previous next

MAT 22

Misali na Bikin Aure

1 Yesu ya sāke yi musu magana da misalai ya ce, 2 t “Za a kwatanta Mulkin Sama da wani sarki, wanda ya yi wa ɗansa biki. 3 t Sai ya aiki bayinsa su kirawo waɗanda aka gayyata bikin, amma waɗanda aka gayyatar suka ƙi zuwa. 4 t Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi, ya ce, ‘Ku gaya wa waɗanda aka gayyata, “Ga shi, na shisshirya abinci, an yanka shanuna da kiwatattun maruƙana, duk an shirya kome, ku zo bikin mana!” ’ 5 Amma suka ƙi kula, suka tafi abinsu, wani ya tafi gona tasa, wani kuma cinikinsa. 6 Sauran kuwa suka kame bayinsa, suka wulaƙanta su, suka kashe su. 7 t Sarki ya yi fushi, ya tura sojansa, suka hallaka masu kisankan nan, suka ƙone garinsu ƙurmus. 8 Sa'an nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin fa ya shiryu sosai, amma waɗanda aka gayyata ba su cancanta ba. 9 t Saboda haka ku tafi ƙofofin gari, ku gayyato duk waɗanda kuka samu, su zo bikin.’

10 t Sai bayin suka yi ta bin titi titi, suka tattaro duk waɗanda suka samu, mugaye da nagargaru duka, har wurin bikin ya cika maƙil da baƙi.
11 “Da sarki ya shigo ganin baƙin sai ya ga wani mutum a can wanda bai sa riga irin ta biki ba. 12 t Sai ya ce masa, ‘Malam, ta yaya ka shigo nan ba tare da sa riga irin ta biki ba?’ Mutumin kuwa ya rasa ta cewa. 13 t Sai sarki ya ce wa barorinsa, ‘Ku ɗaure shi ƙafa da hannu, ku jefa shi cikin matsanancin duhu. Nan za a yi kuka da cizon baƙi.’

14 t Gama da yawa ake kira, amma kaɗan ne zaɓaɓɓu.”

Biyan Haraji ga Kaisar

(Mar 12.13-17; Luka 20.20-26)


15 Sai Farisiyawa suka je suka yi shawara yadda za su burma shi cikin maganarsa. 16 t Suka aiko almajiransu wurinsa tare da waɗansu mutanen Hirudus, suka ce, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi, ba ka kuma zaɓen kowa, don ka ɗauki kowa da kowa daidai. 17 t To, faɗa mana abin da ka gani. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa?” 18 Yesu kuwa domin ya gane muguntarsu, sai ya ce musu, “Don me kuke jarraba ni? Ku munafukai! 19 Ku nuna mini kuɗin harajin.” Sai suka kawo masa dinari. 20 Yesu ya ce musu, “Surar nan da sunan nan na wane ne?” 21 t Suka ce, “Na Kaisar ne.” Sa'an nan ya ce musu, “To, sai ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.”

22 t Da suka ji haka, sai suka yi mamaki, suka rabu da shi, suka yi tafiyarsu.

Tambaya a kan Tashin Matattu

(Mar 12.18-27; Luka 20.27-40)


23  t A ran nan sai waɗansu Sadukiyawa (su da suke cewa, ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka yi masa tambaya, 24 t suka ce, “Malam, Musa dai ya ce, ‘In mutum ya mutu, bai bar na baya ba, sai lalle ɗan'uwansa ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya.’ 25 To, an yi waɗansu 'yan'uwa maza bakwai a cikinmu. Na farkon ya yi aure, da ya rasu, da yake bai haifu kuma ba, sai ya bar wa ɗan'uwansa matarsa. 26 Haka ya faru ga na biyun da na ukun, har ya kai kan na bakwai ɗin. 27 Bayansu duka sai matar ta rasu.

28 To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu, su bakwai ɗin? Don duk sun aure ta.”
29  t Amma Yesu ya amsa musu ya ce, “Kun ɓăta ne, domin ba ku san Littattafai ba, ba ku kuma san ikon Allah ba. 30 t Domin a tashin matattu, ba a aure, ba a aurarwa, sai dai kamar mala'ikun da suke Sama ake. 31 Game da tashin matattu, ashe, ba ku taɓa karanta abin da Allah ya ce muku ba? cewa, 32 t ‘Ni ne Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.’ Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba.”

33 t Da jama'a suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.

Umarni Mafi Girma

(Mar 12.28-34; Luka 10.25-28)


34  t Amma da Farisiyawa suka ji ya ƙure Sadukiyawa, suka taru. 35 t Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Attaura, ya yi masa tambaya, yana gwada shi, ya ce, 36 “Malam, wane umarni ne mafi girma a cikin Attaura?” 37 t Ya ce masa, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka. 38 Wannan shi ne babban umarni na farko. 39 t Na biyu kuma kamarsa yake, ‘Ka ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.’

