previous next

LUK 8

Waɗansu Mata sun Tafi tare da Yesu

1  t Ba da daɗewa ba Yesu ya zazzaga birni da ƙauye yana wa'azi, yana yin bisharar Mulkin Allah. Sha biyun nan kuwa suna tare da shi, 2 t da waɗansu mata da aka raba da baƙaƙen aljannu da kuma rashin lafiyarsu. Cikinsu da Maryamu mai suna Magadaliya, wadda aka fitar wa da aljannu bakwai,

3 t da Yuwana matar Kuza, wakilin Hirudus, da Suzanatu, da kuma waɗansu da yawa da suka yi musu ɗawainiya da kayansu.

Misali na Mai Shuka

(Mat 13.1-9; Mar 4.1-9)


4 Da jama'a masu yawa suka taru, mutane suna ta zuwa gare shi gari da gari, sai ya yi musu misali ya ce. 5 “Wani mai shuka ya tafi shuka. Yana cikin yafa iri sai waɗansu suka fāɗi a hanya, aka tattake su, tsuntsaye suka tsince su. 6 Waɗansu kuma suka fāɗi a dutse. Da suka tsiro sai suka bushe, don ba danshi. 7 Waɗansu kuma suka fāɗi cikin ƙaya, suka tashi tare, har ƙayar ta sarƙe su.

8 t Waɗansu kuwa suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka girma, suka yi ƙwaya riɓi ɗari ɗari.” Da ya faɗi haka, sai ya ta da murya ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”

Manufar Misalin

(Mat 13.10-17; Mar 4.10-12)


9 Almajiransa suka tambaye shi ma'anar misalin.

10 t Sai ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Allah. Amma ga sauran sai da misali, don gani kam, su gani, amma ba za su gane ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba.

Yesu Ya Ba da Bayanin Misalin Mai Shuka

(Mat 13.18-23; Mar 4.13-20)


11  t “To, misalin shi ne, irin Maganar Allah ne. 12 Waɗanda suka fāɗi a hanya su ne kwatancin waɗanda suka ji Maganar Allah, sa'an nan Iblis ya zo ya ɗauke Maganar daga zuciyarsu, don kada su ba da gaskiya su sami ceto. 13 t Na kan dutsen kuwa su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar, sai su karɓa da farin ciki. Su kam, ba su da tushe. Sukan ba da gaskiya 'yan kwanaki kaɗan, amma a lokacin gwaji, sai su bauɗe. 14 Waɗanda suka fāɗi cikin ƙaya kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, amma a kwana a tashi, sai yawan taraddadin duniya, da dukiya, da shagalin duniya su sarƙe su, har su kasa yin amfani.

15 Waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, suka riƙe ta kamkam da zuciya ɗaya kyakkyawa, suka jure har suka yi amfani.

Fitila a Rufe da Masaki

(Mar 4.21-25)


16  t “Ba mai kunna fitila ya rufe ta da masaki, ko ya ajiye ta a ƙarƙashin gado. A'a, sai dai ya ɗora ta a maɗorinta, don masu shiga su ga hasken. 17 t Ba abin da yake a ɓoye da ba za a bayyana ba. Ba kuma asirin da ba zai tonu ya zama bayyananne ba.

18 t Ku kula fa, ku iya ji, don mai abu akan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake tsammani yake da shi ma, sai a karɓe masa.”

Uwar Yesu da 'Yan'uwansa

(Mat 12.46-50; Mar. 3.31-35)


19 Uwa tasa da 'yan'uwansa suka zo wurinsa, amma suka kasa isa gunsa saboda taro. 20 t Sai aka ce masa, “Tsohuwarka da 'yan'uwanka suna tsaye a waje, suna son ganinka.”

21 t Amma ya amsa musu ya ce, “Masu jin Maganar Allah, suna kuma aikata ta, ai, su ne uwata, su ne kuma 'yan'uwana.”

