MAR 16
Tashin Yesu daga Matattu
(Mat 28.1-10; Luka 24.1-12; Yah 20.1-10)
1 t Da Asabar ta wuce, Maryamu Magadaliya, da Maryamu uwar Yakubu, da kuma Salome, suka sayo kayan ƙanshi, domin su je su shafa masa. 2 A ranar farko ta mako, da assussuba suka tafi kabarin, da fitowar rana sai suka isa. 3 t Suna ce wa juna, “Wa zai mirgine mana dutsen nan daga bakin kabarin?” 4 Da suka ɗaga kai, suka ga, ashe, an mirgine dutsen waje ɗaya, ga shi kuwa, ƙato ne ƙwarai. 5 t Suna shiga kabarin, sai suka ga wani saurayi a zaune daga dama, saye da farar riga. Sai suka firgita. 6 t Shi kuwa ya ce musu, “Kada ku firgita. Yesu Banazare kuke nema, wanda aka gicciye. Ai, ya tashi, ba ya nan. Kun ga ma wurin da suka sa shi! 7 t Amma ku tafi ku gaya wa almajiransa, duk da Bitrus, cewa zai riga ku zuwa ƙasar Galili, a can ne za ku gan shi, kamar yadda ya faɗa muku.”
8 Sai suka fita, suka ruga a guje daga kabarin, suna rawar jiki a ruɗe. Ba su kuma ce wa kowa kome ba, domin suna tsoro.Yesu Ya Bayyana ga Maryamu Magadaliya
(Yah 20.11-18)
[ 9 t Da ya tashi da rai da wuri ranar farko ta mako, ya fara bayyana ga Maryamu Magadaliya, wadda ya fitar wa da aljannu bakwai. 10 Ita kuwa ta tafi ta faɗa wa waɗanda dā suke tare da shi, ta tarar suna baƙin ciki, suna kuka.
11 t Amma da suka ji yana da rai, har ma ta gan shi, sai suka ƙi gaskatawa.Yesu Ya Bayyana ga Almajirai Biyu
(Luka 24.13-35)
12 t Bayan haka ya bayyana da wata kama ga waɗansu biyu daga cikinsu, sa'ad da suke tafiya ƙauye.
13 Suka koma suka gaya wa sauran, su ma kuwa ba su gaskata su ba.Umarnin Yesu ga Goma Sha Ɗayan
(Mat 28.16-20; Luka 24.36-49; Yah 20.19-23; A.M. 1.6-8)
14 t Daga baya ya bayyana ga sha ɗayan nan, su kansu, sa'ad da suke cin abinci. Sai ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu da taurinkansu, domin ba su gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi ba. 15 t Sai ya ce musu, “Ku tafi ko'ina a duniya, ku yi wa dukkan 'yan adam bishara. 16 t Duk wanda ya ba da gaskiya, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma wanda ya ƙi ba da gaskiya za a hukunta shi. 17 t Za a ga waɗannan mu'ujizai wurin masu ba da gaskiya, wato da sunana za su fitar da aljannu, za su yi magana da waɗansu baƙin harsuna,
18 t za su iya ɗaukar maciji, kowace irin guba kuma suka sha, ba za ta cuce su ba ko kaɗan, za su kuma ɗora wa marasa lafiya hannu, su warke.”An Ɗauke Yesu zuwa Sama
(Luka 24.50-53; A.M. 1.9-11)
19 t To, bayan da Ubangiji Yesu ya yi musu jawabi, aka ɗauke shi aka kai shi Sama, ya zauna dama ga Allah. 20 Su kuwa suka tafi, suka yi ta wa'azi ko'ina, Ubangiji yana taimakonsu, yana kuma tabbatar da maganarsu ta mu'ujizan nan da suke biye da maganar.]
Mark 16
1 And when the sabbath was past, Mary Magdalene, and Mary the mother of James, and Salome, bought spices, that they might come and anoint him.2 And very early on the first day of the week, they come to the tomb when the sun was risen.3 And they were saying among themselves, Who shall roll us away the stone from the door of the tomb?4 and looking up, they see that the stone is rolled back: for it was exceeding great.5 And entering into the tomb, they saw a young man sitting on the right side, arrayed in a white robe; and they were amazed.6 And he saith unto them, Be not amazed: ye seek Jesus, the Nazarene, who hath been crucified: he is risen; he is not here: behold, the place where they laid him!7 But go, tell his disciples and Peter, He goeth before you into Galilee: there shall ye see him, as he said unto you.8 And they went out, and fled from the tomb; for trembling and astonishment had come upon them: and they said nothing to any one; for they were afraid.9 Now when he was risen early on the first day of the week, he appeared first to Mary Magdalene, from whom he had cast out seven demons.10 She went and told them that had been with him, as they mourned and wept.11 And they, when they heard that he was alive, and had been seen of her, disbelieved.12 And after these things he was manifested in another form unto two of them, as they walked, on their way into the country.13 And they went away and told it unto the rest: neither believed they them.14 And afterward he was manifested unto the eleven themselves as they sat at meat; and he upbraided them with their unbelief and hardness of heart, because they believed not them that had seen him after he was risen.15 And he said unto them, Go ye into all the world, and preach the gospel to the whole creation.16 He that believeth and is baptized shall be saved; but he that disbelieveth shall be condemned.17 And these signs shall accompany them that believe: in my name shall they cast out demons; they shall speak with new tongues;18 they shall take up serpents, and if they drink any deadly thing, it shall in no wise hurt them; they shall lay hands on the sick, and they shall recover.19 So then the Lord Jesus, after he had spoken unto them, was received up into heaven, and sat down at the right hand of God.20 And they went forth, and preached everywhere, the Lord working with them, and confirming the word by the signs that followed. Amen.