previous next

MAT 21

Mutanen Urushalima Sun Marabci Yesu

(Mar 11.1-11; Luka 19.28-40; Yah 12.12-19)

1  t Da suka kusato Urushalima suka zo Betafaji, wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu, 2 ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake gabanku. Da shigarku za ku ga wata jaka a ɗaure, da kuma ɗanta. Ku kwanto su. 3 Kowa ya yi muku magana, ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsu,’ zai kuwa aiko da su nan da nan.”

4 An yi wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Zakariya cewa,

5  t “Ku ce wa 'yar Sihiyona,
Ga Sarkinki yana zuwa gare ki,
Mai tawali'u ne,
Yana kan aholaki, wato, ɗan jaki.”
6 Sai almajiran suka tafi suka bi umarnin Yesu. 7 Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa masu mayafansu, ya hau. 8 t Yawancin jama'a suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya, waɗansu kuma suka kakkaryo ganye suna bazawa a hanya. 9 t Taron jama'a da suke tafiya a gabansa da kuma a bayansa, sai suka ɗauki sowa suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji! Hosanna ga Allah!” 10 Da ya shiga Urushalima dukkan birnin ya ruɗe, ana ta cewa, “Wane ne wannan?”

11 t Sai jama'a suka ce, “Ai, wannan shi ne Annabi Yesu daga Nazarat ta ƙasar Galili.”

Yesu Ya Tsabtace Haikalin

(Mar 11.15-19; Luka 19.45-48; Yah 2.13-22)


12  t Sai Yesu ya shiga Haikalin ya kakkori dukkan masu saye da sayarwa a ciki, ya birkice teburorin 'yan canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tattabarai.

13 t Ya ce musu, “A rubuce yake cewa, ‘Za a kira gidana ɗakin addu'a,’ amma ku kun maishe shi kogon 'yan fashi.”
14  t Sai makafi da guragu suka zo wurinsa a Haikalin, ya kuwa warkar da su. 15 t Amma manyan firistoci da malaman Attaura suka ga abubuwan al'ajabi da ya yi, har yara suna sowa a Haikalin suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” sai suka ji haushi.

16 t Suka ce masa, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?” Yesu kuwa ya ce musu, “I. Amma ba ku taɓa karantawa ba cewa,
‘Kai ne ka shiryar da 'yan yara da masu shan mama su yabe ka’?”

17  t Sai ya bar su, ya fita daga birnin, ya tafi Betanya, ya sauka a can.

La'antar da Itacen Ɓaure

(Mar 11.12-14, 20-24)


18 Kashegari da sassafe yana komowa birni, sai ya ji yunwa. 19 t Da ya ga wani ɓaure a gefen hanya, ya je wurin, amma bai sami kome ba, sai ganye kawai. Sai ya ce wa ɓauren, “Kada ka ƙara yin 'ya'ya har abada!” Nan take ɓauren ya bushe. 20 Da almajiran suka ga haka, suka yi mamaki suka ce, “Yaya ɓauren nan ya bushe haka nan da nan?” 21 t Yesu ya amsa musu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, in dai kuna da bangaskiya, ba tare da wata shakka ba, ba abin da aka yi wa ɓauren nan kaɗai za ku yi ba, har ma in kun ce wa dutsen nan, ‘Ka ciru, ka faɗa teku,’ sai kuwa ya auku.

22 t Kome kuka roƙa da addu'a, in dai kuna da bangaskiya, za ku samu.”

Ana Shakkar Izinin Yesu

(Mar 11.27-33; Luka 20.1-8)


23  t Ya shiga Haikali yana cikin koyarwa, sai manyan firistoci da shugabannin jama'a suka zo wurinsa, suka ce, “Da wane izini kake yin abubuwan nan, wa ya ba ka izinin?” 24 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. In kun ba ni amsa, ni ma sai in gaya muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan. 25 To, baftismar da Yahaya ya yi, daga ina take? Daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?” Sai suka yi ta muhawwara da juna, suna cewa, “In muka ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce mana, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’ 26 t In kuwa muka ce, ‘Ta mutum ce,’ ai, muna jin tsoron jama'a, don duk kowa ya ɗauki Yahaya a kan annabi ne.”