Yesu Ya Tsawata wa Hadiri

(Mat 8.23-27; Mar 4.35-41)


22 Wata rana ya shiga jirgi tare da almajiransa. Ya ce musu, “Mu haye wancan hayin teku.” Sai suka tashi. 23 Suna cikin tafiya sai barci ya kwashe shi. Hadiri mai iska ya taso a tekun, jirginsu ya tasar wa cika da ruwa, har suna cikin hatsari. 24 t Suka je suka tashe shi, suka ce, “Maigida, Maigida, mun hallaka!” Ya farka, ya tsawata wa iskar da kuma haukan ruwa. Sai suka kwanta, wurin ya yi tsit.

25 Ya ce musu, “Ina bangaskiyarku?” Suka kuwa tsorata suka yi mamaki, suna ce wa juna, “Wa ke nan kuma, har iska da ruwa ma yake yi wa umarni, suna kuwa yi masa biyayya?”

Warkar da Mai Aljan na Garasinawa

(Mat 8.28-34; Mar 5.1-20)


26 Sai suka iso ƙasar Garasinawa wadda take hannun riga da ƙasar Galili. 27 Da saukarsa a gaci sai wani mai aljannu ya fito daga cikin gari ya tarye shi. Ya daɗe bai sa tufa ba, ba ya zama a gida kuwa, sai a makabarta. 28 t Da ganin Yesu sai ya ƙwala ihu, ya faɗi a gabansa, ya ɗaga murya ya ce, “Ina ruwanka da ni, ya Yesu Ɗan Allah Maɗaukaki? Ina roƙonka, kada ka yi mini azaba.” 29 Ya faɗi haka ne domin Yesu ya umarci baƙin aljanin ya rabu da mutumin. Gama sau da yawa aljanin yakan buge shi, akan kuma tsare shi, a ɗaure shi da sarƙa da mari, amma ya tsintsinka ɗaurin, aljanin ya kora shi jeji. 30 Sai Yesu ya tambaye shi, “Yaya sunanka?” Ya ce, “Tuli,” don aljannu da yawa sun shiga cikinsa.

31 t Sai suka yi ta roƙansa kada ya umarce su su fāɗa a mahalaka.
32 To, wurin nan kuwa akwai wani babban garkin alade na kiwo a gangaren dutse, suka roƙe shi ya yardar musu su shiga cikinsu. Ya kuwa yardar musu.

33 t Sai aljannun suka rabu da mutumin, suka shiga aladun. Garken kuwa suka rungungunta ta gangaren, suka faɗa tekun, suka halaka a ruwa.
34 Da 'yan kiwon aladen nan suka ga abin da ya faru, suka gudu, suka ba da labari a birni da ƙauye. 35 t Sai jama'a suka firfito su ga abin da ya auku. Suka zo wurin Yesu, suka tarar da mutumin da aljannun suka rabu da shi, zaune gaban Yesu, saye da tufa, yana cikin hankalinsa. Sai suka tsorata. 36 t Waɗanda aka yi abin a idonsu kuwa, suka gaya musu yadda aka warkar da mai aljannun nan. 37 t Dukan mutanen kewayen ƙasar Garasinawa suka roƙi Yesu ya rabu da su, don tsoro mai yawa ya kama su. Sai ya shiga jirgi ya koma. 38 Mutumin da aljannun suka rabu da shi kuwa, ya roƙe shi izinin tafiya tare da shi. Amma ya sallame shi ya ce,

39 “Koma gida, ka faɗi irin manyan abubuwan da Allah ya yi maka.” Sai ya tafi ko'ina a cikin birnin yana sanar da manyan abubuwan da Yesu ya yi masa.

Warkar da 'Yar Yayirus da Matar da ta Taɓa Gezar Mayafin Yesu

(Mat 9.18-26; Mar 5.21-43)


40 To, da Yesu ya komo, taron suka yi masa maraba domin ko a dā ma duk suna jiransa ne. 41 t Sai ga wani mutum mai suna Yayirus, wani shugaban majami'a, ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya roƙe shi ya je gidansa.

