yawa daga rashin lafiyarsu da cuce-cucensu da kuma baƙaƙen aljannu. Makafi da yawa kuma ya yi musu baiwar gani. 22 t Sai ya amsa musu ya ce, “Ku je ku gaya wa Yahaya abin da kuka ji da abin da kuka gani. Makafi na samun gani, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta bishara.

23 Albarka tā tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni.”
24 Baya jakadun Yahaya sun tafi, sai Yesu ya fara yi wa taro maganar Yahaya, ya ce, “Kallon me kuka je yi a jeji? Kyauron da iska take kaɗawa? 25 To, kallon me kuka je yi? Wani mai adon alharini? Ai kuwa, masu adon gaske, masu zaman annashuwa, a fāda suke. 26 t To, kallon me kuka je yi? Annabi? Hakika, ina gaya muku, har ya fi annabi nesa.

27 t Wannan shi ne wanda labarinsa yake rubuce cewa,
‘Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba,
Wanda zai shirya maka hanya gabaninka.’
28  t Ina gaya muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yahaya girma. Duk da haka wanda ya fi ƙasƙanta a Mulkin Allah ya fi shi.” 29 t Da duk jama'a da masu karɓar haraji suka ji haka, suka tabbata Allah mai adalci ne, aka yi musu baftisma da baftismar Yahaya.

30 t Amma Farisiyawa da masanan Attaura suka shure abin da Allah yake nufinsu da shi, da yake sun ƙi ya yi musu baftisma.
31 “To, da me zan kwatanta mutanen zamanin nan? Waɗanne iri ne su?

32 Kamar yara suke da suke zaune a bakin kasuwa, suna kiran juna, suna cewa,
‘Mun busa muku sarewa, ba ku yi rawa ba,
Mun yi makoki, ba ku yi kuka ba.’
33  t Ga shi, Yahaya Maibaftisma ya zo, ba ya cin gurasa, ba ya shan ruwan inabi, amma kuna cewa, ‘Ai, yana da iska.’ 34 t Ga Ɗan Mutum ya zo, yana ci yana sha, kuna kuma cewa, ‘Ga mai haɗama, mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi!’

35 Duk da haka hikimar Allah, ta dukkan aikinta ne ake tabbatar da gaskiya tata.”

Yesu a Gidan Saminu Bafarisiye


36 Wani Bafarisiye ya kira shi cin abinci. Sai ya shiga gidan Bafarisiyen, ya ƙishingiɗa wurin cin abincin. 37 Sai ga wata matar garin, mai zunubi, da ta ji Yesu na cin abinci a gidan Bafarisiyen, ta kawo wani ɗan tandu na man ƙanshi, 38 ta tsaya a bayansa a wajen ƙafafunsa, tana kuka. Sai hawayenta ya fara zuba a ƙafafunsa, ta goge su da gashinta, ta yi ta sumbantarsu, ta shafa musu man ƙanshin. 39 t To, da Bafarisiyen da ya kira shi ya ga haka, sai ya ce a ransa, “Da mutumin nan annabi ne, da ya san ko wace ce, da kuma ko wace irin mace ce wannan da yake taɓa shi, don mai zunubi ce.” 40 Yesu ya amsa ya ce, “Saminu, ina da magana da kai.” Sai shi kuma ya ce, “Malam, sai ka faɗa.” 41 Yesu ya ce, “Wani yana bin mutum biyu bashi, ɗaya dinari ɗari biyar, ɗayan kuma hamsin. 42 Da suka gagara biya, sai ya yafe musu dukansu biyu. To, a cikinsu wa zai fi ƙaunarsa?” 43 Saminu ya amsa masa ya ce, “A ganina, wanda ya yafe wa mai yawa.” Sai ya ce masa “Ka faɗa daidai.” 44 t Da ya waiwaya wajen matar, ya ce wa Saminu. “Ka ga matan nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwan wanke ƙafa ba, amma ita ta zub da hawayenta a ƙafafuna, ta kuma goge su da gashinta. 45 t Kai ba ka sumbance ni ba, ita kuwa, tun shigowata nan ba ta daina sumbantar ƙafafuna ba. 46 t Ba ka shafa mini mai a ka ba, amma ita ta shafa man ƙanshi a ƙafafuna. 47 Saboda haka ina gaya maka, zunubanta masu yawan nan duk an gafarta mata, domin ta yi ƙauna mai yawa. Wanda aka gafarta wa kaɗan kuwa, ƙauna kaɗan yake yi.” 48 t Sai ya ce mata, “An gafarta miki zunubanki.” 49 Masu ci tare da shi kuwa suka fara ce wa juna, “Wannan kuwa wane ne wanda har yake gafarta zunubai?” 50 t Sai Yesu ya ce wa matar, “Bangaskiyarki ta cece ki. Ki sauka lafiya.”