27 Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Shi kuma ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”

Misali na Mai 'Ya'ya Biyu Maza


28  t “To, me kuka gani? An yi wani mutun mai 'ya'ya biyu maza. Ya je wurin na farkon, ya ce, ‘Ɗana, yau je ka ka yi aiki a garkar inabi.’ 29 Sai ya ce, ‘Na ƙi.’ Amma daga baya sai ya tuba, ya tafi. 30 Sai ya je gun na biyun ya faɗa masa haka. Shi kuwa ya amsa ya ce, ‘To, za ni, baba,’ amma bai je ba. 31 t To, wane ne a cikin su biyun ya yi abin da ubansu yake so?” Sai suka ce, “Na farkon.” Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga Mulkin Allah.

32 t Ga shi, Yahaya ya zo ya bayyana muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba. Amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata shi, duk da ganin haka kuma, daga baya ba ku tuba kun gaskata shi ba.”

Misali na Manoman da Suka Yi Sufurin Garkar Inabi

(Mar 12.1-12; Luka 20.9-19)


33  t “To, ga kuma wani misali. An yi wani maigida da ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabi a ciki, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa. 34 t Da kakar inabi ta kusa, sai ya aiki bayinsa wurin manoman nan su karɓo masa gallar garkar. 35 t Manoman kuwa suka kama bayinsa, suka yi wa ɗaya dūka, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi ɗaya. 36 t Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi fiye da na dā, suka kuma yi musu haka. 37 Daga baya sai ya aiki ɗansa gare su, yana cewa, ‘Sā ga girman ɗana.’ 38 t Amma da manoman suka ga ɗan, suka ce wa juna, ‘Ai, wannan shi ne magajin, ku zo mu kashe shi, gādonsa ya zama namu.’ 39 Sai suka kama shi, suka jefa shi bayan shinge, suka kashe shi. 40 To, sa'ad da ubangijin garkar nan ya zo, me zai yi wa manoman nan?”

41 t Sai suka ce masa, “Zai yi wa mutanen banzan nan mugun kisa, ya ba waɗansu manoma sufurinta, waɗanda za su riƙa ba shi gallar garkar a lokacin nunanta.”

42  t Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karantawa a Littattafai ba? cewa,
‘Dutsen da magina suka ƙi,
Shi ne ya zama mafificin dutsen gini.
Wannan aikin Ubangiji ne,
A gare mu kuwa abin al'ajabi ne.’
43  t Domin haka ina gaya muku, za a karɓe Mulkin Allah daga gare ku, a bai wa wata al'umma wadda za ta ba da amfani nagari.

44 t Kowa ya faɗo a kan dutsen nan, sai ya ragargaje. Amma wanda dutsen nan ya faɗa wa, niƙe shi zai yi kamar gari.”
45 Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan nan da ya yi, sai suka gane, ashe, da su yake. 46 t Amma da suka nemi kama shi, suka ji tsoron jama'a, don su sun ɗauke shi shi annabi ne.

Matthew 21

1 And when they drew nigh unto Jerusalem, and came unto Bethphage, unto the mount of Olives, then Jesus sent two disciples,2 saying unto them, Go into the village that is over against you, and straightway ye shall find an ass tied, and a colt with her: loose them, and bring them unto me.3 And if any one say aught unto you, ye shall say, The Lord hath need of them; and straightway he will send them.4 Now this is come to pass, that it might be fulfilled which was spoken through the prophet, saying,

5 Tell ye the daughter of Zion, Behold, thy King cometh unto thee, Meek, and riding upon an ass, And upon a colt the foal of an ass.

6 And the disciples went, and did even as Jesus appointed them,7 and brought the ass, and the colt, and put on them their garments; and he sat thereon.8 And the most part of the multitude spread their garments in the way; and others cut branches from the trees, and spread them in the way.9 And the multitudes that went before him, and that followed, cried, saying, Hosanna to the son of David: Blessed is he that cometh in the name of the Lord; Hosanna in the highest.10 And when he was come into Jerusalem, all the city was stirred, saying, Who is this?11 And the multitudes said, This is the prophet, Jesus, from Nazareth of Galilee.