42 Yana da 'ya ɗaya tilo, mai shekara misalin goma sha biyu, tana kuma bakin mutuwa.
Yana tafiya, taro masu yawa na matsa tasa,
43 t sai ga wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini, ta kuma ɓad da duk abin hannunta wajen masu magani, ba wanda ya iya warkar da ita. 44 t Ta raɓo ta bayansa, ta taɓa gezar mayafinsa. Nan take zubar jininta ta tsaya. 45 t Sai Yesu ya ce, “Wa ya taɓa ni?” Da kowa ya yi mūsū, Bitrus da waɗanda suke tare da shi suka ce, “Maigida, ai, taro masu yawa ne suke tutturarka, suna matsarka.” 46 t Amma Yesu ya ce, “An dai taɓa ni, domin na ji iko ya fita daga gare ni.” 47 Da matar ta ga ba dama ta ɓuya, sai ta matso tana rawar jiki, ta fāɗi a gabansa, ta bayyana a gaban duk jama'a dalilin da ya sa ta taɓa shi, da kuma yadda ta warke nan take.

48 t Sai ya ce mata, “'Yata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.”
49  t Yana cikin magana, sai ga wani ya zo daga gidan shugaban majami'ar, ya ce, “Ai, 'yarka ta rasu. Kada ka ƙara wahalar da Malamin.” 50 Amma da Yesu ya ji haka, ya amsa ya ce wa shugaban majami'ar, “Kada ka ji tsoro. Ka ba da gaskiya kawai, za ta kuwa warke.” 51 t Da ya isa gidan bai yarda kowa ya shiga tare da shi ba, sai Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, da kuma uban yarinyar da uwa tata, 52 t Duk kuwa ana ta kuka da kururuwa saboda ita. Amma Yesu ya ce, “Ku daina kuka. Ai, ba matacciya take ba, barci take yi.” 53 Sai suka yi masa dariyar raini, don sun sani ta mutu. 54 t Shi kuwa sai ya riƙe hannunta, ya ta da murya ya ce, “Yarinya, ki tashi.” 55 Ruhunta kuwa ya dawo, nan take ta tashi. Sai ya yi umarni a ba ta abinci. 56 t Iyayenta suka yi mamaki. Amma ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa abin da ya faru.