Luke 7

1 After he had ended all his sayings in the ears of the people, he entered into Capernaum.2 And a certain centurion’s servant, who was dear unto him, was sick and at the point of death.3 And when he heard concerning Jesus, he sent unto him elders of the Jews, asking him that he would come and save his servant.4 And they, when they came to Jesus, besought him earnestly, saying, He is worthy that thou shouldest do this for him;5 for he loveth our nation, and himself built us our synagogue.6 And Jesus went with them. And when he was now not far from the house, the centurion sent friends to him, saying unto him, Lord, trouble not thyself; for I am not worthy that thou shouldest come under my roof:7 wherefore neither thought I myself worthy to come unto thee: but say the word, and my servant shall be healed.8 For I also am a man set under authority, having under myself soldiers: and I say to this one, Go, and he goeth; and to another, Come, and he cometh; and to my servant, Do this, and he doeth it.9 And when Jesus heard these things, he marvelled at him, and turned and said unto the multitude that followed him, I say unto you, I have not found so great faith, no, not in Israel.10 And they that were sent, returning to the house, found the servant whole.11 And it came to pass soon afterwards, that he went to a city called Nain; and his disciples went with him, and a great multitude.12 Now when he drew near to the gate of the city, behold, there was carried out one that was dead, the only son of his mother, and she was a widow: and much people of the city was with her.13 And when the Lord saw her, he had compassion on her, and said unto her, Weep not.14 And he came nigh and touched the bier: and the bearers stood still. And he said, Young man, I say unto thee, Arise.15 And he that was dead sat up, and began to speak. And he gave him to his mother.16 And fear took hold on all: and they glorified God, saying, A great prophet is arisen among us: and, God hath visited his people.17 And this report went forth concerning him in the whole of Judaea, and all the region round about.18 And the disciples of John told him of all these things.19 And John calling unto him two of his disciples sent them to the Lord, saying, Art thou he that cometh, or look we for another?20 And when the men were come unto him, they said, John the Baptist hath sent us unto thee, saying, Art thou he that cometh, or look we for another?21 In that hour he cured many of diseases and plagues and evil spirits; and on many that were blind he bestowed sight.22 And he answered and said unto them, Go and tell John the things which ye have seen and heard; the blind receive their sight, the lame walk, the lepers are cleansed, and the deaf hear, the dead are raised up, the poor have good tidings preached to them.23 And blessed is he, whosoever shall find no occasion of stumbling in me.24 And when the messengers of John were departed, he began to say unto the multitudes concerning John, What went ye out into the wilderness to behold? a reed shaken with the wind?25 But what went ye out to see? a man clothed in soft raiment? Behold, they that are gorgeously apparelled, and live delicately, are in kings’ courts.26 But what went ye out to see? a prophet? Yea, I say unto you, and much more than a prophet.27 This is he of whom it is written, Behold, I send my messenger before thy face, Who shall prepare thy way before thee.

28 I say unto you, Among them that are born of women there is none greater than John: yet he that is but little in the kingdom of God is greater than he.29 And all the people when they heard, and the publicans, justified God, being baptized with the baptism of John.30 But the Pharisees and the lawyers rejected for themselves the counsel of God, being not baptized of him.31 Whereunto then shall I liken the men of this generation, and to what are they like?32 They are like unto children that sit in the marketplace, and call one to another; who say, We piped unto you, and ye did not dance; we wailed, and ye did not weep.33 For John the Baptist is come eating no bread nor drinking wine; and ye say, He hath a demon.34 The Son of man is come eating and drinking; and ye say, Behold, a gluttonous man, and a winebibber, a friend of publicans and sinners!35 And wisdom is justified of all her children.36 And one of the Pharisees desired him that he would eat with him. And he entered into the Pharisee’s house, and sat down to meat.37 And behold, a woman who was in the city, a sinner; and when she knew that he was sitting at meat in the Pharisee’s house, she brought an alabaster cruse of ointment,38 and standing behind at his feet, weeping, she began to wet his feet with her tears, and wiped them with the hair of her head, and kissed his feet, and anointed them with the ointment.39 Now when the Pharisee that had bidden him saw it, he spake within himself, saying, This man, if he were a prophet, would have perceived who and what manner of woman this is that toucheth him, that she is a sinner.40 And Jesus answering said unto him, Simon, I have somewhat to say unto thee. And he saith, Teacher, say on.41 A certain lender had two debtors: the one owed five hundred shillings, and the other fifty.42 When they had not wherewith to pay, he forgave them both. Which of them therefore will love him most?43 Simon answered and said, He, I suppose, to whom he forgave the most. And he said unto him, Thou hast rightly judged.44 And turning to the woman, he said unto Simon, Seest thou this woman? I entered into thy house, thou gavest me no water for my feet: but she hath wetted my feet with her tears, and wiped them with her hair.45 Thou gavest me no kiss: but she, since the time I came in, hath not ceased to kiss my feet.46 My head with oil thou didst not anoint: but she hath anointed my feet with ointment.47 Wherefore I say unto thee, Her sins, which are many, are forgiven; for she loved much: but to whom little is forgiven, the same loveth little.48 And he said unto her, Thy sins are forgiven.49 And they that sat at meat with him began to say within themselves, Who is this that even forgiveth sins?50 And he said unto the woman, Thy faith hath saved thee; go in peace.