previous next

MAT 18

Wane ne Mafi Girma?

(Mar 9.33-37; Luka 9.46-48)

1 A lokacin nan almajirai suka zo wurin Yesu, suka ce, “Wa ya fi girma duka a Mulkin Sama?” 2 Sai ya kira wani ƙaramin yaro, ya sa shi a tsakiyarsu, 3 t ya ce, “Hakika, ina gaya muku, in ba kun juyo kun zama kamar ƙananan yara ba, har abada ba za ku shiga Mulkin Sama ba.

4 t Duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar ɗan yaron nan, ai, shi ne mafi girma a Mulkin Sama.
5  t “Wanda duk ya karɓi ƙaramin yaro ɗaya kamar wannan saboda sunana, Ni ya karɓa.

6 t Amma fa duk wanda ya sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara masu gaskatawa da ni ya yi laifi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.”

Sanadodin Yin Zunubi

(Mar 9.42-48; Luka 17.1-2)


7  t “Kaiton duniya saboda sanadodin tuntuɓe! Lalle sanadodin tuntuɓe ba su da makawa, duk da haka kaiton wanda shi ne sanadin! 8 t In kuwa hannunka ko ƙafarka suna sa ka laifi, to, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai dungu ko da gurguntaka, da a jefa ka madawwamiyar wuta da hannu biyu ko ƙafa biyu.

9 t In kuwa idonka yana sa ka laifi, to ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da ido ɗaya, da a jefa ka Gidan Wuta da ido biyu.”

Misali na Ɓatacciyar Tunkiya

(Luka 15.3-7)


10  t “Ku dai lura, kada ku raina ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara. Ina gaya muku, mala'ikunsu a Sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin Sama.[ 11 Domin Ɗan Mutum ya zo ne musamman ceton abin da ya ɓata.] 12 To, me kuka gani? In wani na da tumaki ɗari, ɗayarsu ta băce, ashe, ba zai bar tasa'in da taran nan a gindin dutse, ya je neman wadda ta ɓăce ba? 13 In kuwa ya samo ta, labudda, ina gaya muku, ai, farin cikin da yake yi a kanta ya fi na tasa'in da taran nan da ba su taɓa ɓăcewa ba.

14 Haka ma, ba nufin Ubanku da yake cikin Sama ba ne ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara ya hallaka.”

Ɗan'uwan da Ya Yi Laifi

(Luka 17.3)


15  t “In ɗan'uwanka ya yi maka laifi, sai ka je, ka gaya masa laifinsa, kai da shi, ku kaɗai. In ya saurare ka, to, kā maido da ɗan'uwanka ke nan. 16 t In kuwa bai saurare ka ba, sai ka tafi da mutum ɗaya ko biyu, don a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.

17 t In kuma ya ƙi sauraronsu, sai ka shaida wa ikilisiya. In kuma har ya ƙi sauraron ikilisiyar, ka maishe shi kamar bare, ko mai karɓar haraji.”

Kullewa da Warwarewa


18  t “Hakika, ina gaya muku, kome kuka ƙulla a duniya, zai zama abin da aka riga ƙullewa a Sama ne. Kome kuka warware a duniya, zai zama abin da aka riga warwarewa a Sama ne. 19 t Har wa yau dai ina gaya muku, in mutum biyu daga cikinku, ra'ayinsu ya zo ɗaya a nan duniya a kan wani abin da za su roƙa, Ubana kuwa da yake Sama zai yi musu shi.

20 Gama kuwa inda mutum biyu ko uku suka taru saboda sunana, ni ma ina nan a tsakiyarsu.”

Misali na Bawa Wanda Bai Yafe Ba


21  t Sai Bitrus ya matso ya ce masa, “Ya Ubangiji, sau nawa ɗan'uwana zai yi mini laifi in yafe masa? Har sau bakwai?”

