MAR 2
Yesu Ya Warkar da Shanyayye
(Mat 9.1-8; Luka 5.17-26)
1 Bayan 'yan kwanaki, da ya sāke komowa Kafarnahum, sai aka ji labari yana gida. 2 t Aka kuwa taru maƙil har ba sauran wuri, ko a bakin ƙofa. Shi kuwa yana yi musu wa'azin Maganar Allah. 3 t Sai suka kawo masa wani shanyayye, mutum huɗu suna ɗauke da shi. 4 Da suka kāsa kusatarsa don yawan mutane, suka buɗe rufin soron ta sama da shi. Da suka huda ƙofa kuwa, suka zura gadon da shanyayye yake kwance a kai. 5 t Da Yesu ya ga bangaskiyarsu sai ya ce wa shanyayyen, “Ɗana, an gafarta maka zunubanka.” 6 To, waɗansu malaman Attaura na nan zaune, suna ta wuswasi a zuciya tasu, 7 t suna cewa, “Don me mutumin nan yake faɗar haka? Ai, sāɓo yake! Wa yake da ikon gafarta zunubi banda Allah kaɗai?” 8 Nan da nan, da Yesu ya gane a ransa suna ta wuswasi haka a zuci, sai ya ce musu, “Don me kuke wuswasi haka a zuciyarku? 9 Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, ‘An gafarta maka zunubanka’, ko kuwa a ce, ‘Tashi ka ɗauki shimfiɗarka ka yi tafiya’? 10 t Amma don ku sakankance Ɗan Mutum na da ikon gafarta zunubi a duniya”–sai ya ce wa shanyayyen– 11 “Na ce maka, tashi ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi gida.”
12 t Sai ya tashi nan da nan, ya ɗauki shimfiɗarsa, ya fita a gaban idon kowa, har suka yi mamaki duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin irin haka ba!”Kiran Lawi
(Mat. 9.9-13; Luka 5.27-32)
13 t Yesu ya sāke fita bakin teku. Duk jama'a suka yi ta zuwa wurinsa, yana koya musu.
14 t Yana cikin wucewa, sai ya ga Lawi ɗan Halfa a zaune yana aiki a wurin karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.
15 Wata rana Yesu yana cin abinci a gidan Lawi, masu karɓar haraji da masu zunubi da yawa kuma suna ci tare da shi da almajiransa, don kuwa da yawa daga cikinsu masu binsa ne; 16 t to, da malaman Attaura na Farisiyawa suka ga yana cin abinci tare da masu zunubi da masu karɓar haraji, suka ce wa almajiransa, “Don me yake ci yake sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”
17 t Da Yesu ya ji haka, ya ce musu, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya. Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai masu zunubi.”Tambaya a kan Azumi
(Mat 9.14-17; Luka 5.33-39)
18 t To, almajiran Yahaya da na Farisiyawa suna azumi, sai aka zo aka ce masa, “Don me almajiran Yahaya da na Farisiyawa suke azumi, amma naka almajirai ba sa yi?” 19 Sai Yesu ya ce musu, “Ashe, abokan ango sa iya azumi tun ango na tare da su? Ai, muddin suna tare da angon, ba za su yi azumi ba. 20 t Ai, lokaci na zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi. 21 Ba mai mahon tsohuwar tufa da sabon ƙyalle. In ma an yi, ai, sai sabon ƙyallen ya kece tsohuwar tufar, har ma ta fi dā kecewa.
