MAT 13
Misali da Mai Shuka
(Mar 4.1-9; Luka 8.4-8)
1 t A ran nan Yesu ya fita daga gidan, ya je ya zauna a bakin teku.
2 t Taro masu yawan gaske suka haɗu a wurinsa, har ya kai shi ga shiga jirgi, ya zauna. Duk taron kuwa suka tsaya a bakin gaci.
3 Sai ya gaggaya musu abubuwa da yawa da misalai, ya ce, “Wani mai shuka ya je shuka. 4 Yana cikin yafa iri sai waɗansu ƙwayoyi suka faɗa a hanya, sai tsuntsaye suka zo suka tsince su. 5 Waɗansu kuma suka faɗa a wuri mai duwatsu inda ba ƙasa da yawa. Nan da nan sai suka tsiro saboda rashin zurfin ƙasa. 6 Da rana fa ta ɗaga, sai suka yanƙwane, da yake ba su da saiwa sosai, suka bushe. 7 Waɗansu kuma suka faɗa cikin ƙaya, sai ƙaya ta tashi ta sarƙe su. 8 t Waɗansu kuma suka faɗa a ƙasa mai kyau, suka yi tsaba, waɗansu riɓi ɗari ɗari, waɗansu sittin sittin, waɗansu kuma talatin talatin.
9 t Duk mai kunnen ji, yă ji.”Manufar Misalan
(Mar 4.10-12; Luka 8.9-10)
10 Sai almajiran suka zo, suka ce masa, “Me ya sa kake musu magana da misalai?” 11 t Ya amsa musu ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Sama, amma su ba a ba su ba. 12 t Domin mai abu akan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa. 13 t Shi ya sa nake musu magana da misalai, don ko sun duba ba sa gani, ko sun saurara ba sa ji, ba sa kuma fahimta.
14 Lalle a kansu ne aka cika annabcin Ishaya cewa,
‘Za ku ji kam, amma ba za ku fahimta ba faufau,
Za ku kuma gani, amma ba za ku gane ba faufau,
15 t Don zuciyar jama'ar nan ta yi kanta,
Sun toshe kunnuwansu,
Sun kuma runtse idanunsu,
Don kada su gani da idanunsu,
Su kuma ji da kunnuwansu,
Su kuma fahimta a zuciyarsu,
Har su juyo gare ni in warkar da su.’
16 t Albarka tā tabbata ga idanunku domin suna gani, da kuma kunnuwanku domin suna ji.
17 t Hakika, ina gaya muku, annabawa da adalai da yawa sun yi ɗokin ganin abin da kuke gani, amma ba su gani ba, su kuma ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.Yesu Ya Ba Da Bayanin Misalin Mai Shuka
(Mar 4.13-20; Luka 8.11-15)
18 “To, ga ma'anar misalin mai shukar nan. 19 t Wanda duk ya ji Maganar Mulki bai kuma fahimce ta ba, sai Mugun ya zo ya zăre abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya faɗa a hanya. 20 Wanda ya faɗa a wuri mai duwatsu kuwa, shi ne wanda da zarar ya ji Maganar Allah, sai ya karɓa da farin ciki. 21 t Amma kuwa ba shi da tushe, rashin ƙarƙo gare shi kuma, har in wani ƙunci ko tsanani ya faru saboda Maganar, sai ya yi tuntuɓe. 22 t Wanda ya faɗa cikin ƙaya kuwa, shi ne wanda ya ji Maganar, amma taraddadin duniya da jarabar dukiya sukan sarƙe Maganar, har ta zama marar amfani.
