previous next

MAR 12

Misali na Manoman da Suka Yi Sufurin Garkar Inabi

(Mat 21.33-46; Luka 20.9-19)

1  t Sai Yesu ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ne ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabin, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa. 2 Da kakar inabin ta yi, sai ya aiki wani bawansa wurin manoman nan ya karɓo masa gallar garkar. 3 Manoman kuwa suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hanu banza. 4 Sai ya sāke aika musu wani bawa. Shi kuma suka yi masa rotsi, suka wulakanta shi. 5 Ya sāke aiken wani, shi kam, sai suka kashe shi. Haka fa aka yi ta yi da waɗansu da yawa, ana dūkan waɗansu, ana kashe waɗansu. 6 t Har yanzu dai yana da sauran ɗaya tak, shi ne makaɗaicin ɗansa. Daga ƙarshe ya aike shi wurinsu, yana cewa, ‘Sā ga girman ɗana.’ 7 Amma manoman nan suka ce wa juna, ‘Ai, wannan shi ne magajin. Ku zo mu kashe shi, gādon yă zama namu.’ 8 Sai suka kama shi, suka kashe shi, suka jefar da shi bayan shinge. 9 To, me ubangijin garkan nan zai yi? Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba waɗansu garkar.

10 t Ashe, ba ku taɓa karanta wannan Nassi ba? cewa,
‘Dutsen da magina suka ƙi,
Shi ne ya zama mafificin dutsen gini.

11  t Wannan aikin Ubangiji ne,
A gare mu kuwa abin al'ajabi ne.’ ”

12  t Sai suka nemi su kama shi, don sun lura a kansu ne ya yi misalin, amma suna jin tsoron jama'a. Don haka suka ƙyale shi, suka tafi.

Biyan Haraji ga Kaisar

(Mat 22.15-22; Luka 20.20-26)


13  t Suka aiko masa da waɗansu Farisiyawa da mutanen Hirudus, don su burma shi cikin magana tasa. 14 Da suka zo, suka ce masa, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, ba ka kuma zaɓen kowa, domin ka ɗauki kowa da kowa daidai, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa? 15 Mu biya, ko kada mu biya?” Shi kuwa da ya gane makircinsu, ya ce musu, “Don me kuke jarraba ni? Ku kawo mini dinari in gani.” 16 Suka kawo masa. Ya ce musu, “Suran nan da sunan nan na wane ne?” Suka ce masa, “Na Kaisar ne.”

17 t Sai Yesu ya ce musu, “To, ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.” Sai suka yi mamakinsa ƙwarai.

Tambaya a kan Tashin Matattu

(Mat 22.23-33; Luka 20.27-40)


18  t Sai Sadukiyawa (su da suke cewa, wai ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka tambaye shi suka ce, 19 t “Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan ɗan'uwan mutum ya mutu, ya bar mata tasa ba ɗa, sai lalle mutumin ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya. 20 To, an yi waɗansu 'yan'uwa maza guda bakwai. Na farkon ya yi aure, ya mutu bai bar baya ba. 21 Na biyun kuma ya aure ta, shi ma ya mutu, ba ɗa. Na ukun ma haka. 22 Haka dai duk bakwai ɗin, ba wanda ya bar ɗa. Daga ƙarshe kuma ita matar ta mutu.

23 To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai ɗin sun aure ta.”
24  t Sai Yesu ya ce musu, “Ba saboda wannan ne ya sa kuka ɓata ba? Wato don ba ku san Littattafai ba, ba ku kuma san ikon Allah ba. 25 t Domin in an tashi daga matattu, ba a aure, ba a aurarwa, amma kamar mala'ikun da suke Sama ake. 26 t Game da tashin matattu kuma, ashe, ba ku taɓa karantawa a Littafin Musa ba, yadda Allah ya ce masa, ‘Ni ne Allahn Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu’?

27 Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba. Kun ɓata da gaske.”