40 t A kan umarnin nan biyu duk Attaura da koyarwar annabawa suka rataya.”

Tambaya a kan Ɗan Dawuda

(Mar 12.35-37; Luka 20.41-44)


41 Tun Farisiyawa suna tare gu ɗaya, sai Yesu ya yi musu tambaya, 42 t ya ce, “Yaya kuka ɗauki Almasihu? Shi ɗan wane ne?” Sai suka ce masa, “Ɗan Dawuda ne.”

43 Ya ce musu, “To, yaya kuwa Dawuda, ta ikon Ruhu, ya ce da shi Ubangiji? Har ya ce,

44  t ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,
Zauna a damana,
Sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.’
45 Tun da Dawuda ya kira shi Ubangiji ne, to, ƙaƙa zai zama ɗansa?” 46 t Ba kuwa wanda ya iya tanka masa. Daga ran nan kuwa ba wanda ya yi ƙarfin halin sāke tambayarsa wani abu.

Matthew 22

1 And Jesus answered and spake again in parables unto them, saying,2 The kingdom of heaven is likened unto a certain king, who made a marriage feast for his son,3 and sent forth his servants to call them that were bidden to the marriage feast: and they would not come.4 Again he sent forth other servants, saying, Tell them that are bidden, Behold, I have made ready my dinner; my oxen and my fatlings are killed, and all things are ready: come to the marriage feast.5 But they made light of it, and went their ways, one to his own farm, another to his merchandise;6 and the rest laid hold on his servants, and treated them shamefully, and killed them.7 But the king was wroth; and he sent his armies, and destroyed those murderers, and burned their city.8 Then saith he to his servants, The wedding is ready, but they that were bidden were not worthy.9 Go ye therefore unto the partings of the highways, and as many as ye shall find, bid to the marriage feast.10 And those servants went out into the highways, and gathered together all as many as they found, both bad and good: and the wedding was filled with guests.11 But when the king came in to behold the guests, he saw there a man who had not on a wedding-garment:12 and he saith unto him, Friend, how camest thou in hither not having a wedding-garment? And he was speechless.13 Then the king said to the servants, Bind him hand and foot, and cast him out into the outer darkness; there shall be the weeping and the gnashing of teeth.14 For many are called, but few chosen.

15 Then went the Pharisees, and took counsel how they might ensnare him in his talk.16 And they send to him their disciples, with the Herodians, saying, Teacher, we know that thou art true, and teachest the way of God in truth, and carest not for any one: for thou regardest not the person of men.17 Tell us therefore, What thinkest thou? Is it lawful to give tribute unto Caesar, or not?18 But Jesus perceived their wickedness, and said, Why make ye trial of me, ye hypocrites?19 Show me the tribute money. And they brought unto him a denarius.20 And he saith unto them, Whose is this image and superscription?21 They say unto him, Caesar’s. Then saith he unto them, Render therefore unto Caesar the things that are Caesar’s; and unto God the things that are God’s.22 And when they heard it, they marvelled, and left him, and went away.

23 On that day there came to him Sadducees, they that say that there is no resurrection: and they asked him,24 saying, Teacher, Moses said, If a man die, having no children, his brother shall marry his wife, and raise up seed unto his brother.25 Now there were with us seven brethren: and the first married and deceased, and having no seed left his wife unto his brother;26 in like manner the second also, and the third, unto the seventh.27 And after them all, the woman died.28 In the resurrection therefore whose wife shall she be of the seven? for they all had her.29 But Jesus answered and said unto them, Ye do err, not knowing the scriptures, nor the power of God.30 For in the resurrection they neither marry, nor are given in marriage, but are as angels in heaven.31 But as touching the resurrection of the dead, have ye not read that which was spoken unto you by God, saying,32 I am the God of Abraham, and the God of Isaac, and the God of Jacob? God is not the God of the dead, but of the living.33 And when the multitudes heard it, they were astonished at his teaching.

34 But the Pharisees, when they heard that he had put the Sadducees to silence, gathered themselves together.35 And one of them, a lawyer, asked him a question, trying him:36 Teacher, which is the great commandment in the law?37 And he said unto him, Thou shalt love the Lord thy God with all thy heart, and with all thy soul, and with all thy mind.38 This is the great and first commandment.39 And a second like unto it is this, Thou shalt love thy neighbor as thyself.40 On these two commandments the whole law hangeth, and the prophets.

41 Now while the Pharisees were gathered together, Jesus asked them a question,42 saying, What think ye of the Christ? whose son is he? They say unto him, The son of David.43 He saith unto them, How then doth David in the Spirit call him Lord, saying,

44 The Lord said unto my Lord, Sit thou on my right hand, Till I put thine enemies underneath thy feet?

45 If David then calleth him Lord, how is he his son?46 And no one was able to answer him a word, neither durst any man from that day forth ask him any more questions.