MAT 10
Yesu Ya Zaɓi Almajirai Sha Biyu
(Mar 3.13-19; Luka 6.12-16)
1 t Sai ya kira almajiransa goma sha biyu, ya kuma ba su ikon fitar da baƙaƙen aljannu, su warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
2 To, ga sunayen manzannin nan goma sha biyu. Da fari, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, da Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya, 3 da Filibus, da Bartalamawas, da Toma, da Matiyu mai karɓar haraji, da Yakubu ɗan Halfa, da Yahuza,
4 t da Saminu Bakan'ane, da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bashe shi.Yesu Ya Aiki Sha Biyu Ɗin
(Mar 6.7-13; Luka 9.1-6)
5 t Su sha biyun nan ne Yesu ya aika, ya yi musu umarni, ya ce, “Kada ku shiga ƙasar al'ummai, ko kuma kowane garin Samariyawa. 6 t Sai dai ku je wurin batattun tumakin jama'ar Isra'ila,Irm 7 t kuna tafiya, kuna wa'azi, kuna cewa, ‘Mulkin Sama ya kusato.’ 8 Ku warkar da marasa lafiya, ku ta da matattu, ku tsarkake kutare, ku kuma fitar da aljannu. Kyauta kuka samu, ku kuma bayar kyauta. 9 t Kada ku riƙi kuɗin zinariya, ko na azurfa, ko na tagulla a ɗamararku, 10 t kada kuma ku ɗauki burgami a tafiyarku, ko taguwa biyu, ko takalma, ko sanda, don ma'aikaci ya cancanci hakkinsa. 11 Duk gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a cikinsa, ku kuma baƙunce shi har ku tashi. 12 t In za ku shiga gidan ku ce, ‘Salama alaiku.’ 13 In gidan na kirki ne, salamarku tă tabbata a gare shi. In kuwa ba na kirki ba ne, to, tă komo muku. 14 t Kowa kuma ya ƙi yin na'am da ku, ko kuwa ya ƙi sauraron maganarku, da fitarku gidan ko garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku.
15 t Hakika, ina gaya muku, a Ranar Shari'a za a fi haƙurce wa ƙasar Saduma da ta Gwamrata a kan garin nan.”Tsanani Mai Zuwa
(Mar 13.9-13; Luka 12.11-12; Luka 21.12-19)
16 t “Ga shi, na aike ku kamar tumaki a tsakiyar kyarketai. Don haka sai ku zama masu azanci kamar macizai, da kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi. 17 t Ku yi hankali da mutane, don za su kai ku gaban majalisa, su kuma yi muku bulala a majami'arsu. 18 t Za su kuma ja ku gaban mahukunta da sarakuna saboda ni, domin ku ba da shaida a gabansu, a gaban al'ummai kuma. 19 t A lokacin da suka ba da ku, kada ku damu da yadda za ku yi magana, ko kuwa abin da za ku faɗa, domin za a ba ku abin da za ku faɗa a lokacin. 20 t Domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhun Ubanku ne yake magana ta bakinku. 21 t 'Dan'uwa zai ba da ɗan'uwansa a kashe shi, uba kuwa ɗansa. 'Ya'ya kuma za su tayar wa iyayensu, har su sa a kashe su. 22 t Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu.
23 In sun tsananta muku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Gaskiya, ina gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra'ila, Ɗan Mutum zai zo.
24 t “Almajiri ba ya fin malaminsa, bawa kuma ba ya fin ubangijinsa.
25 t Ya isa wa almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira maigida Ba'alzabul, to, mutanen gidansa kuma fa?”Wanda Za a Ji Tsoro
(Luka 12.2-7)
26 t “Don haka kada ku ji tsoronsu, domin ba abin da yake a rufe da ba zai tonu ba, ko kuwa abin da yake ɓoye da ba za a bayyana ba. 27 Abin da nake gaya muku a asirce, ku faɗa a sarari. Abin da kuma kuka ji a raɗe, ku yi shelarsa daga kan soraye. 28 t Kada ku ji tsoron masu kisan mutum, amma ba sa iya kashe kurwarsa. Sai dai ku ji tsoron wannan da yake da ikon hallaka kurwar da jikin duka a Gidan Wuta. 29 Ashe, ba gwara biyu ne kobo ba? Ba kuwa ɗayarsu da za ta mutu, ba da yardar Ubanku ba. 30 t Ai, ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye yake.
31 t Kada ku ji tsoro. Ai, martabarku ta fi ta gwara masu yawa.”Bayyana Yarda da Almasihu gaban Mutane
(Luka 12.8-9)
32 t “Kowa ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin Sama.
33 t Duk wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, ni ma zan yi musun saninsa a gaban Ubanmu da yake cikin Sama.”Ban Kawo Salama Ba, Sai Takobi
(Luka 12.51-53; 14.26-27)
34 “Kada dai ku zaci na zo ne in kawo salama a duniya. A'a, ban zo domin in kawo salama ba, sai dai takobi. 35 t Domin na zo ne in haɗa mutum da ubansa gāba, 'ya da uwatata, matar ɗa kuma da surukarta. 36 t Zai zamana kuma magabtan mutum su ne mutanen gidansa. 37 t Wanda duk ya fi son ubansa ko uwarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son ɗansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. 38 t Wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai cancanci zama nawa ba.
