previous next

MAT 24

Yesu Ya Faɗi Irin Rushewar da Za ta Sami Haikalin

(Mar 13.1-2; Luka 21.5-6)

1 Yesu ya fita Haikalin, yana cikin tafiya, sai almajiransa suka zo suka nuna masa gine-ginen Haikalin.

2 t Amma ya amsa musu ya ce, “Kun ga duk waɗannan ko? Hakika, ina gaya muku, ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗan'uwansa ba a baje shi ba.”

Farkon Azaba

(Mar 13.3-13; Luka 21.7-19)


3  t Yana zaune a kan Dutsen Zaitun sai almajiransa suka zo wurinsa a kaɗaice, suka ce, “Gaya mana, yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Mece ce kuma alamar dawowarka, da ta ƙarewar zamani?” 4 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku kula fa kada kowa ya ɓad da ku, 5 t domin mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa, su ne Almasihu, har su ɓad da mutane da yawa. 6 Za ku kuma riƙa jin labarin yaƙe-yaƙe da jitajitarsu. Kada fa hankalinku ya tashi, don lalle ne a yi haka, amma ƙarshen tukuna. 7 t Al'umma za ta tasar wa al'umma, mulki ya tasar wa mulki. Za a kuma yi yunwa da raurawar ƙasa a wurare dabam dabam.

8 Amma fa duk wannan masomin azaba ne tukuna.
9  t “Sa'an nan za su bashe ku, a ƙuntata muku, su kuma kashe ku. Duk al'ummai za su ƙi ku saboda sunana. 10 A sa'an nan da yawa za su yi tuntuɓe, su ci amanar juna, su kuma ƙi juna. 11 t Annabawan ƙarya da yawa za su firfito, su ɓad da mutane da yawa. 12 Saboda kuma yaɗuwar mugun aiki, sai ƙaunar yawancin mutane ta yi sanyi. 13 t Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu.

14 t Za a kuma yi bisharar nan ta Mulkin Sama ko'ina a duniya domin shaida ga dukkan al'ummai. Sa'an nan kuma sai ƙarshen ya zo.”

Matsananciyar Wahala

(Mar 13.14-23; Luka 21.20-24)


15  t “Don haka sa'ad da kuka ga mummunan aikin saɓo mai banƙyama, wanda Annabi Daniyel ya faɗa, an tsai da shi a Wuri Mai Tsarki (mai karatu fa yă fahimta), 16 to, sai waɗanda suke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu. 17 t Wanda yake soro, kada ya sauko garin ɗaukar wanda yake a gidansa. 18 Wanda yake a gona kuma, kada ya koma garin ɗaukar mayafinsa. 19 t Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci! 20 Ku yi addu'a kada gudunku ya zo da damuna, ko ran Asabar. 21 t A lokacin nan za a yi wata matsananciyar wahala, irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu, ba kuwa za a ƙara yi ba har abada. 22 t Ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da ba ɗan adam ɗin da zai tsira. Amma sabili da zaɓaɓɓun nan za a taƙaita kwanakin. 23 t A sa'an nan kowa ya ce muku, ‘Kun ga, ga Almasihu nan!’ ko, ‘Ga shi can!’ kada ku yarda. 24 t Don almasihan ƙarya da annabawan ƙarya za su firfito, su nuna manyan alamu da abubuwan al'ajabi, don su ɓad da ko da zaɓaɓɓu ma in dai zai yiwu. 25 To, na dai gaya muku tun da wuri. 26 Saboda haka in sun ce da ku, ‘Ga shi can a jeji,’ kada ku fita. In kuwa sun ce, ‘Yana can cikin lolloki,’ kada ku yarda. 27 t Kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka komowar Ɗan Mutum za ta zama.

28 t Inda mushe yake, ai, a nan ungulai sukan taru.

Komowar Ɗan Mutum

(Mar 13.24-27; Luka 21.25-28)


29  t “Bayan tsabar wahalar nan, nan da nan sai a duhunta rana, wata kuma ba zai yi haske ba. Taurari kuma za su farfaɗo daga sararin sama, za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke sararin sama. 30 t A sa'an nan ne alamar Ɗan Mutum za ta bayyana a sararin sama, duk kabilan duniya kuma za su yi kuka, za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gajimare, da iko da ɗaukaka mai yawa.

31 t Zai kuwa aiko mala'ikunsa su busa ƙaho mai tsananin ƙara, su kuma tattaro zaɓaɓɓunsa daga gabas da yamma, kudu da arewa, wato, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.”

Aya a kan Itacen Ɓaure

(Mar 13.28-31; Luka 21.29-33)


32 “Ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa sun fara sakuwa, suna toho, kun san damuna ta yi kusa ke nan. 33 t Haka kuma in kun ga duk waɗannan abubuwa, ku sani ya kusato, a bakin ƙofa ma yake. 34 t Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun auku.

35 t Sararin sama da kasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”

Ba Wanda Ya San Ranar ko Sa'ar

(Mar 13.32-37; Luka 17.26-30, 34-36)


36  t “Amma fa wannan rana da wannan sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun da yake Sama, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai. 37 t Kamar yadda aka yi a zamanin Nuhu, haka dawowar Ɗan Mutum za ta zama. 38 t Kamar a kwanakin nan ne gabannin Ruwan Tsufana, ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har ya zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi, 39 ba su farga ba har Ruwan Tsufana ya zo ya share su. Haka komowar Ɗan Mutum za ta zama. 40 t A sa'an nan za a ga mutum biyu a gona, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya. 41 t Za a ga mata biyu suna niƙa, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya. 42 t To, ku zauna a faɗake fa, don ba ku san ranar da Ubangijinku zai dawo ba. 43 t Amma dai ku sani, da maigida zai san ko a wane lokaci ne da dare ɓarawo zai zo, da ya zauna a faɗake ya hana a shigar masa gida.