23 t Wanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa, shi ne wanda yake jin Maganar, ya kuma fahimce ta. Hakika shi ne mai yin amfani har ya yi albarka, wani riɓi ɗari, wani sittin, wani kuma talatin.”Ciyayi a Cikin Alkama
24 t Ya kawo musu wani misali kuma, ya ce, “Za a kwatanta Mulkin Sama da mutumin da ya yafa iri mai kyau a gonarsa. 25 Sa'ad da mutane suke barci, sai anokin gābansa ya je ya yafa irin wata ciyawa a cikin alkamar, ya tafi abinsa. 26 Da shukar ta tashi, ta yi ƙwaya, sai ciyawar ta bayyana. 27 Sai bayin maigidan suka zo, suka ce masa, ‘Maigida, ashe, ba kyakkyawan iri ka yafa a gonarka ba? To, ta yaya ke nan ta yi ciyawa?’ 28 Sai ya ce musu, ‘Wani magabci ne ya yi wannan aiki.’ Bayin suka ce masa, ‘To, kana so mu je mu cire mu tara ta?’ 29 Amma ya ce, ‘A'a, kada garin cire ciyawar ku tumɓuke har da alkamar ma.
30 t Ku bari su zauna tare har lokacin yanka. A lokacin yanka kuma zan gaya wa masu yankan su fara yanke ciyawar su tara, su ɗaure dami dami a ƙone, alkamar kuwa su taro ta su sa a taskata.’ ”Misali da Ƙwayar Mastad
(Mar 4.30-32; Luka 13.18-19)
31 t Ya kawo musu wani misali, ya ce, “Mulkin Sama kamar ƙwayar mastad yake, wadda wani mutum ya je ya shuka a lambunsa.
32 t Ita ce mafi ƙanƙanta a cikin ƙwayoyi, amma in ta girma, sai ta fi duk sauran ganyaye, har ta zama itace, har ma tsuntsaye su zo su yi sheƙarsu a rassanta.”Misali na Yisti
(Luka 13.20-21)
33 t Ya kuma ba su wani misali, ya ce, “Mulkin Sama kamar yisti yake, wanda wata mace ta ɗauka ta cuɗe da mudu uku na garin alkama, har duk garin ya game da yistin.”Yesu Ya Yi Amfani da Misalai
(Mar 4.33-34)
34 t Yesu ya gaya wa taro duk waɗannan abubuwa da misalai. Ba ya faɗa musu kome sai da misali.
35 t Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa,
“Zan yi magana da misalai,
Zan sanar da abin da yake ɓoye tun farkon duniya.”Yesu Ya Ba Da Bayanin Misalin Ciyayi a Cikin Alkama
36 t Sai ya bar taron, ya shiga gida. Almajiransa kuma suka zo gare shi, suka ce, “Ka fassara mana misalin nan na ciyawa a gonar.” 37 t Ya amsa ya ce, “Mai yafa kyakkyawan irin nan, shi ne Ɗan Mutum. 38 t Gonar kuwa ita ce duniya, kyakkyawan irin nan, su ne 'ya'yan Mulkin Allah, ciyawar kuwa, 'ya'yan Mugun ne. 39 t Magabcin nan da ya yafa ta kuwa, Iblis ne. Lokacin yankan kuwa, ƙarshen duniya ne, masu yankan kuma, mala'iku ne. 40 Kamar yadda ake tara ciyawa a ƙone ta, haka zai kasance a ƙarshen duniya. 41 t Ɗan Mutum zai aiko mala'ikunsa, za su tattaro duk masu sa mutane laifi, da kuma duk masu yin mugun aiki, su fitar da su daga Mulkinsa, 42 t su kuma jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon haƙora.
43 t Sa'an nan ne masu adalci za su haskaka kamar rana a Mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.”Dukiyar da Take Binne
44 t “Mulkin Sama kamar dukiya yake da take binne a gona, wadda wani ya samu, ya sāke binnewa. Yana tsaka da murna tasa, sai ya je ya sayar da dukan mallaka tasa, ya sayi gonar.”Lu'ulu'u Mai Tamanin Gaske
45 t “Har wa yau kuma Mulkin Sama kamar attajiri yake, mai neman lu'ulu'u masu daraja.