Umarni Mafi Girma

(Mat 22.34-40; Luka 10.25-28)


28  t Sai wani malamin Attaura ya zo ya ji suna muhawara da juna. Da dai ya ga Yesu ya ba su kyakkyawar amsa, sai ya tambaye shi, “Wane umarni ne mafi girma duka?” 29 Yesu ya amsa masa ya ce, “Mafi girma shi ne, ‘Ku saurara, ya Isra'ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 30 t Sai ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka, da kuma dukkan ƙarfinka.’ 31 t Mabiyinsa shi ne, ‘Ka ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.’ Ba fa sauran wani umarni da ya fi waɗannan girma.” 32 t Sai malamin Attaura ya ce masa, “Hakika gaskiyarka Malam, Ubangiji ɗaya ne, ba kuwa wani sai shi. 33 t A ƙaunace shi kuma da dukkan zuciya, da dukan hankali, da dukkan ƙarfi, a kuma ƙaunaci ɗan'uwa kamar kai, ai, ya fi dukkan hadayar ƙone-ƙone da yanke-yanke nesa.”

34 t Da Yesu ya ga ya yi masa magana da fasaha, sai ya ce masa, “Ba ka nesa da Mulkin Allah.” Bayan wannan kuma ba wanda ya yi ƙarfin halin sāke tambayarsa wani abu.

Tambaya a kan Ɗan Dawuda

(Mat 22.41-46; Luka 20.41-44)


35  t Sa'ad da Yesu yake koyarwa a Haikalin sai ya ce, “Ƙaƙa malaman Attaura za su ce Almasihu ɗan Dawuda ne?

36 t Domin Dawuda kansa, ta ikon Ruhu Mai Tsarki ya ce,
‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,
Zauna a damana,
Sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.’

37  t Dawuda da kansa ya kira shi Ubangiji. To, ƙaƙa zai zama ɗansa?” Babban taron mutane kuwa sun saurare shi da murna.

Yesu Ya Fallashi Malaman Attaura

(Mat 23.1-36; Luka 11.37-54; 20.45-47)


38 A koyarwa tasa har ya ce, “Ku yi hankali da malaman Attaura, masu son yawo da manyan riguna, suna so a gaishe su a kasuwa, 39 t da kuma mafifitan mazaunai a majami'u, da mazaunan alfarma a wurin biki.

40 Su ne masu cin kayan matan da mazansu suka mutu, da yin doguwar addu'a don ɓad da sawu. Su za a yi wa hukunci mafi tsanani.”

Baiko Wadda aka Zuba

(Luka 21.1-4)


41  t Sai ya zauna gaban baitulmalin Haikalin, yana duban yadda jama'a suke zuba kuɗi a ciki. Waɗansu masu arziki da yawa suna zuba kuɗi masu tsoka. 42 Sai ga wata gajiyayyiya da mijinta ya mutu ta zo, ta zuba rabin kobo biyu a ciki, wato kobo ke nan. 43 Sai ya kira almajiransa, ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, abin da gajiyayyiya gwauruwan nan ta zuba cikin baitulmalin nan ya fi na sauran duka. 44 t Su duk sun bayar daga yalwa tasu ne, ita kuwa daga cikin rashinta ta ba da duk abin da take da shi, duk ma da kuɗinta na abinci.”

Mark 12

1 And he began to speak unto them in parables. A man planted a vineyard, and set a hedge about it, and digged a pit for the winepress, and built a tower, and let it out to husbandmen, and went into another country.2 And at the season he sent to the husbandmen a servant, that he might receive from the husbandmen of the fruits of the vineyard.3 And they took him, and beat him, and sent him away empty.4 And again he sent unto them another servant; and him they wounded in the head, and handled shamefully.5 And he sent another; and him they killed: and many others; beating some, and killing some.6 He had yet one, a beloved son: he sent him last unto them, saying, They will reverence my son.7 But those husbandmen said among themselves, This is the heir; come, let us kill him, and the inheritance shall be ours.8 And they took him, and killed him, and cast him forth out of the vineyard.9 What therefore will the lord of the vineyard do? he will come and destroy the husbandmen, and will give the vineyard unto others.10 Have ye not read even this scripture: The stone which the builders rejected, The same was made the head of the corner;