12 And Jesus entered into the temple of God, and cast out all them that sold and bought in the temple, and overthrew the tables of the money-changers, and the seats of them that sold the doves;13 and he saith unto them, It is written, My house shall be called a house of prayer: but ye make it a den of robbers.14 And the blind and the lame came to him in the temple; and he healed them.15 But when the chief priests and the scribes saw the wonderful things that he did, and the children that were crying in the temple and saying, Hosanna to the son of David; they were moved with indignation,16 and said unto him, Hearest thou what these are saying? And Jesus saith unto them, Yea: did ye never read, Out of the mouth of babes and sucklings thou has perfected praise?17 And he left them, and went forth out of the city to Bethany, and lodged there.

18 Now in the morning as he returned to the city, he hungered.19 And seeing a fig tree by the way side, he came to it, and found nothing thereon, but leaves only; and he saith unto it, Let there be no fruit from thee henceforward for ever. And immediately the fig tree withered away.20 And when the disciples saw it, they marvelled, saying, How did the fig tree immediately wither away?21 And Jesus answered and said unto them, Verily I say unto you, If ye have faith, and doubt not, ye shall not only do what is done to the fig tree, but even if ye shall say unto this mountain, Be thou taken up and cast into the sea, it shall be done.22 And all things, whatsoever ye shall ask in prayer, believing, ye shall receive.

23 And when he was come into the temple, the chief priests and the elders of the people came unto him as he was teaching, and said, By what authority doest thou these things? and who gave thee this authority?24 And Jesus answered and said unto them, I also will ask you one question, which if ye tell me, I likewise will tell you by what authority I do these things.25 The baptism of John, whence was it? from heaven or from men? And they reasoned with themselves, saying, If we shall say, From heaven; he will say unto us, Why then did ye not believe him?26 But if we shall say, From men; we fear the multitude; for all hold John as a prophet.27 And they answered Jesus, and said, We know not. He also said unto them, Neither tell I you by what authority I do these things.28 But what think ye? A man had two sons; and he came to the first, and said, Son, go work to-day in the vineyard.29 And he answered and said, I will not: but afterward he repented himself, and went.30 And he came to the second, and said likewise. And he answered and said, I go, sir: and went not.31 Which of the two did the will of his father? They say, The first. Jesus saith unto them, Verily I say unto you, that the publicans and the harlots go into the kingdom of God before you.32 For John came unto you in the way of righteousness, and ye believed him not; but the publicans and the harlots believed him: and ye, when ye saw it, did not even repent yourselves afterward, that ye might believe him.

33 Hear another parable: There was a man that was a householder, who planted a vineyard, and set a hedge about it, and digged a winepress in it, and built a tower, and let it out to husbandmen, and went into another country.34 And when the season of the fruits drew near, he sent his servants to the husbandmen, to receive his fruits.35 And the husbandmen took his servants, and beat one, and killed another, and stoned another.36 Again, he sent other servants more than the first: and they did unto them in like manner.37 But afterward he sent unto them his son, saying, They will reverence my son.38 But the husbandmen, when they saw the son, said among themselves, This is the heir; come, let us kill him, and take his inheritance.39 And they took him, and cast him forth out of the vineyard, and killed him.40 When therefore the lord of the vineyard shall come, what will he do unto those husbandmen?41 They say unto him, He will miserably destroy those miserable men, and will let out the vineyard unto other husbandmen, who shall render him the fruits in their seasons.42 Jesus saith unto them, Did ye never read in the scriptures, The stone which the builders rejected, The same was made the head of the corner; This was from the Lord, And it is marvelous in our eyes?

43 Therefore say I unto you, The kingdom of God shall be taken away from you, and shall be given to a nation bringing forth the fruits thereof.44 And he that falleth on this stone shall be broken to pieces: but on whomsoever it shall fall, it will scatter him as dust.45 And when the chief priests and the Pharisees heard his parables, they perceived that he spake of them.46 And when they sought to lay hold on him, they feared the multitudes, because they took him for a prophet.