previous next

MAR 4

Misali da Mai Shuka

(Mat 13.1-9; Luka 8.4-8)

1  t Ya kuma fara koyarwa a bakin teku ke nan, sai babban taro ya haɗu a wurinsa, har ya kai shi ga shiga jirgi a tekun, ya kuwa zauna a ciki. Duk taron kuwa na kan tudu a bakin tekun. 2 t Sai ya koya musu abubuwa da yawa da misalai. A cikin koyarwa tasa har ya ce musu, 3 t “Ku saurara! Wani mai shuka ya tafi shuka. 4 Yana cikin yafa iri, sai waɗansu ƙwayoyi suka faɗa a hanya, tsuntsaye kuma suka zo suka tsince su. 5 Waɗansu kuma suka faɗa a wuri mai duwatsu inda ba ƙasa da yawa. Nan da nan kuwa suka tsiro saboda rashin zurfin ƙasa. 6 Da rana fa ta ɗaga, sai suka yanƙwane, da yake ba su da saiwa sosai, suka bushe. 7 Waɗansu kuma suka faɗa cikin ƙaya, sai ƙayar ta tashi ta sarƙe su, ba su yi tsaba ba. 8 t Waɗansu kuma suka faɗa a ƙasa mai kyau, suka yi yabanya, suka girma, suka yi tsaba, waɗansu riɓi talatin talatin, waɗansu sittin sittin, waɗansu ma har ɗari ɗari.”

9 t Sai ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”

Manufar Misalan

(Mat 13.10-17; Luka 8.9-10)


10 Da suka kaɗaita, masu binsa da su sha biyun nan suka tambaye shi ma'anar misalan. 11 t Sai ya ce musu, “Ku kam, an yardar muku ku san asirin Mulkin Allah, amma ga waɗanda ba sa cikinku, kome sai a cikin misali,

12 t don gani da ido kam, su gani, amma ba da zuci ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba, wai don kada su juyo a yafe musu.”

Yesu Ya Ba da Bayanin Misalin Mai Shuka

(Mat 13.18-23; Luka 8.11-15)


13 Ya ce musu, “Ashe, ba ku fahimci wannan misali ba? Ƙaƙa za ku fahimci sauran ke nan? 14 t Mai shukan nan fa Maganar Allah yake shukawa. 15 t Waɗanda suka fāda a hanya kuwa, su ne kwatancin waɗanda aka shuka Maganar a zuciya tasu. Da zarar sun ji, nan da nan sai Shaiɗan ya zo ya ɗauke Maganar da aka shuka a zuciya tasu. 16 Haka kuma waɗanda aka shuka a wuri mai duwatsu, su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar sai su karɓa da farin ciki. 17 Su kam, ba su da tushe, rashin ƙarƙo gare su, har in wani ƙunci ko tsanani ya faru domin wannan Magana, nan da nan sai su yi tuntuɓe. 18 Waɗansu kuma su ne kwatancin waɗanda suka fāɗa cikin ƙaya, su ne waɗanda suke jin Maganar, 19 t amma taraddadin duniya, da jarabar dukiya, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa, sukan shiga su sarƙe Maganar, har ta zama marar amfani.

20 Waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa, su ne kwatancin waɗanda suke jin Maganar, su karɓa, su kuma amfana, waɗansu riɓi talatin talatin, waɗansu sittin sittin, waɗansu ma har ɗari ɗari.”

Fitila a Rufe da Masaki

(Luka 8.16-18)


21  t Sai ya ce musu, “Shin, ana kawo fitila don a rufe ta da masaki, ko a ajiye ta a ƙarƙashin gado ne, ba don a ɗora ta a kan maɗorinta ba? 22 t Ba abin da yake ɓoye, sai domin a bayyana shi a gaba. Ba kuma wani abin da yake asiri, sai domin a bayyana shi a gaba. 23 t In da mai kunnen ji, yă ji.” 24 t Sai ya ce musu, “Ku ji. Mudun da ka auna, da shi za a auna maka, har ma a ƙara.

25 t Domin mai abu akan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.”

Misali na Irin da ya Tsiro


26  t Ya ce kuma, “Mulkin Allah kamar mutum yake mai yafa iri a ƙasa. 27 A kwana a tashi har irin ya tsiro, ya girma, bai kuwa san ta yadda aka yi ba. 28 Ƙasa da kanta takan ba da amfani, tsiro shi ne na farko, sa'an nan kai, sai kuma ƙwaƙƙwarar ƙwaya a kan.

29 t Sa'ad da amfani ya nuna, sai ya sa lauje ya yanke nan da nan, wato kaka ta yi ke nan.”

Misali na Ƙwayar Mastad

(Mat 13.31-32; Luka 13.18-19)


30  t Ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta Mulkin Allah? Ko kuwa da wane misali za mu misalta shi? 31 Kamar ƙwayar mastad da yake, wadda, in an shuka ta, ko da yake ita ce mafi ƙanƙantar ƙwayoyi a duniya,

32 duk da haka in an shuka ta, sai ta girma ta fi duk sauran ganye, ta yi manyan rassa, har tsuntsaye su iya sauka a inuwarta.”

Yesu Ya Yi Amfani da Misalai

(Mat 13.34-35)


33  t Da misalai da yawa irin waɗannan Yesu ya yi musu Maganar Allah, daidai gwargwadon ganewa tasu.