22 t Yesu ya ce masa, “Ba sau bakwai kawai na ce maka ba, sai dai bakwai har saba'in.
23  t “Saboda haka za a misalta Mulkin Sama da wani sarkin da yake so ya yi ƙididdigar dukiyarsa da yake hannun bayinsa. 24 Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wanda yake bi talanti dubu goma bashi. 25 t Da yake ya gagara biya, sai ubangidansa ya yi umarni a sayar da shi da mata tasa da 'ya'yansa da kuma duk abin da ya mallaka, a biya kuɗin. 26 t Sai bawan ya faɗi a gabansa ya yi masa ladabi, ya ce, ‘Ya ubangida, ka yi mini haƙuri, zan biya ka tsaf.’ 27 Saboda tausayin bawan nan ubangidansa ya sake shi, ya yafe masa bashin. 28 Amma wannan bawa, da fitarsa sai ya tarar da wani abokin bautarsa, wanda yake bi dinari ɗari bashi. Ya cafi wuyarsa, ya ce, ‘Biya ni abin da nake binka.’ 29 Sai abokin bautarsa ya faɗi a gabansa, ya yi ta roƙonsa ya ce, ‘Ka yi mini haƙuri, ai, zan biya ka.’ 30 Amma ya ƙi, ya kuma je ya sa shi a kurkuku, har yā biya bashin. 31 Da abokan bautarsa suka ga abin da ya faru, suka yi baƙin ciki gaya, har suka je suka gaya wa ubangidansu duk abin da ya gudana. 32 Sai ubangiji nasa ya kira shi, ya ce masa, ‘Kai mugun bawa ne! Na yafe maka duk bashin nan saboda ka roƙe ni, 33 ashe, bai kyautu kai ma ka ji tausayin abokin bautarka, kamar yadda na ji tausayinka ba?’ 34 Ubangijinsa ya yi fushi, ya ba da shi ga masu azabtarwa har yă biya duk bashin da ake binsa. 35 t Haka kuma Ubana da yake Sama zai yi da ko wannenku, in ba ku yafe wa 'yan'uwanku da zuciya ɗaya ba.”

Matthew 18

1 In that hour came the disciples unto Jesus, saying, Who then is greatest in the kingdom of heaven?2 And he called to him a little child, and set him in the midst of them,3 and said, Verily I say unto you, Except ye turn, and become as little children, ye shall in no wise enter into the kingdom of heaven.4 Whosoever therefore shall humble himself as this little child, the same is the greatest in the kingdom of heaven.5 And whoso shall receive one such little child in my name receiveth me:6 But whoso shall cause one of these little ones that believe on me to stumble, it is profitable for him that a great millstone should be hanged about his neck, and that he should be sunk in the depth of the sea.

7 Woe unto the world because of occasions of stumbling! for it must needs be that the occasions come; but woe to that man through whom the occasion cometh!8 And if thy hand or thy foot causeth thee to stumble, cut it off, and cast it from thee: it is good for thee to enter into life maimed or halt, rather than having two hands or two feet to be cast into the eternal fire.9 And if thine eye causeth thee to stumble, pluck it out, and cast it from thee: it is good for thee to enter into life with one eye, rather than having two eyes to be cast into the hell of fire.10 See that ye despise not one of these little ones; for I say unto you, that in heaven their angels do always behold the face of my Father who is in heaven.11 For the Son of man came to save that which was lost.12 How think ye? if any man have a hundred sheep, and one of them be gone astray, doth he not leave the ninety and nine, and go unto the mountains, and seek that which goeth astray?13 And if so be that he find it, verily I say unto you, he rejoiceth over it more than over the ninety and nine which have not gone astray.14 Even so it is not the will of your Father who is in heaven, that one of these little ones should perish.

15 And if thy brother sin against thee, go, show him his fault between thee and him alone: if he hear thee, thou hast gained thy brother.16 But if he hear thee not, take with thee one or two more, that at the mouth of two witnesses or three every word may be established.17 And if he refuse to hear them, tell it unto the church: and if he refuse to hear the church also, let him be unto thee as the Gentile and the publican.18 Verily I say unto you, what things soever ye shall bind on earth shall be bound in heaven; and what things soever ye shall loose on earth shall be loosed in heaven.19 Again I say unto you, that if two of you shall agree on earth as touching anything that they shall ask, it shall be done for them of my Father who is in heaven.20 For where two or three are gathered together in my name, there am I in the midst of them.

21 Then came Peter and said to him, Lord, how oft shall my brother sin against me, and I forgive him? until seven times?22 Jesus saith unto him, I say not unto thee, Until seven times; but, Until seventy times seven.23 Therefore is the kingdom of heaven likened unto a certain king, who would make a reckoning with his servants.24 And when he had begun to reckon, one was brought unto him, that owed him ten thousand talents.25 But forasmuch as he had not wherewith to pay, his lord commanded him to be sold, and his wife, and children, and all that he had, and payment to be made.26 The servant therefore fell down and worshipped him, saying, Lord, have patience with me, and I will pay thee all.27 And the lord of that servant, being moved with compassion, released him, and forgave him the debt.28 But that servant went out, and found one of his fellow-servants, who owed him a hundred shillings: and he laid hold on him, and took him by the throat, saying, Pay what thou owest.29 So his fellow-servant fell down and besought him, saying, Have patience with me, and I will pay thee.30 And he would not: but went and cast him into prison, till he should pay that which was due.31 So when his fellow-servants saw what was done, they were exceeding sorry, and came and told unto their lord all that was done.32 Then his lord called him unto him, and saith to him, Thou wicked servant, I forgave thee all that debt, because thou besoughtest me:33 shouldest not thou also have had mercy on thy fellow-servant, even as I had mercy on thee?34 And his lord was wroth, and delivered him to the tormentors, till he should pay all that was due.35 So shall also my heavenly Father do unto you, if ye forgive not every one his brother from your hearts.