46 Da ya sami lu'ulu'u ɗaya mai tamanin gaske, sai ya je ya sai da dukan mallaka tasa, ya saye shi.”Taru
47 t “Har wa yau kuma Mulkin Sama kamar taru yake da aka jefa a teku, ya kamo kifi iri iri. 48 Da ya cika, aka jawo shi gaci, aka zauna, aka tsince kyawawan kifi, aka zuba a goruna, munanan kuwa aka watsar. 49 t Haka zai kasance a ƙarshen duniya. Mala'iku za su fito, su ware mugaye daga masu adalci,
50 t su jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon hakora.”Sabuwar Dukiya da Tsohuwa
51 “Kun fahimci duk wannan?” Suka ce masa, “I.”
52 Sai ya ce musu, “To, duk malamin Attaura da ya zama almajirin Mulkin Sama, kamar maigida yake, wanda ya ɗebo dukiya sabuwa da tsohuwa daga taskarsa.”An Ƙi Yesu a Nazarat
(Mar 6.1-6; Luka 4.16-30)
53 t Da Yesu ya gama waɗannan misalai, sai ya tashi daga nan. 54 t Da ya zo garinsu, ya koya musu a majami'arsu, har suka yi mamaki, suka ce, “Daga ina mutumin nan ya sami wannan hikima haka, da kuma mu'ujizan nan? 55 t Ashe, wannan ba ɗan masassaƙin nan ba ne? Uwa tasa ba sunanta Maryamu ba? 'Yan'uwansa kuwa ba su ne Yakubu, da Yusufu, da Saminu, da kuma Yahuza ba? 56 'Yan'uwansa mata ba duk tare da mu suke ba? To a ina ne mutumin nan ya sami waɗannan abu duka?” 57 t Sai suka yi tuntuɓe sabili da shi. Amma Yesu ya ce musu, “Ai, annabi ba ya rasa girma sai dai a garinsu da kuma a gidansu.” 58 Bai kuma yi mu'ujizai masu yawa a can ba, saboda rashin bangaskiyarsu.
Matthew 13
1 On that day went Jesus out of the house, and sat by the sea side.2 And there were gathered unto him great multitudes, so that he entered into a boat, and sat; and all the multitude stood on the beach.3 And he spake to them many things in parables, saying, Behold, the sower went forth to sow;4 and as he sowed, some seeds fell by the way side, and the birds came and devoured them:5 and others fell upon the rocky places, where they had not much earth: and straightway they sprang up, because they had no deepness of earth:6 and when the sun was risen, they were scorched; and because they had no root, they withered away.7 And others fell upon the thorns; and the thorns grew up and choked them:8 and others fell upon the good ground, and yielded fruit, some a hundredfold, some sixty, some thirty.9 He that hath ears, let him hear.
10 And the disciples came, and said unto him, Why speakest thou unto them in parables?11 And he answered and said unto them, Unto you it is given to know the mysteries of the kingdom of heaven, but to them it is not given.12 For whosoever hath, to him shall be given, and he shall have abundance: but whosoever hath not, from him shall be taken away even that which he hath.13 Therefore speak I to them in parables; because seeing they see not, and hearing they hear not, neither do they understand.14 And unto them is fulfilled the prophecy of Isaiah, which saith, By hearing ye shall hear, and shall in no wise understand; And seeing ye shall see, and shall in no wise perceive:
15 For this people’s heart is waxed gross, And their ears are dull of hearing, And their eyes they have closed; Lest haply they should perceive with their eyes, And hear with their ears, And understand with their heart, And should turn again, And I should heal them.
16 But blessed are your eyes, for they see; and your ears, for they hear.17 For verily I say unto you, that many prophets and righteous men desired to see the things which ye see, and saw them not; and to hear the things which ye hear, and heard them not.18 Hear then ye the parable of the sower.19 When any one heareth the word of the kingdom, and understandeth it not, then cometh the evil one, and snatcheth away that which hath been sown in his heart. This is he that was sown by the way side.20 And he that was sown upon the rocky places, this is he that heareth the word, and straightway with joy receiveth it;21 yet hath he not root in himself, but endureth for a while; and when tribulation or persecution ariseth because of the word, straightway he stumbleth.22 And he that was sown among the thorns, this is he that heareth the word; and the care of the world, and the deceitfulness of riches, choke the word, and he becometh unfruitful.23 And he that was sown upon the good ground, this is he that heareth the word, and understandeth it; who verily beareth fruit, and bringeth forth, some a hundredfold, some sixty, some thirty.