Luke 8

1 And it came to pass soon afterwards, that he went about through cities and villages, preaching and bringing the good tidings of the kingdom of God, and with him the twelve,2 and certain women who had been healed of evil spirits and infirmities: Mary that was called Magdalene, from whom seven demons had gone out,3 and Joanna the wife of Chuzas Herod’s steward, and Susanna, and many others, who ministered unto them of their substance.4 And when a great multitude came together, and they of every city resorted unto him, he spake by a parable:5 The sower went forth to sow his seed: and as he sowed, some fell by the way side; and it was trodden under foot, and the birds of the heaven devoured it.6 And other fell on the rock; and as soon as it grew, it withered away, because it had no moisture.7 And other fell amidst the thorns; and the thorns grew with it, and choked it.8 And other fell into the good ground, and grew, and brought forth fruit a hundredfold. As he said these things, he cried, He that hath ears to hear, let him hear.9 And his disciples asked him what this parable might be.10 And he said, Unto you it is given to know the mysteries of the kingdom of God: but to the rest in parables; that seeing they may not see, and hearing they may not understand.11 Now the parable is this: The seed is the word of God.12 And those by the way side are they that have heard; then cometh the devil, and taketh away the word from their heart, that they may not believe and be saved.13 And those on the rock are they who, when they have heard, receive the word with joy; and these have no root, who for a while believe, and in time of temptation fall away.14 And that which fell among the thorns, these are they that have heard, and as they go on their way they are choked with cares and riches and pleasures of this life, and bring no fruit to perfection.15 And that in the good ground, these are such as in an honest and good heart, having heard the word, hold it fast, and bring forth fruit with patience.16 And no man, when he hath lighted a lamp, covereth it with a vessel, or putteth it under a bed; but putteth it on a stand, that they that enter in may see the light.17 For nothing is hid, that shall not be made manifest; nor anything secret, that shall not be known and come to light.18 Take heed therefore how ye hear: for whosoever hath, to him shall be given; and whosoever hath not, from him shall be taken away even that which he thinketh he hath.19 And there came to him his mother and brethren, and they could not come at him for the crowd.20 And it was told him, Thy mother and thy brethren stand without, desiring to see thee.21 But he answered and said unto them, My mother and my brethren are these that hear the word of God, and do it.22 Now it came to pass on one of those days, that he entered into a boat, himself and his disciples; and he said unto them, Let us go over unto the other side of the lake: and they launched forth.23 But as they sailed he fell asleep: and there came down a storm of wind on the lake; and they were filling with water, and were in jeopardy.24 And they came to him, and awoke him, saying, Master, master, we perish. And he awoke, and rebuked the wind and the raging of the water: and they ceased, and there was a calm.25 And he said unto them, Where is your faith? And being afraid they marvelled, saying one to another, Who then is this, that he commandeth even the winds and the water, and they obey him?26 And they arrived at the country of the Gerasenes, which is over against Galilee.27 And when he was come forth upon the land, there met him a certain man out of the city, who had demons; and for a long time he had worn no clothes, and abode not in any house, but in the tombs.28 And when he saw Jesus, he cried out, and fell down before him, and with a loud voice said, What have I to do with thee, Jesus, thou Son of the Most High God? I beseech thee, torment me not.29 For he was commanding the unclean spirit to come out from the man. For oftentimes it had seized him: and he was kept under guard, and bound with chains and fetters; and breaking the bands asunder, he was driven of the demon into the deserts.30 And Jesus asked him, What is thy name? And he said, Legion; for many demons were entered into him.31 And they entreated him that he would not command them to depart into the abyss.32 Now there was there a herd of many swine feeding on the mountain: and they entreated him that he would give them leave to enter into them. And he gave them leave.33 And the demons came out from the man, and entered into the swine: and the herd rushed down the steep into the lake, and were drowned.34 And when they that fed them saw what had come to pass, they fled, and told it in the city and in the country.35 And they went out to see what had come to pass; and they came to Jesus, and found the man, from whom the demons were gone out, sitting, clothed and in his right mind, at the feet of Jesus: and they were afraid.36 And they that saw it told them how he that was possessed with demons was made whole.37 And all the people of the country of the Gerasenes round about asked him to depart from them, for they were holden with great fear: and he entered into a boat, and returned.38 But the man from whom the demons were gone out prayed him that he might be with him: but he sent him away, saying,39 Return to thy house, and declare how great things God hath done for thee. And he went his way, publishing throughout the whole city how great things Jesus had done for him.40 And as Jesus returned, the multitude welcomed him; for they were all waiting for him.41 And behold, there came a man named Jairus, and he was a ruler of the synagogue: and he fell down at Jesus’ feet, and besought him to come into his house;42 for he had an only daughter, about twelve years of age, and she was dying. But as he went the multitudes thronged him.43 And a woman having an issue of blood twelve years, who had spent all her living upon physicians, and could not be healed of any,44 came behind him, and touched the border of his garment: and immediately the issue of her blood stanched.45 And Jesus said, Who is it that touched me? And when all denied, Peter said, and they that were with him, Master, the multitudes press thee and crush thee.46 But Jesus said, Some one did touch me; for I perceived that power had gone forth from me.47 And when the woman saw that she was not hid, she came trembling, and falling down before him declared in the presence of all the people for what cause she touched him, and how she was healed immediately.48 And he said unto her, Daughter, thy faith hath made thee whole; go in peace.49 While he yet spake, there cometh one from the ruler of the synagogue’s house, saying, Thy daughter is dead; trouble not the Teacher.50 But Jesus hearing it, answered him, Fear not: only believe, and she shall be made whole.51 And when he came to the house, he suffered not any man to enter in with him, save Peter, and John, and James, and the father of the maiden and her mother.52 And all were weeping, and bewailing her: but he said, Weep not; for she is not dead, but sleepeth.53 And they laughed him to scorn, knowing that she was dead.54 But he, taking her by the hand, called, saying, Maiden, arise.55 And her spirit returned, and she rose up immediately: and he commanded that something be given her to eat.56 And her parents were amazed: but he charged them to tell no man what had been done.