previous next

MAR 10

Koyarwar Yesu a kan Kisan Aure

(Mat 19.1-12; Luka 16.18)

1  t Sai Yesu ya tashi daga nan, ya tafi ƙasar Yahudiya, da kuma hayin Kogin Urdun. Taro kuma ya sāke haɗuwa wurinsa, ya kuma sāke koya musu kamar yadda ya saba.
2  t Sai waɗansu Farisiyawa suka zo wajensa don su gwada shi, suka tambaye shi suka ce, “Halal ne mutum ya saki mata tasa?” 3 Sai ya amsa musu ya ce, “Me Musa ya umarce ku?” 4 t Suka ce, “Musa ya ba da izini a rubuta takardar kisan aure, a kuma saki matar.” 5 t Yesu ya ce musu, “Don taurinkanku ne Musa ya rubuta muku wannan umarni. 6 t Amma tun farkon halitta ‘Allah ya halicce su, namiji da tamata.’ 7 ‘Don haka fa sai mutum yă bar uwa tasa da ubansa, yă manne wa mata tasa. 8 t Haka su biyun nan su zama jiki guda.’ Har nan gaba su zama ba jiki biyu ba ne, ɗaya ne.

9 Abin da Allah fa ya gama, kada mutum ya raba.”
10 A cikin gida kuma sai almajiransa suka sāke tambayarsa wannan magana. 11 t Sai ya ce musu, “Kowa ya saki mata tasa, ya auri wata, zina yake yi da ta biyun.

12 t In kuma matar ta saki mijinta ta auri wani, ta yi zina ke nan.”

Yesu Ya Sa wa 'Yan Yara Albarka

(Mat 19.13-15; Luka 18.15-17)


13 Suna kawo masa waɗansu yara ƙanana domin ya taɓa su, sai almajiransa suka kwaɓe su. 14 t Da Yesu ya ga haka, sai ya ji haushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai, Mulkin Allah na irinsu ne. 15 t Hakika, ina gaya muku, duk wanda bai yi na'am da Mulkin Allah kamar yadda ƙaramin yaro yake yi ba, ba zai shiga Mulkin ba har abada.”

16 t Sai Yesu ya rugume su, yana ɗora musu hannu, yana sa musu albarka.

Saurayi Mai Dukiya

(Mat 19.16-30; Luka 18.18-30)


17  t Ya fara tafiya ke nan, sai ga wani ya sheƙo a guje, ya durƙusa a gabansa, ya tambaye shi ya ce, “Malam managarci, me zan yi in gaji rai madawwami?” 18 Sai Yesu ya ce masa, “Don me ka kira ni managarci? Ai, ba wani Managarci sai Allah kaɗai. 19 t Ka dai san umarnan nan, ‘Kada ka yi kisankai. Kada ka yi zina. Kada ka yi sata. Kada ka yi shaidar zur. Kada ka yi zamba. Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ” 20 Sai ya ce masa, “Malam, ai, duk na kiyaye waɗannan tun ƙuruciyata.” 21 t Yesu ya dube shi duban ƙauna, ya ce masa, “Abu guda ne kawai ya rage maka. Sai ka je, ka sayar da duk mallakarka, ka ba gajiyayyu, za ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.”

22 Da jin wannan magana gabansa ya fāɗi, ya tafi yana baƙin ciki, don yana da arziki ƙwarai.
23  t Daga nan sai Yesu ya duddubi almajiransa, ya ce musu, “Da ƙyar kamar me masu dukiya su shiga Mulkin Allah!” 24 t Almajiran kuwa suka yi mamakin maganarsa. Sai Yesu ya sāke ce musu, “Ya ku 'ya'yana, da ƙyar ne kamar me a shiga Mulkin Allah! 25 t Zai fiye wa raƙumi sauƙi ya bi ta kafar allura, da mai arziki ya shiga Mulkin Allah.” 26 Sai suka yi mamaki ƙwarai da gaske, suka ce masa, “To, in haka ne, wa zai sami ceto ke nan?” 27 t Yesu ya dube su, ya ce, “Ga mutane kam ba mai yiwuwa ba ne, amma fa ba ga Allah ba. Domin kowane abu mai yiwuwa ne a gun Allah.” 28 t Sai Bitrus ya fara ce masa, “To, ai, ga shi, mu mun bar kome, mun bi ka.” 29 Yesu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ba wanda zai bar gida, ko 'yan'uwansa mata, ko 'yan'uwansa maza, ko uwa tasa, ko ubansa, ko 'ya'yansa, ko gonakinsa, sabili da ni da kuma bishara, 30 t sa'an nan ya kasa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu, na gidaje, da 'yan'uwa mata, da 'yan'uwa maza, da iyaye mata, da 'ya'ya, da gonaki, amma game da tsanani, a lahira kuma ya sami rai madawwami.

