previous next

MAT 25

Misali na Budurwai Goma

1  t “Sa'an nan za a kwatanta Mulkin Sama da 'yan mata goma da suka ɗauki fitilunsu suka tafi taryen ango. 2 t Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuwa masu hikima. 3 Don kuwa a lokacin da wawayen nan suka ɗauki fitilunsu, ashe, ba su riƙo mai ba. 4 Masu hikimar nan kuwa sun riƙo kwalaben mai da fitilunsu. 5 t Da yake angon ya yi jinkiri, duk sai suka yi gyangyaɗi, har barci ya share su. 6 Can tsakar dare sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito ku tarye shi!’ 7 Duk 'yan matan nan suka tashi suka gyaggyara fitilunsu. 8 t Sai wawayen nan suka ce wa masu hikimar, ‘Ku sa mana ɗan manku kaɗan mana, fitilunmu na mutuwa!’ 9 Amma masu hikimar suka amsa suka ce, ‘Ai, watakila ba zai ishe mu mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’ 10 t Tun suna wajen sayen, sai angon ya iso, waɗanda suke shirye suka shiga wurin biki tare da shi, aka kuma rufe ƙofa. 11 Daga baya sai waɗancan 'yan matan ma suka iso, suka ce, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji, ka buɗe mana!’ 12 Sai ya amsa ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, ni ban san ku ba.’

13 t Don haka, sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ba, ko kuwa sa'ar.”

Misali na Talanti


14  t “Kamar mutum ne da zai yi tafiya, ya kira bayinsa, ya danƙa musu dukiyarsa. 15 t Ya ba ɗaya talanti biyar, ɗaya talanti biyu, wani kuma ya ba shi ɗaya, kowa dai gwargwadon ƙarfinsa. Sa'an nan ya tafi. 16 Shi wanda ya karɓi talanti biyar ɗin nan, nan da nan sai ya je ya yi ta jujjuya su, har wuri ya bugi wuri. 17 Haka kuma wanda ya karɓi talanti biyu, shi ma sai wuri ya bugi wuri. 18 Amma wannan da ya karɓi talanti ɗaya ɗin, sai ya je ya tona rami ya ɓoye kuɗin ubangijinsa. 19 t To, da aka daɗe sai ubangijin bayin nan ya dawo ya daidaita lissafi da su. 20 Shi wannan da ya karɓi talanti biyar sai ya matso ya kawo waɗansu talanti biyar, ya ce, ‘Ya ubangiji, kā ba ni talanti biyar, ga shi kuma, na ci ribar biyar.’ 21 t Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangidanka.’ 22 Sai mai talanti biyun nan kuma ya matso, ya ce, ‘Ya ubangiji, kā ba ni talanti biyu, ga shi kuma, na ci ribar biyu.’ 23 t Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangijinka.’ 24 Shi kuma wanda ya karɓi talanti guda ɗin, sai ya matso, ya ce, ‘Ya ubangiji, na sani kai mutum ne mai tsanani, kana son girbi inda ba kai ka shuka ba, mai son banza ne. 25 Shi ya sa na ji tsoro, har na je na yi tono na ɓoye talantinka. To, ga kayanka nan!’ 26 Sai ubangijinsa ya amsa masa ya ce, ‘Kai mugun bawa, malalaci! Ashe, ka sani ina girbi inda ba ni na shuka ba, ni kuma mai son banza ne? 27 Ya kamata ka sa kuɗina a ma'aji, da na dawo kuma da sai in karɓi abina har da riba! 28 Don haka sai ku karɓe talantin daga gunsa, ku bai wa mai goman nan. 29 t Don duk mai abu a kan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.

30 t Ku kuma jefa banzan bawan nan a baƙin duhu. Nan za a yi kuka da cizon baki.’ ”

Shara'anta wa Al'ummai


31  t “Sa'ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa tare da mala'iku duka, sa'an nan ne zai zauna a maɗaukakin kursiyinsa. 32 t Za a tara dukan al'ummai a gabansa, zai kuma ware su dabam dabam, kamar yadda makiyayi yake ware tumaki da awaki. 33 Zai sa tumaki a damansa, awaki kuwa a hagunsa. 34 t Sa'an nan ne Sarki zai ce wa waɗanda suke dama da shi, ‘Ku zo, ya ku da Ubana ya yi wa albarka, sai ku gāji mulkin da aka tanadar muku tun daga farkon duniya. 35 t Domin na ji yunwa, kun ba ni abinci. Na ji ƙishirwa, kun ba ni na sha. Na yi baƙunci, kun saukar da ni. 36 t Na yi huntanci, kun tufasar da ni. Na yi rashin lafiya, kun ziyarce ni. Ina kurkuku, kun kula da ni.’ 37 Sa'an nan ne masu adalci za su amsa masa su ce, ‘Ya Ubangiji, a yaushe muka gan ka da yunwa muka cishe ka, ko kuwa da ƙishirwa muka shayar da kai? 38 A yaushe kuma muka gan ka baƙo muka sauke ka, ko kuwa huntu muka tufasar da kai? 39 Ko kuma a yaushe muka gan ka da rashin lafiya, ko a kurkuku muka kula da kai?’ 40 t Sai Sarkin zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake kun yi wa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan'uwana mafi ƙanƙanta, ai, ni kuka yi wa.’ 41 t Sa'an nan zai ce wa waɗanda suke na hagun, ‘Ku rabu da ni, la'anannu, ku shiga madawwamiyar wuta, wadda aka tanadar wa Iblis da mala'ikunsa. 42 Don na ji yunwa, ba ku ba ni abinci ba. Na ji ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba. 43 Na yi baƙunci, ba ku sauke ni ba. Na yi huntanci, ba ku tufasar da ni ba. Na yi rashin lafiya, ina kuma kurkuku, ba ku kula da ni ba.’ 44 Sa'an nan su ma za su amsa su ce, ‘Ya Ubangiji, a yaushe muka gan ka da yunwa, ko da ƙishirwa, ko da baƙunci, ko da huntanci, ko da rashin lafiya, ko a kurkuku, ba mu kula da kai ba?’ 45 t Sa'an nan zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ai, ni ne ba ku yi mini ba.’ 46 t Waɗannan ne za su shiga madawwamiyar azaba, masu adalci kuwa rai madawwami.”