22 Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ma an ɗura, sai ruwan inabin ya fasa salkunan, a kuma yi hasara tasa da ta salkunan. Sabon ruwan inabi, ai sai sababbin salkuna.”Almajirai na Zagar Alkama Ran Asabar
(Mat 12.1-8; Luka 6.1-5)
23 t Wata rana ran Asabar, yana ratsa gonakin alkama, suna cikin tafiya sai almajiransa suka fara zagar alkamar. 24 t Farisiyawa suka ce masa, “Ka ga! Don me suke yin abin da bai halatta a yi ran Asabar ba?” 25 Sai ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba, sa'ad da ya matsu da yunwa, shi da abokan tafiyarsa? 26 t Yadda ya shiga masujadar Allah a zamanin Abiyata babban firist, ya ci keɓaɓɓiyar gurasan nan, wadda bai halatta kowa ya ci ba, sai firistoci kaɗai, har ma ya ba abokan tafiyarsa?” 27 t Sai ya ce musu, “Ai, Asabar domin mutum aka yi ta, ba mutum aka yi domin Asabar ba. 28 t Saboda haka Ɗan Mutum shi ne Ubangijin har da na ranar Asabar ma.”
Mark 2
1 And when he entered again into Capernaum after some days, it was noised that he was in the house.2 And many were gathered together, so that there was no longer room for them, no, not even about the door: and he spake the word unto them.3 And they come, bringing unto him a man sick of the palsy, borne of four.4 And when they could not come nigh unto him for the crowd, they uncovered the roof where he was: and when they had broken it up, they let down the bed whereon the sick of the palsy lay.5 And Jesus seeing their faith saith unto the sick of the palsy, Son, thy sins are forgiven.6 But there were certain of the scribes sitting there, and reasoning in their hearts,7 Why doth this man thus speak? he blasphemeth: who can forgive sins but one, even God?8 And straightway Jesus, perceiving in his spirit that they so reasoned within themselves, saith unto them, Why reason ye these things in your hearts?9 Which is easier, to say to the sick of the palsy, Thy sins are forgiven; or to say, Arise, and take up thy bed, and walk?10 But that ye may know that the Son of man hath authority on earth to forgive sins (he saith to the sick of the palsy),11 I say unto thee, Arise, take up thy bed, and go unto thy house.12 And he arose, and straightway took up the bed, and went forth before them all; insomuch that they were all amazed, and glorified God, saying, We never saw it on this fashion.13 And he went forth again by the sea side; and all the multitude resorted unto him, and he taught them.14 And as he passed by, he saw Levi the son of Alphaeus sitting at the place of toll, and he saith unto him, Follow me. And he arose and followed him.15 And it came to pass, that he was sitting at meat in his house, and many publicans and sinners sat down with Jesus and his disciples: for there were many, and they followed him.16 And the scribes of the Pharisees, when they saw that he was eating with the sinners and publicans, said unto his disciples, How is it that he eateth and drinketh with publicans and sinners?17 And when Jesus heard it, he saith unto them, They that are whole have no need of a physician, but they that are sick: I came not to call the righteous, but sinners.18 And John’s disciples and the Pharisees were fasting: and they come and say unto him, Why do John’s disciples and the disciples of the Pharisees fast, but thy disciples fast not?19 And Jesus said unto them, Can the sons of the bridechamber fast, while the bridegroom is with them? as long as they have the bridegroom with them, they cannot fast.20 But the days will come, when the bridegroom shall be taken away from them, and then will they fast in that day.21 No man seweth a piece of undressed cloth on an old garment: else that which should fill it up taketh from it, the new from the old, and a worse rent is made.22 And no man putteth new wine into old wineskins; else the wine will burst the skins, and the wine perisheth, and the skins: but they put new wine into fresh wine-skins.23 And it came to pass, that he was going on the sabbath day through the grainfields; and his disciples began, as they went, to pluck the ears.24 And the Pharisees said unto him, Behold, why do they on the sabbath day that which is not lawful?25 And he said unto them, Did ye never read what David did, when he had need, and was hungry, he, and they that were with him?26 How he entered into the house of God when Abiathar was high priest, and ate the showbread, which it is not lawful to eat save for the priests, and gave also to them that were with him?27 And he said unto them, The sabbath was made for man, and not man for the sabbath:28 so that the Son of man is lord even of the sabbath.