31 t Da yawa na farko za su koma na ƙarshe, na ƙarshe kuma za su zama na farko.”

Yesu kuma Ya Sāke Faɗar Irin Mutuwar da Zai Yi

(Mat 20.17-19; Luka 18.31-34)


32  t Suna tafiya Urushalima, Yesu kuwa na tafe gabansu, sai suka yi mamaki, mutanen da suke biye kuma suka tsorata. Ya sāke keɓe sha biyun nan, ya fara shaida musu abin da zai same shi. 33 t Ya ce, “Ga shi, za mu Urushalima, za a ba da Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman Attaura, za su kuwa yi masa hukuncin kisa, su bāshe shi ga al'ummai.

34 t Za su yi masa ba'a, su tofa masa yau, su yi masa bulala, su kashe shi, bayan kwana uku kuma ya tashi.”

Roƙon Yakubu da Yahaya

(Mat 20.20-28)


35 Yakubu da Yahaya, 'ya'yan Zabadi, suka kusato shi, suka ce masa, “Malam, muna so ka yi mana duk abin da muka roƙe ka.” 36 Sai ya ce musu, “Me kuke so in yi muku?” 37 t Suka ce masa, “Ka yardar mana, ranar ɗaukakarka, mu zauna ɗaya a damanka, ɗaya a hagun.” 38 t Amma Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Kwa iya sha da ƙoƙon da ni zan sha? Ko kwa iya a yi muku baftisma da baftismar da za a yi mini?” 39 t Suka ce masa, “Ma iya.” Sai Yesu ya ce musu, “Ƙoƙon da ni zan sha, da shi za ku sha, baftismar da za a yi mini kuwa, da ita za a yi muku. 40 Amma zama a damana, ko a haguna, ba nawa ba ne da zan bayar, ai, na waɗanda aka riga aka shirya wa ne.” 41 Da almajiran nan goma suka ji haka, suka fara jin haushin Yakubu da Yahaya. 42 Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun sani waɗanda aka san su da mulkin al'ummai sukan nuna musu iko, hakimansu ma sukan gasa musu iko. 43 t Ba haka zai zama a tsakaninku ba. Amma duk wanda yake son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku. 44 Wanda duk kuma yake so ya shugabance ku, lalle ne ya zama bawan kowa.

45 t Domin Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba, sai dai domin shi ya yi bautar, ya kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”

Bartimawas Makaho Ya Sami Ganin Gari

(Mat 20.29-34; Luka 18.35-43)


46 Sai suka iso Yariko. Yana fita daga Yariko ke nan, da shi, da almajiransa, da wani ƙasaitaccen taro, sai ga wani makaho mai bara, wai shi Bartimawas, ɗan Timawas, yana zaune a gefen hanya. 47 t Da ya ji dai Yesu Banazare ne, sai ya fara ɗaga murya yana cewa, “Ya Yesu, Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!” 48 Waɗansu da yawa suka kwaɓe shi, cewa ya yi shiru. Amma sai ƙara ɗaga murya yake yi ƙwarai da gaske, yana cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!” 49 Sai Yesu ya tsaya ya ce, “Ku kirawo shi.” Sai suka kirawo makahon suka ce masa, “Albishirinka! Taso, yana kiranka.” 50 Sai ya yar da mayafinsa, ya zaburo wurin Yesu. 51 t Yesu ya ce masa, “Me kake so in yi maka?” Makahon ya ce masa, “Malam, in sami gani!” 52 t Sai Yesu ya ce masa, “Yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan take ya gani, ya bi Yesu, suka tafi.