Matthew 25

1 Then shall the kingdom of heaven be likened unto ten virgins, who took their lamps, and went forth to meet the bridegroom.2 And five of them were foolish, and five were wise.3 For the foolish, when they took their lamps, took no oil with them:4 but the wise took oil in their vessels with their lamps.5 Now while the bridegroom tarried, they all slumbered and slept.6 But at midnight there is a cry, Behold, the bridegroom! Come ye forth to meet him.7 Then all those virgins arose, and trimmed their lamps.8 And the foolish said unto the wise, Give us of your oil; for our lamps are going out.9 But the wise answered, saying, Peradventure there will not be enough for us and you: go ye rather to them that sell, and buy for yourselves.10 And while they went away to buy, the bridegroom came; and they that were ready went in with him to the marriage feast: and the door was shut.11 Afterward came also the other virgins, saying, Lord, Lord, open to us.12 But he answered and said, Verily I say unto you, I know you not.13 Watch therefore, for ye know not the day nor the hour.

14 For it is as when a man, going into another country, called his own servants, and delivered unto them his goods.15 And unto one he gave five talents, to another two, to another one; to each according to his several ability; and he went on his journey.16 Straightway he that received the five talents went and traded with them, and made other five talents.17 In like manner he also that received the two gained other two.18 But he that received the one went away and digged in the earth, and hid his lord’s money.19 Now after a long time the lord of those servants cometh, and maketh a reckoning with them.20 And he that received the five talents came and brought other five talents, saying, Lord, thou deliveredst unto me five talents: lo, I have gained other five talents.21 His lord said unto him, Well done, good and faithful servant: thou hast been faithful over a few things, I will set thee over many things; enter thou into the joy of thy lord.22 And he also that received the two talents came and said, Lord, thou deliveredst unto me two talents: lo, I have gained other two talents.23 His lord said unto him, Well done, good and faithful servant: thou hast been faithful over a few things, I will set thee over many things; enter thou into the joy of thy lord.24 And he also that had received the one talent came and said, Lord, I knew thee that thou art a hard man, reaping where thou didst not sow, and gathering where thou didst not scatter;25 and I was afraid, and went away and hid thy talent in the earth: lo, thou hast thine own.26 But his lord answered and said unto him, Thou wicked and slothful servant, thou knewest that I reap where I sowed not, and gather where I did not scatter;27 thou oughtest therefore to have put my money to the bankers, and at my coming I should have received back mine own with interest.28 Take ye away therefore the talent from him, and give it unto him that hath the ten talents.29 For unto every one that hath shall be given, and he shall have abundance: but from him that hath not, even that which he hath shall be taken away.30 And cast ye out the unprofitable servant into the outer darkness: there shall be the weeping and the gnashing of teeth.

31 But when the Son of man shall come in his glory, and all the angels with him, then shall he sit on the throne of his glory:32 and before him shall be gathered all the nations: and he shall separate them one from another, as the shepherd separateth the sheep from the goats;33 and he shall set the sheep on his right hand, but the goats on the left.34 Then shall the King say unto them on his right hand, Come, ye blessed of my Father, inherit the kingdom prepared for you from the foundation of the world:35 for I was hungry, and ye gave me to eat; I was thirsty, and ye gave me drink; I was a stranger, and ye took me in;36 naked, and ye clothed me; I was sick, and ye visited me; I was in prison, and ye came unto me.37 Then shall the righteous answer him, saying, Lord, when saw we thee hungry, and fed thee? or athirst, and gave thee drink?38 And when saw we thee a stranger, and took thee in? or naked, and clothed thee?39 And when saw we thee sick, or in prison, and came unto thee?40 And the King shall answer and say unto them, Verily I say unto you, Inasmuch as ye did it unto one of these my brethren, even these least, ye did it unto me.41 Then shall he say also unto them on the left hand, Depart from me, ye cursed, into the eternal fire which is prepared for the devil and his angels:42 for I was hungry, and ye did not give me to eat; I was thirsty, and ye gave me no drink;43 I was a stranger, and ye took me not in; naked, and ye clothed me not; sick, and in prison, and ye visited me not.44 Then shall they also answer, saying, Lord, when saw we thee hungry, or athirst, or a stranger, or naked, or sick, or in prison, and did not minister unto thee?45 Then shall he answer them, saying, Verily I say unto you, Inasmuch as ye did it not unto one of these least, ye did it not unto me.46 And these shall go away into eternal punishment: but the righteous into eternal life.