previous next

MAR 3

Mai Shanyayyen Hannu

(Mat 12.9-14; Luka 6.6-11)

1  t Sai ya sāke shiga majami'a. Akwai wani mutum a nan kuwa mai shanyayyen hannu. 2 t Sai suka yi haƙwansa su ga ko zai warkar da shi ran Asabar, don su samu su kai ƙararsa. 3 Sai ya ce wa mai shanyayyen hannun, “Fito nan fili.” 4 Ya ce musu, “Ya halatta ran Asabar a yi alheri ko kuwa mugunta? A ceci rai, ko kuwa a kashe shi?” Amma sai suka yi shiru. 5 Da ya duddube su da fushi, yana baƙin ciki da taurin zuciyarsu, sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.

6 t Da Farisiyawa suka fita, nan da nan suka yi shawara da mutanen Hirudus a kansa, yadda za su hallaka shi.

Taro Mai Yawa a Bakin Teku


7  t Sai Yesu ya tashi tare da almajiransa, suka je bakin tekun. Taro mai yawan gaske kuwa daga ƙasar Galili ya biyo shi, har ma daga ƙasar Yahudiya, 8 t da Urushalima, da ƙasar Edom, da hayin Kogin Urdun, da kuma wajen Taya da Sidon, babban taro ya zo wurinsa, don sun ji labarin duk abin da yake yi. 9 Don gudun kada taron ya mammatse shi kuwa, sai ya ce wa almajiransa su keɓe masa ƙaramin jirgi guda, 10 t saboda ya riga ya warkar da mutane da yawa, har ya kai ga duk masu cuta na dannowa wurinsa domin su taɓa shi. 11 t Baƙaƙen aljannu kuwa, duk sa'ad da suka gan shi, sai su fāɗi gabansa suna kururuwa, suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne.”

12 t Sai ya kwaɓe su ƙwarai kada su bayyana shi.

Yesu Ya Zaɓi Almajirai Sha Biyu

(Mat 10.1-4; Luka 6.12-16)


13  t Ya hau dutse, ya kira waɗanda yake so, suka je wurinsa. 14 t Ya zaɓi mutum goma sha biyu su zauna tare da shi, ya riƙa aikensu suna wa'azi. 15 t Ya kuma ba su ikon fitar da aljannu. 16 t Ga waɗanda ya zaɓa, Bitrus, 17 da Yakubu ɗan Zabadi, da kuma ɗan'uwansa Yahaya, ya sa musu suna Buwanarjis, wato 'ya'yan tsawa. 18 Sai kuma Andarawas, da Filibus, da Bartalamawas, da Matiyu, da Toma, da Yakubu ɗan Halfa, da Yahuza, da Saminu Bakan'ane,

19 da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bāshe shi.

Yesu da Ba'alzabul

(Mat 12.22-32; Luka 11.14-23)


Sa'an nan ya shiga wani gida. 20 t Taron kuwa ya sāke haɗuwa har ya hana su cin abinci. 21 t Da 'yan'uwansa suka ji haka, sai suka fita su kamo shi, saboda sun ce, “Ai, ya ruɗe.” 22 t Malaman Attaura kuwa da suka zo daga Urushalima sai suka ce, “Ai, Ba'alzabul ne ya hau shi, da ikon sarkin aljannu kuma yake fitar da aljannu.” 23 t Sai Yesu ya kira su, ya ba su misali da cewa, “Ina Shaiɗan zai iya fitar da Shaiɗan? 24 Ai, in mulki ya rabu a kan gāba, wannan mulki ba zai ɗore ba. 25 Haka in gida ya rabu a kan gāba, wannan gida ba zai ɗore ba. 26 Shaiɗan kuma in ya tayar wa kansa, ya rabu, ba zai ɗore ba, ƙarewa tasa ce ta zo.

27 t Ba mai iya shiga gidan ƙaƙƙarfan mutum ya washe kayansa, sai ko ya fara ɗaure ƙaƙƙarfan mutumin, sa'an nan kuma ya washe gidansa.
28 “Hakika, ina gaya muku, ā gafarta wa 'yan adam duk zunubansu, da kowane saɓon da suka hurta, 29 t amma fa, duk wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki ba ya samun gafara har abada, ya yi madawwamin zunubi ke nan.”