Mark 10

1 And he arose from thence and cometh into the borders of Judaea and beyond the Jordan: and multitudes come together unto him again; and, as he was wont, he taught them again.2 And there came unto him Pharisees, and asked him, Is it lawful for a man to put away his wife? trying him.3 And he answered and said unto them, What did Moses command you?4 And they said, Moses suffered to write a bill of divorcement, and to put her away.5 But Jesus said unto them, For your hardness of heart he wrote you this commandment.6 But from the beginning of the creation, Male and female made he them.7 For this cause shall a man leave his father and mother, and shall cleave to his wife;8 and the two shall become one flesh: so that they are no more two, but one flesh.9 What therefore God hath joined together, let not man put asunder.10 And in the house the disciples asked him again of this matter.11 And he saith unto them, Whosoever shall put away his wife, and marry another, committeth adultery against her:12 and if she herself shall put away her husband, and marry another, she committeth adultery.13 And they were bringing unto him little children, that he should touch them: and the disciples rebuked them.14 But when Jesus saw it, he was moved with indignation, and said unto them, Suffer the little children to come unto me; forbid them not: for to such belongeth the kingdom of God.15 Verily I say unto you, Whosoever shall not receive the kingdom of God as a little child, he shall in no wise enter therein.16 And he took them in his arms, and blessed them, laying his hands upon them.17 And as he was going forth into the way, there ran one to him, and kneeled to him, and asked him, Good Teacher, what shall I do that I may inherit eternal life?18 And Jesus said unto him, Why callest thou me good? none is good save one, even God.19 Thou knowest the commandments, Do not kill, Do not commit adultery, Do not steal, Do not bear false witness, Do not defraud, Honor thy father and mother.20 And he said unto him, Teacher, all these things have I observed from my youth.21 And Jesus looking upon him loved him, and said unto him, One thing thou lackest: go, sell whatsoever thou hast, and give to the poor, and thou shalt have treasure in heaven: and come, follow me.22 But his countenance fell at the saying, and he went away sorrowful: for he was one that had great possessions.23 And Jesus looked round about, and saith unto his disciples, How hardly shall they that have riches enter into the kingdom of God!24 And the disciples were amazed at his words. But Jesus answereth again, and saith unto them, Children, how hard is it for them that trust in riches to enter into the kingdom of God!25 It is easier for a camel to go through a needle’s eye, than for a rich man to enter into the kingdom of God.26 And they were astonished exceedingly, saying unto him, Then who can be saved?27 Jesus looking upon them saith, With men it is impossible, but not with God: for all things are possible with God.28 Peter began to say unto him, Lo, we have left all, and have followed thee.29 Jesus said, Verily I say unto you, There is no man that hath left house, or brethren, or sisters, or mother, or father, or children, or lands, for my sake, and for the gospel’s sake,30 but he shall receive a hundredfold now in this time, houses, and brethren, and sisters, and mothers, and children, and lands, with persecutions; and in the world to come eternal life.31 But many that are first shall be last; and the last first.32 And they were on the way, going up to Jerusalem; and Jesus was going before them: and they were amazed; and they that followed were afraid. And he took again the twelve, and began to tell them the things that were to happen unto him,33 saying, Behold, we go up to Jerusalem; and the Son of man shall be delivered unto the chief priests and the scribes; and they shall condemn him to death, and shall deliver him unto the Gentiles:34 and they shall mock him, and shall spit upon him, and shall scourge him, and shall kill him; and after three days he shall rise again.35 And there come near unto him James and John, the sons of Zebedee, saying unto him, Teacher, we would that thou shouldest do for us whatsoever we shall ask of thee.36 And he said unto them, What would ye that I should do for you?37 And they said unto him, Grant unto us that we may sit, one on thy right hand, and one on thy left hand, in thy glory.38 But Jesus said unto them, Ye know not what ye ask. Are ye able to drink the cup that I drink? or to be baptized with the baptism that I am baptized with?39 And they said unto him, We are able. And Jesus said unto them, The cup that I drink ye shall drink; and with the baptism that I am baptized withal shall ye be baptized:40 but to sit on my right hand or on my left hand is not mine to give; but it is for them for whom it hath been prepared.41 And when the ten heard it, they began to be moved with indignation concerning James and John.42 And Jesus called them to him, and saith unto them, Ye know that they who are accounted to rule over the Gentiles lord it over them; and their great ones exercise authority over them.43 But it is not so among you: but whosoever would become great among you, shall be your minister;44 and whosoever would be first among you, shall be servant of all.45 For the Son of man also came not to be ministered unto, but to minister, and to give his life a ransom for many.46 And they come to Jericho: and as he went out from Jericho, with his disciples and a great multitude, the son of Timaeus, Bartimaeus, a blind beggar, was sitting by the way side.47 And when he heard that it was Jesus the Nazarene, he began to cry out, and say, Jesus, thou son of David, have mercy on me.48 And many rebuked him, that he should hold his peace: but he cried out the more a great deal, Thou son of David, have mercy on me.49 And Jesus stood still, and said, Call ye him. And they call the blind man, saying unto him, Be of good cheer: rise, he calleth thee.50 And he, casting away his garment, sprang up, and came to Jesus.51 And Jesus answered him, and said, What wilt thou that I should do unto thee? And the blind man said unto him, Rabboni, that I may receive my sight.52 And Jesus said unto him, Go thy way; thy faith hath made thee whole. And straightway he received his sight, and followed him in the way.