24 Another parable set he before them, saying, The kingdom of heaven is likened unto a man that sowed good seed in his field:25 but while men slept, his enemy came and sowed tares also among the wheat, and went away.26 But when the blade sprang up and brought forth fruit, then appeared the tares also.27 And the servants of the householder came and said unto him, Sir, didst thou not sow good seed in thy field? whence then hath it tares?28 And he said unto them, An enemy hath done this. And the servants say unto him, Wilt thou then that we go and gather them up?29 But he saith, Nay; lest haply while ye gather up the tares, ye root up the wheat with them.30 Let both grow together until the harvest: and in the time of the harvest I will say to the reapers, Gather up first the tares, and bind them in bundles to burn them; but gather the wheat into my barn.
31 Another parable set he before them, saying, The kingdom of heaven is like unto a grain of mustard seed, which a man took, and sowed in his field:32 which indeed is less than all seeds; but when it is grown, it is greater than the herbs, and becometh a tree, so that the birds of the heaven come and lodge in the branches thereof.
33 Another parable spake he unto them; The kingdom of heaven is like unto leaven, which a woman took, and hid in three measures of meal, till it was all leavened.
34 All these things spake Jesus in parables unto the multitudes; and without a parable spake he nothing unto them:35 that it might be fulfilled which was spoken through the prophet, saying, I will open my mouth in parables; I will utter things hidden from the foundation of the world.
36 Then he left the multitudes, and went into the house: and his disciples came unto him, saying, Explain unto us the parable of the tares of the field.37 And he answered and said, He that soweth the good seed is the Son of man;38 and the field is the world; and the good seed, these are the sons of the kingdom; and the tares are the sons of the evil one;39 and the enemy that sowed them is the devil: and the harvest is the end of the world; and the reapers are angels.40 As therefore the tares are gathered up and burned with fire; so shall it be in the end of the world.41 The Son of man shall send forth his angels, and they shall gather out of his kingdom all things that cause stumbling, and them that do iniquity,42 and shall cast them into the furnace of fire: there shall be the weeping and the gnashing of teeth.43 Then shall the righteous shine forth as the sun in the kingdom of their Father. He that hath ears, let him hear.
44 The kingdom of heaven is like unto a treasure hidden in the field; which a man found, and hid; and in his joy he goeth and selleth all that he hath, and buyeth that field.
45 Again, the kingdom of heaven is like unto a man that is a merchant seeking goodly pearls:46 and having found one pearl of great price, he went and sold all that he had, and bought it.
47 Again, the kingdom of heaven is like unto a net, that was cast into the sea, and gathered of every kind:48 which, when it was filled, they drew up on the beach; and they sat down, and gathered the good into vessels, but the bad they cast away.49 So shall it be in the end of the world: the angels shall come forth, and sever the wicked from among the righteous,50 and shall cast them into the furnace of fire: there shall be the weeping and the gnashing of teeth.
51 Have ye understood all these things? They say unto him, Yea.52 And he said unto them, Therefore every scribe who hath been made a disciple to the kingdom of heaven is like unto a man that is a householder, who bringeth forth out of his treasure things new and old.
53 And it came to pass, when Jesus had finished these parables, he departed thence.
54 And coming into his own country he taught them in their synagogue, insomuch that they were astonished, and said, Whence hath this man this wisdom, and these mighty works?55 Is not this the carpenter’s son? is not his mother called Mary? and his brethren, James, and Joseph, and Simon, and Judas?56 And his sisters, are they not all with us? Whence then hath this man all these things?57 And they were offended in him. But Jesus said unto them, A prophet is not without honor, save in his own country, and in his own house.58 And he did not many mighty works there because of their unbelief.