11 This was from the Lord, And it is marvellous in our eyes?

12 And they sought to lay hold on him; and they feared the multitude; for they perceived that he spake the parable against them: and they left him, and went away.13 And they send unto him certain of the Pharisees and of the Herodians, that they might catch him in talk.14 And when they were come, they say unto him, Teacher, we know that thou art true, and carest not for any one; for thou regardest not the person of men, but of a truth teachest the way of God: Is it lawful to give tribute unto Caesar, or not?15 Shall we give, or shall we not give? But he, knowing their hypocrisy, said unto them, Why make ye trial of me? bring me a denarius, that I may see it.16 And they brought it. And he saith unto them, Whose is this image and superscription? And they said unto him, Caesar’s.17 And Jesus said unto them, Render unto Caesar the things that are Caesar’s, and unto God the things that are God’s. And they marvelled greatly at him.18 And there come unto him Sadducees, who say that there is no resurrection; and they asked him, saying,19 Teacher, Moses wrote unto us, If a man’s brother die, and leave a wife behind him, and leave no child, that his brother should take his wife, and raise up seed unto his brother.20 There were seven brethren: and the first took a wife, and dying left no seed;21 and the second took her, and died, leaving no seed behind him; and the third likewise:22 and the seven left no seed. Last of all the woman also died.23 In the resurrection whose wife shall she be of them? for the seven had her to wife.24 Jesus said unto them, Is it not for this cause that ye err, that ye know not the scriptures, nor the power of God?25 For when they shall rise from the dead, they neither marry, nor are given in marriage; but are as angels in heaven.26 But as touching the dead, that they are raised; have ye not read in the book of Moses, in the place concerning the Bush, how God spake unto him, saying, I am the God of Abraham, and the God of Isaac, and the God of Jacob?27 He is not the God of the dead, but of the living: ye do greatly err.28 And one of the scribes came, and heard them questioning together, and knowing that he had answered them well, asked him, What commandment is the first of all?29 Jesus answered, The first is, Hear, O Israel; The Lord our God, the Lord is one:30 and thou shalt love the Lord thy God with all thy heart, and with all thy soul, and with all thy mind, and with all thy strength.31 The second is this, Thou shalt love thy neighbor as thyself. There is none other commandment greater than these.32 And the scribe said unto him, Of a truth, Teacher, thou hast well said that he is one; and there is none other but he:33 and to love him with all the heart, and with all the understanding, and with all the strength, and to love his neighbor as himself, is much more than all whole burnt-offerings and sacrifices.34 And when Jesus saw that he answered discreetly, he said unto him, Thou art not far from the kingdom of God. And no man after that durst ask him any question.35 And Jesus answered and said, as he taught in the temple, How say the scribes that the Christ is the son of David?36 David himself said in the Holy Spirit, The Lord said unto my Lord, Sit thou on my right hand, Till I make thine enemies the footstool of thy feet.

37 David himself calleth him Lord; and whence is he his son? And the common people heard him gladly.38 And in his teaching he said, Beware of the scribes, who desire to walk in long robes, and to have salutations in the marketplaces,39 and chief seats in the synagogues, and chief places at feasts:40 they that devour widows’ houses, and for a pretence make long prayers; these shall receive greater condemnation.41 And he sat down over against the treasury, and beheld how the multitude cast money into the treasury: and many that were rich cast in much.42 And there came a poor widow, and she cast in two mites, which make a farthing.43 And he called unto him his disciples, and said unto them, Verily I say unto you, This poor widow cast in more than all they that are casting into the treasury:44 for they all did cast in of their superfluity; but she of her want did cast in all that she had, even all her living.