44 t Don haka ku ma sai ku zauna a kan shiri, domin a lokacin da ba ku zata ba, Ɗan Mutum zai zo.”

Amintaccen Bawa ko Marar Aminci

(Luka 12.41-48)


45  t “Wane ne amintaccen bawan nan mai hikima, da ubangidansa ya ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari? 46 t Albarka tā tabbata ga bawan da in ubangidansa ya dawo zai samu yana yin haka. 47 t Hakika, ina gaya muku, sai ya ɗora shi a kan dukan mallakarsa. 48 Amma in bawan nan mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Ubangidana ya jinkirta zuwansa,’ 49 t sa'an nan ya soma dūkan abokan bautarsa, yana ci yana sha tare da mashaya, 50 ai, ubangidan wannan bawa zai zo a ranar da bai zata ba, a kuma lokacin da bai sani ba, 51 t yă farfasa masa jiki da bulala, ya ba shi rabonsa tare da munafukai. Nan za a yi kuka da cizon baki.”

Matthew 24

1 And Jesus went out from the temple, and was going on his way; and his disciples came to him to show him the buildings of the temple.2 But he answered and said unto them, See ye not all these things? verily I say unto you, There shall not be left here one stone upon another, that shall not be thrown down.

3 And as he sat on the mount of Olives, the disciples came unto him privately, saying, Tell us, when shall these things be? and what shall be the sign of thy coming, and of the end of the world?4 And Jesus answered and said unto them, Take heed that no man lead you astray.5 For many shall come in my name, saying, I am the Christ; and shall lead many astray.6 And ye shall hear of wars and rumors of wars; see that ye be not troubled: for these things must needs come to pass; but the end is not yet.7 For nation shall rise against nation, and kingdom against kingdom; and there shall be famines and earthquakes in divers places.8 But all these things are the beginning of travail.9 Then shall they deliver you up unto tribulation, and shall kill you: and ye shall be hated of all the nations for my name’s sake.10 And then shall many stumble, and shall deliver up one another, and shall hate one another.11 And many false prophets shall arise, and shall lead many astray.12 And because iniquity shall be multiplied, the love of the many shall wax cold.13 But he that endureth to the end, the same shall be saved.14 And this gospel of the kingdom shall be preached in the whole world for a testimony unto all the nations; and then shall the end come.

15 When therefore ye see the abomination of desolation, which was spoken of through Daniel the prophet, standing in the holy place (let him that readeth understand),16 then let them that are in Judaea flee unto the mountains:17 let him that is on the housetop not go down to take out things that are in his house:18 and let him that is in the field not return back to take his cloak.19 But woe unto them that are with child and to them that give suck in those days!20 And pray ye that your flight be not in the winter, neither on a sabbath:21 for then shall be great tribulation, such as hath not been from the beginning of the world until now, no, nor ever shall be.22 And except those days had been shortened, no flesh would have been saved: but for the elect’s sake those days shall be shortened.23 Then if any man shall say unto you, Lo, here is the Christ, or, Here; believe it not.24 For there shall arise false Christs, and false prophets, and shall show great signs and wonders; so as to lead astray, if possible, even the elect.25 Behold, I have told you beforehand.26 If therefore they shall say unto you, Behold, he is in the wilderness; go not forth: Behold, he is in the inner chambers; believe it not.27 For as the lightning cometh forth from the east, and is seen even unto the west; so shall be the coming of the Son of man.28 Wheresoever the carcase is, there will the eagles be gathered together.

29 But immediately after the tribulation of those days the sun shall be darkened, and the moon shall not give her light, and the stars shall fall from heaven, and the powers of the heavens shall be shaken:30 and then shall appear the sign of the Son of man in heaven: and then shall all the tribes of the earth mourn, and they shall see the Son of man coming on the clouds of heaven with power and great glory.31 And he shall send forth his angels with a great sound of a trumpet, and they shall gather together his elect from the four winds, from one end of heaven to the other.

32 Now from the fig tree learn her parable: when her branch is now become tender, and putteth forth its leaves, ye know that the summer is nigh;33 even so ye also, when ye see all these things, know ye that he is nigh, even at the doors.34 Verily I say unto you, This generation shall not pass away, till all these things be accomplished.35 Heaven and earth shall pass away, but my words shall not pass away.36 But of that day and hour knoweth no one, not even the angels of heaven, neither the Son, but the Father only.37 And as were the days of Noah, so shall be the coming of the Son of man.38 For as in those days which were before the flood they were eating and drinking, marrying and giving in marriage, until the day that Noah entered into the ark,39 and they knew not until the flood came, and took them all away; so shall be the coming of the Son of man.40 Then shall two man be in the field; one is taken, and one is left:41 two women shall be grinding at the mill; one is taken, and one is left.42 Watch therefore: for ye know not on what day your Lord cometh.43 But know this, that if the master of the house had known in what watch the thief was coming, he would have watched, and would not have suffered his house to be broken through.44 Therefore be ye also ready; for in an hour that ye think not the Son of man cometh.

45 Who then is the faithful and wise servant, whom his lord hath set over his household, to give them their food in due season?46 Blessed is that servant, whom his lord when he cometh shall find so doing.47 Verily I say unto you, that he will set him over all that he hath.48 But if that evil servant shall say in his heart, My lord tarrieth;49 and shall begin to beat his fellow-servants, and shall eat and drink with the drunken;50 the lord of that servant shall come in a day when he expecteth not, and in an hour when he knoweth not,51 and shall cut him asunder, and appoint his portion with the hypocrites: there shall be the weeping and the gnashing of teeth.