39 t Duk mai son adana ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, adana shi yake yi.”Ayyukan Lada
(Mar 9.41)
40 t “Wanda ya yi na'am da ku, ya yi na'am da ni ke nan. Wanda ya yi na'am da ni kuwa, to, ya yi na'am da wanda ya aiko ni. 41 Wanda ya yi na'am da wani annabi domin shi annabi ne, zai sami ladar annabi. Wanda kuma ya yi na'am da adali domin shi adali ne, zai sami ladar adali. 42 t Kowa ya ba ɗaya daga cikin 'yan yaran nan, ko da moɗa guda ta baƙin ruwa, kan shi almajirina ne, hakika, ina gaya muku, ba zai rasa ladarsa ba.”
Matthew 10
1 And he called unto him his twelve disciples, and gave them authority over unclean spirits, to cast them out, and to heal all manner of disease and all manner of sickness.
2 Now the names of the twelve apostles are these: The first, Simon, who is called Peter, and Andrew his brother; James the son of Zebedee, and John his brother;3 Philip, and Bartholomew; Thomas, and Matthew the publican; James the son of Alphaeus, and Thaddaeus;4 Simon the Cananaean, and Judas Iscariot, who also betrayed him.
5 These twelve Jesus sent forth, and charged them, saying, Go not into any way of the Gentiles, and enter not into any city of the Samaritans:6 but go rather to the lost sheep of the house of Israel.7 And as ye go, preach, saying, The kingdom of heaven is at hand.8 Heal the sick, raise the dead, cleanse the lepers, cast out demons: freely ye received, freely give.9 Get you no gold, nor silver, nor brass in your purses;10 no wallet for your journey, neither two coats, nor shoes, nor staff: for the laborer is worthy of his food.11 And into whatsoever city or village ye shall enter, search out who in it is worthy; and there abide till ye go forth.12 And as ye enter into the house, salute it.13 And if the house be worthy, let your peace come upon it: but if it be not worthy, let your peace return to you.14 And whosoever shall not receive you, nor hear your words, as ye go forth out of that house or that city, shake off the dust of your feet.15 Verily I say unto you, It shall be more tolerable for the land of Sodom and Gomorrah in the day of judgment, than for that city.
16 Behold, I send you forth as sheep in the midst of wolves: be ye therefore wise as serpents, and harmless as doves.17 But beware of men: for they will deliver you up to councils, and in theirs synagogues they will scourge you;18 yea and before governors and kings shall ye be brought for my sake, for a testimony to them and to the Gentiles.19 But when they deliver you up, be not anxious how or what ye shall speak: for it shall be given you in that hour what ye shall speak.20 For it is not ye that speak, but the Spirit of your Father that speaketh in you.21 And brother shall deliver up brother to death, and the father his child: and children shall rise up against parents, and cause them to be put to death.22 And ye shall be hated of all men for my name’s sake: but he that endureth to the end, the same shall be saved.23 But when they persecute you in this city, flee into the next: for verily I say unto you, Ye shall not have gone through the cities of Israel, till the Son of man be come.
24 A disciple is not above his teacher, nor a servant above his lord.25 It is enough for the disciple that he be as his teacher, and the servant as his lord. If they have called the master of the house Beelzebub, how much more them of his household!26 Fear them not therefore: for there is nothing covered, that shall not be revealed; and hid, that shall not be known.27 What I tell you in the darkness, speak ye in the light; and what ye hear in the ear, proclaim upon the house-tops.28 And be not afraid of them that kill the body, but are not able to kill the soul: but rather fear him who is able to destroy both soul and body in hell.29 Are not two sparrows sold for a penny? and not one of them shall fall on the ground without your Father:30 but the very hairs of your head are all numbered.31 Fear not therefore: ye are of more value than many sparrows.32 Every one therefore who shall confess me before men, him will I also confess before my Father who is in heaven.33 But whosoever shall deny me before men, him will I also deny before my Father who is in heaven.
34 Think not that I came to send peace on the earth: I came not to send peace, but a sword.35 For I came to set a man at variance against his father, and the daughter against her mother, and the daughter in law against her mother in law:36 and a man’s foes shall be they of his own household.37 He that loveth father or mother more than me is not worthy of me; and he that loveth son or daughter more than me is not worthy of me.38 And he that doth not take his cross and follow after me, is not worthy of me.39 He that findeth his life shall lose it; and he that loseth his life for my sake shall find it.
40 He that receiveth you receiveth me, and he that receiveth me receiveth him that sent me.41 He that receiveth a prophet in the name of a prophet shall receive a prophet’s reward: and he that receiveth a righteous man in the name of a righteous man shall receive a righteous man’s reward.42 And whosoever shall give to drink unto one of these little ones a cup of cold water only, in the name of a disciple, verily I say unto you he shall in no wise lose his reward.