30 Wannan kuwa don sun ce, “Yana da baƙin aljan ne.”

Uwar Yesu da 'Yan'uwansa

(Mat 12.46-50; Luka 8.19-21)


31  t Sa'an nan uwa tasa da 'yan'uwansa suka zo. Suna tsaye a waje, sai suka aika masa yă je. 32 Taro kuwa na zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, “Ga tsohuwarka da 'yan'uwanka suna nemanka a waje.” 33 Ya amsa musu ya ce, “Su wane ne tsohuwata da 'yan'uwana?” 34 Sai ya waiwayi waɗanda suke zaune kewaye da shi, ya ce, “Ga tsohuwata a nan da 'yan'uwana! 35 Ai, kowa ya yi abin da Allah yake so, shi ne ɗan'uwana, ita ce 'yar'uwata, ita ce kuma tsohuwata.”

Mark 3

1 And he entered again into the synagogue; and there was a man there who had his hand withered.2 And they watched him, whether he would heal him on the sabbath day; that they might accuse him.3 And he saith unto the man that had his hand withered, Stand forth.4 And he saith unto them, Is it lawful on the sabbath day to do good, or to do harm? to save a life, or to kill? But they held their peace.5 And when he had looked round about on them with anger, being grieved at the hardening of their heart, he saith unto the man, Stretch forth thy hand. And he stretched it forth; and his hand was restored.6 And the Pharisees went out, and straightway with the Herodians took counsel against him, how they might destroy him.7 And Jesus with his disciples withdrew to the sea: and a great multitude from Galilee followed; and from Judaea,8 and from Jerusalem, and from Idumaea, and beyond the Jordan, and about Tyre and Sidon, a great multitude, hearing what great things he did, came unto him.9 And he spake to his disciples, that a little boat should wait on him because of the crowd, lest they should throng him:10 for he had healed many; insomuch that as many as had plagues pressed upon him that they might touch him.11 And the unclean spirits, whensoever they beheld him, fell down before him, and cried, saying, Thou art the Son of God.12 And he charged them much that they should not make him known.13 And he goeth up into the mountain, and calleth unto him whom he himself would; and they went unto him.14 And he appointed twelve, that they might be with him, and that he might send them forth to preach,15 and to have authority to cast out demons:16 and Simon he surnamed Peter;17 and James the son of Zebedee, and John the brother of James; and them he surnamed Boanerges, which is, Sons of thunder:18 and Andrew, and Philip, and Bartholomew, and Matthew, and Thomas, and James the son of Alphaeus, and Thaddaeus, and Simon the Cananaean,19 and Judas Iscariot, who also betrayed him. And he cometh into a house.20 And the multitude cometh together again, so that they could not so much as eat bread.21 And when his friends heard it, they went out to lay hold on him: for they said, He is beside himself.22 And the scribes that came down from Jerusalem said, He hath Beelzebub, and, By the prince of the demons casteth he out the demons.23 And he called them unto him, and said unto them in parables, How can Satan cast out Satan?24 And if a kingdom be divided against itself, that kingdom cannot stand.25 And if a house be divided against itself, that house will not be able to stand.26 And if Satan hath risen up against himself, and is divided, he cannot stand, but hath an end.27 But no one can enter into the house of the strong man, and spoil his goods, except he first bind the strong man; and then he will spoil his house.28 Verily I say unto you, All their sins shall be forgiven unto the sons of men, and their blasphemies wherewith soever they shall blaspheme:29 but whosoever shall blaspheme against the Holy Spirit hath never forgiveness, but is guilty of an eternal sin:30 because they said, He hath an unclean spirit.31 And there come his mother and his brethren; and, standing without, they sent unto him, calling him.32 And a multitude was sitting about him; and they say unto him, Behold, thy mother and thy brethren without seek for thee.33 And he answereth them, and saith, Who is my mother and my brethren?34 And looking round on them that sat round about him, he saith, Behold, my mother and my brethren!35 For whosoever shall do the will of God, the same is my brother, and sister, and mother.