previous next

MAT 23

Yesu Ya Fallashi Malaman Attaura da Farisiyawa

(Mar 12.38-40; Luka 11.37-54; 20.45-47)

1 Sa'an nan Yesu ya yi wa jama'a da almajiransa magana, ya ce, 2 t “Malaman Attaura da Farisiyawa suka tsaya a matsayin Musa. 3 Don haka, sai ku kiyaye, ku kuma aikata duk abin da suka gaya muku, amma banda aikinsu. Don suna faɗa ne, ba aikatawa. 4 t Sukan ɗaura kaya masu nauyi, masu wuyar ɗauka, su jibga wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu ko tallafa musu da ɗan yatsa ba sa yi. 5 t Duk ayyukansu suna yi ne don idon mutane, suna yin layunsu fantam-fantam, lafin rigunansu kuma har gwiwa. 6 t Suna son mazaunan alfarma a wurin biki, da mafifitan mazaunai a majami'u, 7 t a gaishe su a kasuwa, a kuma riƙa ce da su ‘Malam’. 8 Amma ku kam, kada a ce muku ‘Malam’, domin Malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa 'yan'uwa ne. 9 t Kada ku kira kowa ‘Uba’ a duniya, domin Uba ɗaya ne yake gare ku, wanda yake cikin Sama. 10 Kada kuma a kira ku ‘Shugabanni’, domin Shugaba ɗaya gare ku, wato, Almasihu. 11 t Amma wanda yake babba a cikinku shi zai zama baranku.

12 t Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.
13  t “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kun toshe wa mutane ƙofar Mulkin Sama. Ku kanku ba ku shiga ba, kuna kuwa hana masu niyyar shiga shiga. [ 14 Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan ci kayan matan da mazansu sun mutu, kukan yi doguwar addu'a don ɓad da sawu. Saboda haka za a yi muku hukunci mafi tsanani.]

15 t Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan kewaye ƙasashe da tekuna don samun almajiri ɗaya tak, in kuwa kun samu, kukan mai da shi ɗan wuta fiye da ku, ninkin ba ninkin.
16  t “Kaitonku, makafin jagora, ku da kuke cewa, ‘Kowa ya rantse da Haikalin ba kome, amma duk wanda ya rantse da zinariyar Haikalin, sai rantsuwarsa ta kama shi.’ 17 t Ku makafi, wawaye! Wanne ya fi girma, zinariyar ce ko kuwa Haikalin da yake tsarkake zinariyar? 18 Kukan ce, ‘Kowa ya rantse da bagaden hadaya, ba kome. Amma duk wanda ya rantse da sadakar da aka ɗora a kai, sai rantsuwarsa ta kama shi.’ 19 t Ku makafi! Wanne ya fi girma, sadakar ko kuwa bagaden hadaya da yake tsarkake sadakar? 20 Don haka kowa ya rantse da bagaden hadaya, ya rantse ke nan da shi, da duk abin da yake a kansa. 21 t Duk kuma wanda ya rantse da Haikalin ya rantse da shi, da kuma wanda yake zaune a cikinsa.

22 t Kowa kuma ya rantse da Sama, ya rantse da kursiyin Allah, da kuma wanda yake zaune a kansa.
23  t “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan fitar da zakkar na'ana'a, da anise, da lafsur, amma kun yar da muhimman jigajigan Attaura, wato, gaskiya, da jinƙai, da aminci. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da sauran ba.

24 t Makafin jagora, kukan tace ƙwaro ɗan mitsil, amma kukan haɗiye raƙumi!
25  t “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki cike suke da zalunci da zari.

26 Kai makahon Bafarisiye! Sai ka fara tsarkake cikin ƙwaryar da akushin don bayansu ma ya tsarkaka.
27  t “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kamar kaburburan da aka shafa wa farar ƙasa kuke, masu kyan gani daga waje, daga ciki kuwa sai ƙasusuwan matattu da ƙazanta iri iri.

28 Haka nan a idon mutane ku adalai ne, amma ciki sai munafunci da mugun aiki.
29  t “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan yi gini a kan kaburburan annabawa, kuna ƙawata gubbobin adalai. 30 Kuna cewa, ‘Da mun zauna a zamanin kakanninmu, da ba mu taya su zub da jinin annabawa ba.’ 31 t Ta haka kuka shaidi kanku ku ne 'ya'yan masu kisan annabawa. 32 t To, sai ku cikasa ayyukan kakanninku! 33 t Ku macizai! Yaya za ku tsere wa hukuncin Gidan Wuta? 34 t Saboda haka nake aiko muku da annabawa, da masu hikima, da masanan Attaura, za ku kashe waɗansunsu, ku gicciye waɗansu, ku kuma yi wa waɗansu bulala a majami'unku, kuna binsu gari gari kuna gwada musu azaba. 35 t Don alhakin jinin dukan adalai da aka zubar a duniya yă komo a kanku, tun daga jinin Habila adali, har ya zuwa na Zakariya ɗan Berikiya, wanda kuka kashe a tsakanin Haikalin da bagaden hadaya.