34 t Ba ya faɗa musu kome sai da misali, amma a keɓe yakan bayyana wa almajiransa kome.

Yesu Ya Tsawata wa Hadiri

(Mat 8.23-27; Luka 8.22-25)


35 A ran nan da maraice ya ce musu, “mu haye can ƙetare.” 36 t Da suka bar taron, suka tafi da shi yadda yake a cikin jirgin, waɗansu jirage kuma na tare da shi. 37 Sai babban hadari mai iska ya taso, raƙuman ruwa kuma na ta fantsama cikin jirgin, har jirgin ya tasar wa cika da ruwa. 38 Yesu kuwa na daga ƙarshen baya na jirgin a kan matashi, yana barci. Sai suka tashe shi, suka ce masa, “Malam, za mu hallaka ba ka kula ba ko?” 39 Sai ya farka, ya tsawata wa iskar, ya kuma ce wa ruwan tekun, “Natsu! Ka yi shiru!” Sai iskar ta kwanta, wurin duk ya yi tsit. 40 t Ya ce musu, “Don me kuka firgita haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya ne?” 41 Sai suka tsorata, matuƙar tsoro, suka ce wa juna, “Wa ke nan kuma, wanda har iska da ruwan teku ma suke yi masa biyayya?”

Mark 4

1 And again he began to teach by the sea side. And there is gathered unto him a very great multitude, so that he entered into a boat, and sat in the sea; and all the multitude were by the sea on the land.2 And he taught them many things in parables, and said unto them in his teaching,3 Hearken: Behold, the sower went forth to sow:4 and it came to pass, as he sowed, some seed fell by the way side, and the birds came and devoured it.5 And other fell on the rocky ground, where it had not much earth; and straightway it sprang up, because it had no deepness of earth:6 and when the sun was risen, it was scorched; and because it had no root, it withered away.7 And other fell among the thorns, and the thorns grew up, and choked it, and it yielded no fruit.8 And others fell into the good ground, and yielded fruit, growing up and increasing; and brought forth, thirtyfold, and sixtyfold, and a hundredfold.9 And he said, Who hath ears to hear, let him hear.10 And when he was alone, they that were about him with the twelve asked of him the parables.11 And he said unto them, Unto you is given the mystery of the kingdom of God: but unto them that are without, all things are done in parables:12 that seeing they may see, and not perceive; and hearing they may hear, and not understand; lest haply they should turn again, and it should be forgiven them.13 And he saith unto them, Know ye not this parable? and how shall ye know all the parables?14 The sower soweth the word.15 And these are they by the way side, where the word is sown; and when they have heard, straightway cometh Satan, and taketh away the word which hath been sown in them.16 And these in like manner are they that are sown upon the rocky places, who, when they have heard the word, straightway receive it with joy;17 and they have no root in themselves, but endure for a while; then, when tribulation or persecution ariseth because of the word, straightway they stumble.18 And others are they that are sown among the thorns; these are they that have heard the word,19 and the cares of the world, and the deceitfulness of riches, and the lusts of other things entering in, choke the word, and it becometh unfruitful.20 And those are they that were sown upon the good ground; such as hear the word, and accept it, and bear fruit, thirtyfold, and sixtyfold, and a hundredfold.21 And he said unto them, Is the lamp brought to be put under the bushel, or under the bed, and not to be put on the stand?22 For there is nothing hid, save that it should be manifested; neither was anything made secret, but that it should come to light.23 If any man hath ears to hear, let him hear.24 And he said unto them, Take heed what ye hear: with what measure ye mete it shall be measured unto you; and more shall be given unto you.25 For he that hath, to him shall be given: and he that hath not, from him shall be taken away even that which he hath.26 And he said, So is the kingdom of God, as if a man should cast seed upon the earth;27 and should sleep and rise night and day, and the seed should spring up and grow, he knoweth not how.28 The earth beareth fruit of herself; first the blade, then the ear, then the full grain in the ear.29 But when the fruit is ripe, straightway he putteth forth the sickle, because the harvest is come.30 And he said, How shall we liken the kingdom of God? or in what parable shall we set it forth?31 It is like a grain of mustard seed, which, when it is sown upon the earth, though it be less than all the seeds that are upon the earth,32 yet when it is sown, groweth up, and becometh greater than all the herbs, and putteth out great branches; so that the birds of the heaven can lodge under the shadow thereof.33 And with many such parables spake he the word unto them, as they were able to hear it;34 and without a parable spake he not unto them: but privately to his own disciples he expounded all things.35 And on that day, when even was come, he saith unto them, Let us go over unto the other side.36 And leaving the multitude, they take him with them, even as he was, in the boat. And other boats were with him.37 And there ariseth a great storm of wind, and the waves beat into the boat, insomuch that the boat was now filling.38 And he himself was in the stern, asleep on the cushion: and they awake him, and say unto him, Teacher, carest thou not that we perish?39 And he awoke, and rebuked the wind, and said unto the sea, Peace, be still. And the wind ceased, and there was a great calm.40 And he said unto them, Why are ye fearful? have ye not yet faith?41 And they feared exceedingly, and said one to another, Who then is this, that even the wind and the sea obey him?