36 t Hakika, ina gaya muku, duk wannan zai auko wa mutanen wannan zamani.”

Yesu Ya Ji Juyayin Urushalima

(Luka 13.34-35)


37  t “Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko a gare ku! Sau nawa ne na so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta cikin fikafikanta, amma kun ƙi! 38 t Ga shi, an bar muku gidanku a yashe! 39 t Ina dai gaya muku, ba za ku ƙara ganina ba, sai ran da kuka ce, ‘Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.’ ”

Matthew 23

1 Then spake Jesus to the multitudes and to his disciples,2 saying, The scribes and the Pharisees sit on Moses seat:3 all things therefore whatsoever they bid you, these do and observe: but do not ye after their works; for they say, and do not.4 Yea, they bind heavy burdens and grievous to be borne, and lay them on men’s shoulders; but they themselves will not move them with their finger.5 But all their works they do to be seen of men: for they make broad their phylacteries, and enlarge the borders of their garments,6 and love the chief place at feasts, and the chief seats in the synagogues,7 and the salutations in the marketplaces, and to be called of men, Rabbi.8 But be not ye called Rabbi: for one is your teacher, and all ye are brethren.9 And call no man your father on the earth: for one is your Father, even he who is in heaven.10 Neither be ye called masters: for one is your master, even the Christ.11 But he that is greatest among you shall be your servant.12 And whosoever shall exalt himself shall be humbled; and whosoever shall humble himself shall be exalted.

13 But woe unto you, scribes and Pharisees, hypocrites! because ye shut the kingdom of heaven against men: for ye enter not in yourselves, neither suffer ye them that are entering in to enter.14 Woe unto you, scribes and Pharisees, hypocrites! for ye devour widows’ houses, even while for a pretence ye make long prayers: therefore ye shall receive greater condemnation.

15 Woe unto you, scribes and Pharisees, hypocrites! for ye compass sea and land to make one proselyte; and when he is become so, ye make him twofold more a son of hell than yourselves.

16 Woe unto you, ye blind guides, that say, Whosoever shall swear by the temple, it is nothing; but whosoever shall swear by the gold of the temple, he is a debtor.17 Ye fools and blind: for which is greater, the gold, or the temple that hath sanctified the gold?18 And, Whosoever shall swear by the altar, it is nothing; but whosoever shall swear by the gift that is upon it, he is a debtor.19 Ye blind: for which is greater, the gift, or the altar that sanctifieth the gift?20 He therefore that sweareth by the altar, sweareth by it, and by all things thereon.21 And he that sweareth by the temple, sweareth by it, and by him that dwelleth therein.22 And he that sweareth by the heaven, sweareth by the throne of God, and by him that sitteth thereon.

23 Woe unto you, scribes and Pharisees, hypocrites! for ye tithe mint and anise and cummin, and have left undone the weightier matters of the law, justice, and mercy, and faith: but these ye ought to have done, and not to have left the other undone.24 Ye blind guides, that strain out the gnat, and swallow the camel!

25 Woe unto you, scribes and Pharisees, hypocrites! for ye cleanse the outside of the cup and of the platter, but within they are full from extortion and excess.26 Thou blind Pharisee, cleanse first the inside of the cup and of the platter, that the outside thereof may become clean also.

27 Woe unto you, scribes and Pharisees, hypocrites! for ye are like unto whited sepulchres, which outwardly appear beautiful, but inwardly are full of dead men’s bones, and of all uncleanness.28 Even so ye also outwardly appear righteous unto men, but inwardly ye are full of hypocrisy and iniquity.

29 Woe unto you, scribes and Pharisees, hypocrites! for ye build the sepulchres of the prophets, and garnish the tombs of the righteous,30 and say, If we had been in the days of our fathers, we should not have been partakers with them in the blood of the prophets.31 Wherefore ye witness to yourselves, that ye are sons of them that slew the prophets.32 Fill ye up then the measure of your fathers.33 Ye serpents, ye offspring of vipers, how shall ye escape the judgment of hell?34 Therefore, behold, I send unto you prophets, and wise men, and scribes: some of them shall ye kill and crucify; and some of them shall ye scourge in your synagogues, and persecute from city to city:35 that upon you may come all the righteous blood shed on the earth, from the blood of Abel the righteous unto the blood of Zachariah son of Barachiah, whom ye slew between the sanctuary and the altar.36 Verily I say unto you, All these things shall come upon this generation.

37 O Jerusalem, Jerusalem, that killeth the prophets, and stoneth them that are sent unto her! how often would I have gathered thy children together, even as a hen gathereth her chickens under her wings, and ye would not!38 Behold, your house is left unto you desolate.39 For I say unto you, Ye shall not see me henceforth, till ye shall say, Blessed is he that cometh in the name of the Lord.